Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 51 of 124

A gida can Ammah ta ha膹a kayan lefen Batuul Babban mota guda, su Aunty Amna da sauran Aunties 膹insu matane suka kai, su bakwai suka ha膹u sukaje, da mutunci aka karb'esu can gidansu Batuul 膹in, abinci kala kala aka shiga serving 膹insu, kowa ya ya6a ganin yawa da kyan kayan da Batuul ta samu, Basuci abubuwan da aka kawo musun ba sai juye musu Aunty tasa akayi, tukuicin 1million ta bawa Sisters 膹in Baba su basu, k'in karb'a sukayi har sai da Yayya ta saka baki tukunna suka karb'a sukayi godiya suka koma.

A can asibiti kuwa nurse ce ta shigo da saurinta jin bell 膹in yayi ringing, ganinshi tayi tsaye daga gefen gadon ya nuna mata gadon yace "call her doctor immediately" da sauri ta fita suka shigo tareda da doctor da stethoscope rataye wuyanshi da wani 膹an board haka a hannunshi, nurse 膹in kuma rik'e da wani k'aramin silver tray da allura akai, yana zuwa ya saka stethoscope 膹innan a kunnenshi yana 膹an gwada gudun pulse 膹inta, alama yayiwa nurse 膹in ta mik'o mishi alluran zai yi mata , ba shiri ta mik'e tana kuka, sosai ta bawa likitan wahala da Aunty Hafsat dake k'ok'arin rik'eta itama, yana tsaye jikin bango yana ganin shure shuren da take tayi, ganin taqi tsayawa ne yasa shi matsowa gaban gadon ba tare da yyi wani tunani ba ya kwanto da ita jikinshi, cikin ra膹a yace mata "I will slap you idan baki tsaya kin dena bawa mutane wahala ba", lamo tayi jikinshi gabanta na faduwa, har sai sai da aka tsikara mata alluran ta da膹a k'ank'ameshi ssae tana hawaye, bai 膹agata daga jikinshi ba bayan likitan yayi mata allura itama dae kasa tashi tayi don duk bata da karfi, a nan jikin nashi bacci ya 膹auketa ya shimfi膹ar da ita ya dubi Aunty Hafsat dake ta kallonsu da sha'awa don sae ka rantse masoya ne, yace zaije gida ya dawo.

Sai yamma Aunty tazo tare da Baba, a kan gado suka tarar da ita tana bacci, daga bakin gadon Baba ya tsaya yana kallonta, sosai ya tausaya mata ganin yadda ta rame ta k'ara haske, hannu ya 膹aura kan goshinta ya tottofa mata addu'a, snn ya ja kujera ya zauna bayan ya gama ya kalli Aunty yace "Yaushe sukace zasu tafi da ita?", Aunty tace "D'azu dai da suka zo basu ce komai ba toh inaga sai gobe", Aunty Hafsat ce tace "Uncle a barta mana in ta warke sai su tafi da ita, amma yanxu ai bata jin da膹i", sai da ya gama jin abinda Aunty Hafsat tace yace "A'ah Hafsat, in kuma yana da abin yi a can fa?, in dae xa a sallameta ko xuwa gobe kawae su tafi ta warke a can din", tashi yayi ya fita yacewa Aunty zai je wajen doctor ya tambayeshi yaushe za a sallametan, ita Aunty bata cewa komai sai ido da ta bishi da, tausayin Batuul sosai takeji a cikin ranta, Babane ya dawo yace musu gobe doctor yace za a sallameta, a nan ya tafi ya bar Aunty da Aunty Hafsat, yana fita Aunty ta dubi Aunty Hafsat tace "Hafsat wlhy tausayin Batuul nake, ban tab'a kawowa zatayi aure so soon ba, sannan kuma ma mai mata, Batuul yarinya ce amma sun k'asa fahimtar abinda nake nufi" Aunty Hafsat ta girgiza kai da damuwa tace "Yaa Maryam ko ni yanxu jimamin abin nakeyi, danma dai naga Aliyun nada hankali da nutsuwa sosai, ko 膹azu shi ya taimaka akayi mata allura da k'yar", Aunty tace "dama nifa bata Aliyu nake ba, nafi kowa sanin Aliyu tunda rainona ne, matarshi nake jiyewa Batuul, familyn su basuda da膹i akan kishiya, bare Batuul da take yarinya, bata ma san meye kishiyar ba", ajiyar Zuciya Aunty Hafsat tayi tace "Yaa Maryam addu'a kawai zamu tayata yi, itama a sata ta dage da yin addu'a, duk abunda zatayi ta kasance shine a bakinta, kuma ai can zata ci gaba da karatu ko?", kai Aunty ta gya膹a tace "Ehhh haka Babanta yace, har admission 膹in wai ya nemata a can, yace gidan nasu ma da makarantar babu nisa, makarantar na Houghton street, gidan kuma na ST GEORGE'S, kinga da kanta ma ta rik'a zuwa", Aunty Hafsat tace "yawwa hakanma yafi kinga zata rage damuwa sosai in tana zuwa school, baza ma tana zaman gidan ba bare su ishi junansu har su samu misunderstanding, Allah dai ya basu zaman lafiya", Aunty tace "Amin ya Allah, sosai zansa ana yiwa Batuul addu'a , duk sati a rik'a mata sauk'an Qur'ani", Aunty Hafsat tace "Allah ya dai ya rufa asiri Yaa Maryam, Allah ya karemu daga sharrin duk mugun abu naji ko na gani", daga nan suka ci gaba da hirarrakinsu.

Sai dare Abutturab ya dawo tare da Ammah, Ammah ce ta fara shigowa yana biye bayanta, Batuul na cin abinci lokacin Aunty Hafsat na kishingi膹e kan sofa dake can angle, tana ganinsu ta mik'e ta zauna suka gaggaisa, Ammah tana tambayanta ya mai jiki, Kan gadon ta zauna ta jawo Batuul jikinta tace "Bitti ya jiki, kina samun sauk'i dai ko", kai Batuul ta gya膹a dan wani kunyan Ammah takeji yau, Abutturab dake tsaye Ammah ta kalla tace "kai baka yi mata ya jikine ka tsaya kana kallonmu", kallon Batuul yayi a takaice yace "ya jiki" hararanshi tayi ta 膹auke kanta cike da jin haushin alluran da ya rik'eta yasa akayi mata daxu, mamakin hararanshi da tayi yayi ya girgixa kai ya 膹auke idonshi daga kanta, sunfi minti talatin wajen Ammah sai nan nan take da Batuul ta rasa ina zata sa Batuul 膹in, shi dai kujera yaja ya zauna lokaci lokaci yake 膹aga kai yana kallonsu, suna ha膹a ido take hararanshi, daga baya dariya ma abun ya fara bashi, mik'ewa Ammah tayi tace "Bitti zamu tafi kinji, Allah ya k'ara lafiya, Aunty Hafsat ta fita rakata shi ya tsaya daga baya, kallonta ya tsaya yi amma taqi 膹agowa ta kalleshi, gabanta ya matso yace "kin gama harare hararen mara kunya, irin na fara sake maki fuska a tunanin ki ko, Gud! yhu had beta stop decievin ur self coz am still the Abuturrab yhu knw!," bata 膹ago ba dan mugun bugawa zuciyanta yake, ya dago kanta yana mata mugun kallo yace "Baki ji na ne?" Kuka ta saki kmr jaririya tana kallonsa, ya koma baya da sauri yana kallonta da mamaki, ya buda manyan idonsa yace "Na maki wani abun ne? Daga magana?" Kin cewa komae tayi sae kukan da take, mamaki ya sa shi k'asa cewa komae, can ya sauke ajiyar xuciya ya runtse ido yana shafa kansa murya can kasa ba tare da ya shirya fadin hkn ba yace "ohkk srry!" Lkci daya ya bude ido jin abinda bakinsa ya furta, D'ago kai tayi tana kallonsa ya maka mata harara ya nufi kofa da sauri, ta bi sa da kallo har ya fita kafin ta tabe baki tana share hawayen fuskarta, lkci daya jikinta yyi sanyi qalau tunawa da tayi ynxu fa ita matar Abuturrab ce, tafiya fa xae yi da ita ya raba ta da iyayenta da 'yan uwanta ya kai ta garin da bata san kowa ba, ta fashe da matsanancin kuka ta fada kan gadon tana tausayin rayuwarta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.