Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 45 of 124

Aunty na komawa gida tasa aka kawo mata Aabid dake wajen Fa'izah ta bashi abinci, dan rabonta dashi tun jiya da Batuul ta zama unconscious, tana gama bashi ta mik'ashi ta shiga yin wanka, fitowanta kenan daga toilet taga Baba zaune akan gado, har ta 膹an tsorata, ganin shine ta k'arasa fitowa daga toilet 膹in, dubanshi tayi taga ita yake bi da ido, ce mishi kawai tayi "Uncle sannu da zuwa", snn tayi gaban mirror, kwaso mayukan da zata shafa tayi ta dawo bakin gadon itama ta zauna, Kallonta yayi yadda takeyin abu kamar bata san yana 膹akin ba, hannunta ya rik'o tare da cewa "Maryam", bata 膹ago ta kalleshi ba tace "Na'am", yace "ya jikin Batuul 膹in, waye a wajenta", k'ok'arin maida hawayen dake shirin zubo mata tayi a hankali tace "Abu na wajenta, wanka nazo inyi in kai mata kayan da zata canja itama", matsowa yayi kusa da Aunty ya jawota jikinshi, hawayen da take ta k'ok'arin maidawa ne ya shiga zubowa, kuka sosai ta shiga yi mishi, patting bayanta ya shiga yi , bai hanata ba har sai da ta 膹an tsagaita dan kanta tukunna ya 膹ago tareda da k'iran sunanta, ajiyar zuciya tayi tace "ina jinka", yace "Maryam yanxu akan nace zanyi wa Batuul aure shine kika bi kika 膹agawa kanki hankali?" yayi tambayar yana kallonta, ganin tak'i magana sai hawayen dake zuba daga idanunta yasa yace "auren nan da zatayi kamata yayi kifi kowa murna, wannan yaron 膹anki ne, kinfi kowa sanin waye shi, ke da kanki kinsan babu wanda Batuul zata aura hankalinmu ya kwanta da yafi Aliyu, da bakin ki kin yabi nutsuwarshi, toh sai yanxu dan zai auri y'arki shine kike qi, wani hali garesa da har baki son ba shi 'yar ki? Naga dae auren nan ko ba yanxu ba dole ta yishi, toh meye amfanin a barshi nan gaban bayan yin hakan shine gatan da zamu iya yi mata, kuma shine rufin asirinta da namu baki 膹aya, inma karatunta kikeji, da kaina zan sa a nemo mata admission a can inda zatayi auren, babu abinda zai tauye mata karatun ta, kiyi hak'uri kiyi mata addu'a Allah ya bata zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk inda zata tsinci kanta", jikinta ne yayi sanyi har yanxu hawayen na ci gaba da zubowa ta shiga gogewa cikin sheshek'a tace "Uncle Batuul k'arama ce fa, batasan meye aure ba bare abinda ke cikinshi, kuma fa mai mata zaku aura mata, abin ai zai yi mata yawa, kai da kanka kasan yadda Batuul ke da rauni, haka zataje a cutar da ita tunda ita ba wani wayo gareta ba", murmushi yayi tareda 膹agota yace "yanxu naji dalilinki na k'in auren, bakiso y'arki ta auri mai mata saboda kema ke ka膹aice gidanki ko, nima 膹in ai zan k'ara", da sauri ta 膹ago tana kallonshi ya sake jawota jikinshi yana murmushi yace " Be optimistic Maryam, in kika nuna tsoron kishiya y'ar taki kuma tayi yaya, addu'a zakiyi musu Allah ya ha膹a kansu ya basu zaman lafiya, shi kuma Allah ya bashi ikon rik'esu da amana, sannan Batuul fa University take, tana second year 膹inta, kinga ba yarinya bace, she is matured enough, she can decide what is wrong and right, tasan abinda zai cutar da ita da wanda zai amfaneta, mubita da Addu'a Allah yasa hakan ne mafi alkhairi", ya fa膹a yana goge mata hawayenta, da haka Baba ya rarrashi Aunty har ta hak'ura da zancen auren, tace Allah sa hkn shine mafi alkhairi.

Su Ammah na isa gida tayi summoning chefs guda biyu, mace 膹aya dattijuwa sai 膹ayar budurwa, order ta shiga basu na abinda takeso a dafawa Batuul kuma kar su 膹au lokaci, waya ta 膹auka ta k'ira Farida data haura sama, ba jimawa ta sauk'o, Ammah tace mata "je ki 膹auko min computer yanxu kizo kimin ordering wasu abubuwa, babu b'ata lokaci Farida ta haura sama bata jima ta sauk'o rik'e da Macbook 膹inta ta 膹aurashi kan table 膹in dake gaban Ammah sannan ta samu waje daga k'asa wajen k'afan Ammah ta zauna ta bu膹e system 膹in tana k'ok'arin jonawa da internet, sai da ta gama taga yayi connecting to internet ta 膹ago tace "Ammah mey zakiyi ordering, Jumia za a shiga ko konga ko kuma universal shopping zakiyi? ta dubi Ammah tana dariya, zama Ammah ta gyara tace mata kayan lefen Abu nakeson ha膹awa, lokaci ya k'ure bazan samu aje a ha膹o kayan ba, shiyasa zanyi ordering komai", da sauri farida ta kalleta tace "Ammah wai auren nan dagaske kukeyi sai anyi, rashin lafiyan nan mafa da take nasan lbrn da taji ne ya sata" harara Ammah ta maka mata tace "sannun gyatuma, ai fimu son Batuul 膹in kikayi, in baza kiyi abinda na saki ba tashi ki bani waje in Sadiq yazo anjima in sashi yayi min, xancen banxa kai", jiki a sanyaye tace "zanyi Ammah,mey za a duba miki yanxu, tace "customised designer akwatuna nakeso kimin order, wanda babu wani da za a sake yiwa irinshi sai ita", murmushi Farida tayi ta shiga surfing sai gashi ba b'ata lokaci tace "Ammah gasu nan da hotunansu, wai akwai na Macs n spencer, sai D&G, LV, Mandarina Duck, Versace, paclane, cartier, ralph Lauren da BOSS, Ammah suna da yawa mafa", sai da Ammah ta karb'i Laptop 膹in ta ga pictures 膹in tace "ki zab'i ten best kiyimin ordern su, kije credit card 膹ina yana kan shelf a 膹akina ki dawo ki gama", Farida na fita Ammah ta 膹au waya ta k'ira Aunty Amna dake Paris, sai da ya kusa katsewa ta 膹auka, Ammah ce tace mata "keh kullum sai waya ya kusa katsewa kike 膹auka, watarana har ya katse ma ba a samunki", tace "Ammah wayan ne tana hannunsu Nawwal basa barina dashi, yanxu ma ita ta kawo min a guje", Ammah tace "toh yanxu duk bama wannan ba, turaruka nakeso ki siya ki turomin da English Golds, Diamonds, Inner wears, vanity sets sai English wears, sai perfumes, shoes, da nighties sai bags" da sauri Aunty Amna tace "Ammah ba dai auren Sadiq bane ya tashi ban sani ba, yaushe za ayi, wace ma matar", ta tambaya with so much excitement sounding vry surprised, Ammah tace "A'ah ba shi bane", Aunty Amna tace "toh waye za a siyawa kayan nan haka da naji kaman lefe", ta fa膹a excitement 膹inta na komawa ciki jin ba Sadiq ne zaiyi aure ba, cewa Ammah tayi "Aliyu ne zai k'ara aure", da mamaki Aunty Amna tace "aure kuma Ammah, yaushe yyi aure har yake son kara wani, wace matar da zai aura 膹in, kardai Abu ya zama mai son aure aure fa", cewa Ammah tayi "Amna auren Aliyu na farko ba amfani ne dashi ba", tas Ammah ta gama gayawa Aunty Amna yadda auren Abutturab 膹in na farko yake da dalilin da yasa take son ya k'ara auren, jiki a sanyaye jin abunda Ammah ta fa膹a mata tace "Ammah ni inace ma ni ka膹ai ya share baya nema, ashe har gidan ma hakane, toh Allah ya rufa asiri, wacece matar da xae auran yanxu", Ammah tace "Batuul", da sauri Aunty Amna ta karb'e tace "Batuul dai, Batuul 膹aya da na sani?", Ammah tace "k'warai kuwa ita", gu膹a Aunty Amna ta sa tace "Ammah dama yarinyar nan nada hankali, sosai nakeson yarinyar tana birgeni, Toh Allah ya tabbatar da alheri, yaushe ne bikin, idan yara na hutu sai muzo kawai gaba daya" Ammah tace "ai next week kenan 膹aurin auren, biki ko daga baya ne sai ayi", da mamaki Aunty Amna tace "Laah Amma, everything so fast, toh shikenan, zan duba sauran, amma Ammah perfumes 膹in bazai yiwu su biyo plane ba, kuma in za ayi shipping zasuyi taking time, so akwai wani abokin Babansu Nawal yana da perfume shop a Aminu Kano crescent, yayi sabon order recently, so kawai zan mishi magana ya kawo har gida, inma container zaki duba, that will be better sai ku zab'a mata, amma sauran yanxu zan shiga in dudduba", Ammah tace "toh shikenan Amnah, zan turo miki ku膹in sai kiyi siyayyan, yanxu zansa Farida ta turo miki sizes da details 膹inta tunda k'awartace tasan komai", da haka sukayi sallama, suna gamawa ta shiga k'iran mai gold 膹inta dake Dubai, yana 膹agawa shima ta bashi order 膹in Gold har na wajen 50 mil zai turo mata samples in ta zab'i wa膹anda take so sai a sakosu a jirgi a turo, shima da haka suka rabu, Farida ganin Ammah dagaske take kuma tasan kayan da k'awatar tafi so tace "Ammah a saka mata abaya a ciki, tana sonsu sosai", Ammah tace sai ki dubo mata suma online shima ki mata ordering ko set 30 ne", sai da ta tabbata ta gama order komai har atampopi daga London tasa aka turo mata su sai laces da lappayu daga switzerland, sai da tabbata ta gama tukunna ta tashi taje tayi sallah.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.