Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 65 of 124
50
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Had'iye dariyarshi yayi ganin kukan da Ajiddeh keyi kamar wacce aka daka ya juyo yana kallon Batuul da tayi saurin gintse dariyarta ta sunkuyar da kai, hannunta ya kamo ya dawo da ita gaban gadon Ajiddeh ya hade rai yace "sake bata hakurin", a hankali Batuul tace "kiyi hak'uri" jajayen Idonta da suka rine ta dago tana mata wani mugun kallo, kallon Batuul yayi yace mata "Get out", kamar munafika ta fice daga d'akin, tana fita ya dawo bakin gadon ya zauna tareda janyo Ajiddeh jikinshi, kukan ta sake fashewa da, bayanta ya shiga bubbugawa yace "Hey babe, tace fa ba dake take ba, beside meye Na zuwa da yin amai bayan har ta ganki kinci, ai cemata zakiyi ta zubo miki ma tunda gidanki ne" ya k'arashe maganan yana murmushi, d'ago kanta tayi tana hararansa da rinannun idanuwanta a fusace tace "toh kai dariyar da kake yi ta me? Memakon kayi mata fad'an abinda tayi shine ka biye mata kuna min dariya don walakanci koh", har lokacin yana murmushi yace "its okay yanxu ai na sata baki hakuri, i will deal with her next time she tries anything stupid thing" d'ago kanta tayi ta sake kallonshi , kai ya kad'a mata yace "i mean it wife, kin ma yi sllhn kuwa" shirun da yaji tayi yasashi gane batayi ba, yace Mata "tashi kije kiyi sllh, I will b back right away" daga haka ya mik'e ya fita
Batuul na fita ta wuce d'akinta, kan gado ta fad'a taci gaba da dariya, sai da tayi mai isarta tukunna ta gyara kwanciyarta kan gadon, nan bacci ya d'auketa, bata dad'e da kwanciya ba taji k'iran sllhn wayarta Na bugawa, a kasalance ta tashi dan ba isanta baccin yayi ba sannan baccin bayan la'asar ne, da k'yar ta mik'e ta kashe, ta Shiga toilet tayi alwala, abun sllh ta shimfida ta hau kai, bayan minti biyar ta tashi tayi sllh magrib, nan ta zauna har akayi Isha tayi, daga nan ta mik'e tayi shirin Kwanciya, wanka tayi ta fito ta saka kayan baccinta riga da dogon wando, snn ta koma kan gadon ta kwanta bayan ta rufe k'ofar d'akin, tafi awa d'aya kwance baccin yaqi xuwa mata, babu abinda takeyi sai tsaki, tashi tayi ta janyo system d'inta, in to the bad lands ta kunna zataci gaba da kallo, tura k'ofan d'akin akayi, a tsorace ta d'ago kanta ganin waye , mamaki ne ya kamata dan tasan ta rufe k'ofarta, toh mesa zai wani ce ta dinga rufe k'ofarta bayan yasan he have access to it, d'an murgud'a baki tayi ta sunkuyar da kanta taci gaba da kallo, shigowa yayi ba tareda yyi bother ya kunna wutan d'akin ba, a bakin gadon ya tsaya, yace "Abinci kike jira a siyo maki da baki sakko neman dinner ba, or are yhu afraid of my wife" zumb'uro baki tayi cikin duhun ganin baya ganinta, a ranta tace shi wannan mutumin ina ruwanshi ne da cin abinci na, jin tayi shiru yasa ranshi ya b'aci, a tsawace yace "ba magana nake maki ba", tsorata tayi ba tare da ta shirya ba ta rufe system din ta mike ta yi kneel kan gadon bata ce komae ba, fixgota yyi tayi 'yar kara ya dago ta da sauri tun kan ta kai kasa, tsayar da ita yy gabansa ya ciro wayanshi a aljihu ya haska fuskanta, a hankali tace "bana jin yunwa" d'an k'aramin bakinta dake motsawa yabi da ido, hka kawae gabansa ya shiga faduwa yana kallonta, ita kanta faduwa gabanta ke yi a lkcn, duk kamshin turarensa ya cika ta, kashe wutan wayar yyi ta juya a hnkli xata bar wajen ya fixgota ta fado kansa, runtse ido tayi a tsorace tace "Ya Abuu ni bna jin yunwaa" D'ago kanta yyi amma taki bude idonta, kallon lips dinta kawae yake cikin duhun ko kiftawa bae yi, murda kofar dakin aka yi, ya tura ta da sauri ya koma baya, ita kam rawa jikinta ya dau yi, da sauri ta haye kan gado, ya kunna fitilar wayarsa, Ajiddeh ce ta shigo ta tsaya tana kallonsa tace "Wae me kke a nn Babe?" Tana masa tambayar tana kallon Batuul da tayi kmr me bacci, Abuturrab ya juya yana kallon Ajiddeh yace "Erm dama amma ce ta kira wae a bata shine na shigo naga tana bacci" hade rai tayi tace "Toh ita bata da waya ne da sae kai xa ace ka bata" ficewa yyi daga dakin ba tare da ya tanka ta ba, sae dae tunawa da yyi ba mutunci gare ta ba yasa ya tsaya daga bakin kofa yace "Mu je" tsaki tayi ta fito daga dakin. Batuul ta sauke ajiyar xuciya ta mike ta rufe kofarta da key ta dawo ta kwanta.
Washegari Batuul na gaban mirror xaune tana shafa lotion don fitowarta daga wanka knn, taji ana bude kofar dakin, turo baki tayi ta jawo hijab da sauri ta sa, yana shigowa yyi mata kallo daya yace "Daga yau, duk safiya kika tashi kafin kiyi shirin sch ki sakko ki tsaftace gidan gaba daya, snn breakfast da dinner ke za ki dinga yi ba kuma wa cikin ki kadae ba, is dat clear?" Shiru tayi tana kallonsa a hnkli tace "Idan ina da lecture da sassafe fa?" Ya galla mata harara yace "Sae ki tashi da asuba!" Juyawa yyi ya fice, ji tayi kmr ta fara kuka, yaushe ne xata tsaya hada breakfast a gidansu tana da lecture da safe, a sanyaye ta mike ta ciro doguwar riga na kanti pink da adon blue ta sa ta fito, bbu kowa falon ta nufi kitchen, breakfast ta hada cikin kankanin lkci na fried Irish da soyayyan kwae sae ruwan Lipton, ta jerasu kan dinning, ta koma kitchen din ta wanke utensils din da ta bata ta gyara kitchen din ta fito, falo ta shiga nan ma duk ta share tayi mopping ko ina, falon ya dawo yana kyalli, dakinta ta koma, ta kuma shiryawa tayi rolling kanta da plain mayafin kayan jikinta blue, ta shafa chappette a lips dinta ta feshe jikinta da turare, ta fiddo flat shoe dinta ta sa, sannan ta dauki jakarta bayan ta sa wayarta a ciki ta fito falo, har lkcn bbu kowa falon, kallon agogo tayi taga har tara ya kusa, duk taji kmr ta rusa kuka to ta ina xata fara ce masa xata tafi suna dakinsu, ta kusa minti goma tsaye falon wata xuciyar tace kawae tayi wucewarta da kafa tunda bbu nisa sosai, amma ta kasa aikata hakan sbda tsoronsa, hawaye na ya cika idonta sanin da wuya ta samu 1st lecture, tara dai dai ta koma sama ta shige dakinta ta fada kan gado ta dinga rusa kuka kmr yarinyar, tara da minti sha biyar Abuturrab ya fito har xae sauka downstairs sae kuma ya nufi dakinta, har lkcn tana kwance tana kuka, ya karasa cikin dakin ya tsaya daga bakin gadon yana kallonta da mamaki yace "Me ya faru" kauda kanta tayi taki basa amsa, yace "Ke kina da hnkli kuwa ina maki magana kina kauda kai" wani sabon kukan ta fara, ba tare da yyi wani tunani ba ya xauna gefen gadon ya d'agota yana kallonta da mamaki yace "What's that, what happen?" Still taki cewa komai bata kuma fasa kukan ba, ya dafa kafadunta yace "Talk to me mana, an maki wani abu ne wae?" Ganin ynda ya tsare ta da ido yasa ta shiga girgixa masa kai sae dae bata ce komae ba, jawota jikinsa yyi ya dago kanta ya hade rai yace "Idan baki bude baki kin min magana ba I will slap yhu" ta sauke idonta kasa wani sabon hawayen ya xubo idonta a hnkli tace "Am late, nayi missing 1st lecture" kallonta ya tsaya yi ko kifta wa bae yi, ya dake yace "What made yhu late?" Shiru tayi bata ce komae ba, yace "Yhu are not deaf fa, ansa me now" a hnkli tace "ko ba kai bne!" Bude idonsa yyi yace "Ni?" Kauda kanta tayi ya juyo da ita da sauri ya hade rae yace "daki daya muka kwana da xan sa ki latti? Ohh har kin kirkiro wani karyar da xa ki ma Ammah ki hada ni da ita koh, wae yhu are late! Did yhu sleep in my room ne xaki ce yhu are late or tunda kika tashi yau kin tsinana mu da wani abu ne a gidan nn, No of course u are just busy sleeping" sake kauda kanta tayi ita ma ta hade rae, ya juyo da kanta yace "Kika sake dauke min kai I will slap yhu wllh" rufe ido tayi da sauri, yyi shiru yana kallonta, sauke idonsa yyi kan lips dinta, hka kawae gabansa ya shiga faduwa, ita kanta Batuul faduwa gabanta ya shiga yi idonta rufe, without thinking twice kawae ya samu kansa da kai lips dinsa nata, a tsorace ta bude ido jin soft lips dinsa a nata, dai dai lkcn da suka ji an bude kofa, mikewa yyi da sauri ya k'asa kallonta, ya nufi kofa, suka kusan cin karo da Ajiddeh bakin kofar xata shigo, ae da sauri ya tsotse tsarabar chappette din da ya yo a lips dinsa, ta wani hade rai tace "Wae me kke dakin nn tun daxu Aliyu?" Daburcewa yyi da farko sae kuma ya wayance daga baya yace "Erm naga lkci ya wuce bata fito ba shi yasa na shiga in ga abinda take, nd nd.. I found her crying" Ajiddeh tace "Gskya idan kana son xaman lfya Aliyu ka daina shigowa dakin nn, bana so, idan tana bukatan abu ne ta jira idan muna falo ta sauko ta same mu" barin ta yyi a nn yyi ficewarsa, ta juya tana kallon Batuul ta galla mata hararan tsana tace "Munafuka kawae, 'yan maula" daga hka tayi ficewarta, ko kadan Batuul bata san me Ajiddeh ta gama cewa ba don har lkcn gabanta bae bar faduwa ba ji take kmr lips dinsa na nata har lkcn. Ta kusa minti sha biyar xaune sae gashi ya dawo, daga bakin kofa ya tsaya ba tare da ya kalleta ba yace "Idan kin ga dama ki fito driver ya kai ki sch" daga hka ya fice, mikewa tayi a sanyaye ta dauki jakarta ta d'an gyara fuskarta kuma snn ta fito. 馃挅馃æŒÂBATUUL馃挅馃æŒÂ
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.