Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 55 of 124

Da yamma Ammah tasa Batuul ta sake shiryawa cikin wani kayan, atampa exclusive ta saka mai kyau, kayan yayi mata kyau sosai har ta gaji, k'asa suka sauk'o lokacin Abutturab shima yana k'asa yana jiranta, shima yayi kyau sosai cikin kaftan 膹inshi fari da hularshi Rawaram, tunda take sauk'owa yake kallonta har sai da ta k'araso tazo kusa dashi tukunna ya 膹auke idonshi daga kanta, Ammah ce tace "ku fara zuwa gidan Yaa Mera daga nan ku wuce gidansu", "Toh kawai yace ya juya yana jira ta fara fita, ganin batada niyyan motsi yayi 膹an siririn tsaki ya fita, a hankali take 膹aga k'afa tabi bayanshi, sai da ya bu膹e motar ya shiga ya zauna tukunna itama ta bu膹e ta shiga, babu wanda yace da wani uffan har suka isa gidan Yaa Mera, sosai taji da膹in ganinsu, Nasiha tayi musu sosai tasa aka cika musu gabansu da abinci iri iri, suna zaune Massa ya shigo shima yayi ta tsokanan Batuul da ta kasa cewa komai, basu wuce awa 膹aya ba suka yiwa su Yaa Mera sallama, itama tayi musu addu'a suka wuce, sai da ya 膹au hanyan gidansu tukunna ya fara magana ba tare da ya kalleta ba "ki dena yiwa mutane wannan shirun naki, sai anyi miki magana kiyi kamar bakya jin abinda ake fa膹i idan aka tambayi dalili ki saka ma mutane kukan munafurci" kamar batasan mey yake cewa ba taci gaba da kallon window ta waje, jin tak'i cewa komai yayi k'wafa yaci gaba da tuk'inshi, suna zuwa gaban gate 膹in gidansu, hannu tasa zata bu膹e k'ofan ta fita kamin masu gadi su bu膹esu musu gate, kamar yasan abinda take shirin yi ya danna lock 膹in motar, mur膹awa tayi taji yaqi bu膹uwa, rau rau tayi da ido tana kallonshi, har idonta ya fara hawaye , mamakinta ya tsayayi yace "da akayi miki mey 膹in zaki fara hawaye kuma", 膹auke kanta tayi tare da 膹an murgu膹a bakinta ta 膹anyi murmuring wani abu sae dae fa duk ganinsu da tayi a kofar gidansu ne yasa ta samu wnn livern, kallonta yayi yace "Did you say anything", daidai lokacin aka bu膹e gate 膹in yayi k'wafa ya 膹auke kanshi daga dubanta ya sa kai cikin gidan, kin bu膹ewa yayi bayan yayi parking har saida ta juyo ta kalleshi, yace "clean those tears , baza ki shiga gidannan da hawaye ba", ba shiri ta shiga share hawayen dake idonta, sai da ta goge ta juyo tana dubanshi ganin yaki budewa har lkcn a hnkli tace " na goge", daga gefenshi ya danna lock 膹in, da sauri ta bu膹e motar ta fita a guje, murmushi yayi ya fito daga cikin motar, da gudu ta shiga palon gidansu tana k'walawa y'an gidansu k'ira a jere, Aunty Hafsat da ta fito daga kitchen ta fara ha膹uwa da, da mamaki Aunty Hafsat tace "A ah Batuul daga ina haka kika shigo kina ihu", tafiya taji kan stairs, juyawa tayi taga Aunty ke sauk'owa, da gudu tayi wajen Aunty ta rungumeta, tana jinta jikin Aunty ta fashe kuka, murmushin k'arfin hali Aunty tayi dan itama kwana 膹aya da tayi bata gidan tayi kewarta sosai, 膹agota tayi tana kallon fuskanta tace "Kukan na meye kuma Batuul", sake komawa tayi ta kwanta jikin Aunty taci gaba da kukan da takeyi, da sallama ya shigo falon, 膹agowa tayi daga jikin Aunty tana kallon Aunty tace "Aunty su Mahir fa", Aunty tace "Ai yau babu wanda yaje Islamiyya cikinsu, Hafiz kam kuka ya dingayi wai sai an kaishi inda kike", hawayen dake idonta ne ya k'arasa gangarowa jin abinda Aunty tace, da gudu ta k'arasa hawa sama tayi 膹akinsu, bu膹ewa tayi tagansu kamar kullum 膹akin yadda yake suna kallon ball, da gudu ta shige ta rungumosu, sai da suka sake juna Yusra tace "Yaa Batuul wai inji Baba zaki tafi Uk yau zamu da膹e bamu ganki ba dagaskene?", ji tayi kamar zata fasa ihu tayi murmushi tace "a ah bazan da膹e ba, ai zaku rakani airport ko", da sauri suka shiga gya膹a kai, ta kalli manyan da sukayi kamar basu san tana 膹akin ba tace "y'an rainin wayo dama nasan jira kuke in bar gidan shiyasa kun ganni yanxu ma baku damu ba", dariya sukayi suka juyo sukace "penalty za a buga shiyasa", duk suka taso suka dawo kan gadon da take, zama tayi suna ta hira da k'annenta har saida Aunty ta tura a k'irata, kitchen ta samu Aunty, anty ta dubeta tace "Batuul wa yace miki haka akeyi, ya zaki tafi ki barshi shi ka膹ai ko ruwa baki bashi ba", baki ta zumb'uro tace "Aunty toh ba su Janet zasu bashi ba", Kai Aunty ta girgiza tasan akwai aiki sosai gaban Batuul dan ba wayone ya gama isanta ba gashi lokacinsu is limited, amma ba komai ko ta wayane zatayi mata magana, kai ta girgiza ta juya ta 膹auko tray ta jera abubuwa tace "膹auki ki kai mishi", baki ta zumb'uro ta kinkimi trayn tayi palo dashi dungure masa tayi a kasa ba tare da ta kallesa ba, ya bi ta da kallo har ta haura sama yyi murmushi, sai magrib lokacin suna shirin tafiya Baba ya dawo, shima ganinshi ta shiga sabon kuka, da k'yar ya samu tayi shiru, Abu kam suna ha膹a ido yake sakar mata harara, cewa Baba tayi sam sai k'annenta sun rakata airport, da farko da yaqi dan sai sun koma gidan Ammah zasu wuce, amma ganin yadda take kuka yasa driver ya kaisu, sai a lokacin Aunty taji baza ta iya jurewa ba itama taja Batuul sukayi 膹aki, sunfi minti talatin har saida Baba ya shigo yace ya isa haka ta fito su tafi, kuka takeyi sosai har ta shiga cikin motar, bai ce mata komai ba shima ya shiga, motar su Ahmad na daga gaba nasu na baya sukayi gidan Ammah.
[8/22, 2:10 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

42

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Kanta ta kifa tsakanin cinyoyinta ta dinga rusa kuka, shi dai bai ce mata komai ba sai kallonta da yake ta gefen ido yaga if she's fine, sai da suka shiga cikin gida bayan yayi parking ya juyo ya dubeta ganin batada niyyan tashi ya sa ya bude motar ya fito ya wuce gun motar k'annenta, sai da k'annenta suka fito suka nufi motar Abuturrab tukunna ta shiga goge hawayen dake fuskanta, dan murmushi tayi masu ta sauk'o daga cikin motar tana kallonsu tace "mu shiga mana", ba musu sukayi gaba, yana daga gefe yana kallonsu, yaran masu kyau duk sun fita haske, juyawa tayi ta dubi inda yake tsaye yasa hannu 膹aya cikin aljihu, wani kallo ya shiga yi mata, 膹auke kanta tayi daga dubanshi tabi bayansu, ita ta bu膹e musu k'ofa sai da suka gama shiga itama ta shiga da sallama, da murna Farida dake zaune tare da Ammah ta mik'e tana k'ok'arin 膹aukan Hafiz, waje suka samu suka zazzauna daga k'asan rug 膹in palon, da fara'a Ammah ta shiga ce musu "Ahmad ku tashi ku zauna kan kujera mana", babu abinda sukeyi sai murmushi, ta dubi Batuul tace "Bitti ce musu su hau kujera mana su tashi daga k'asan nan", kallonsu kawai Batuul tayi ta kasa musu magana, ganin sunqi tashi Ammah ta mik'awa Yusra, Mahir da Hafiz hannu alamun suzo wajenta, Yusrace ka膹ai taje dan ita tana da saurin sabo, Janet Farida tashiga k'walawa k'ira, babu b'ata lokaci ta fito tace "Aunty gani nazo", ta dubeta tace "kawo musu ruwa", ba b'ata lokaci ta juya ta tafi kawo musu ruwa, Ammah zatayi magana kenan ya turo k'ofa ya shigo yana tafiyarshi ta k'asaita, palon ya k'araso ya zauna, Ammah ta dubeshi tace " tare da su xa ku airport knn", Batuul da kanta ke k'asa taqi 膹agowa yake kallo kamin ya kalli Ammah yace "Ehhh kuka tayi ta musu kamar yarinya wai tanaso su rakata", Ammah tayi dariya tace "Babu wani yarinta, ai gaskiyanta da tace su rakota su yi bankwana", baice komai ba sae tab'e baki da yyi ya mik'e yana kallon Ammah yace "Ammah Sadiq 膹in ya fito ne, saura thirty minutes tafiyan namu", Ammah tace "Ai yanxun nan ya shiga wanka", daga jin haka ya wuce, Ammah ma tashi tayi tace "Bitti muje ki shirya kar lokaci ya k'ure kinji", ba musu ta mik'e amma har lokacin ta kasa yadda wai itace za a rakata airport zata bar garinsu dan tayi aure zataje zama da wani, take idonta ya fara kawo ruwa, jiki a sanyaye ta bi bayan Ammah, tana shiga bath tub ta dinga kuka dan kanta ta mik'e ta fito bayan ta kusa minti goma a ciki, wasu kaya ta gani Ammah ta ajiye mata kan gado, Lace maroon ne mai green designs da jewellery 膹insu na gwal, ba b'ata lokaci ta 膹auka ta sakasu cikin rashin kuxari, riga da skirt ne, kayan sun mata kyau sosai, a bakin gado ta zauna bayan ta gama y'an shafe shafenta ta shiga tunanin irin rayuwar da xata yi ynxu.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.