Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 113 of 124

聽 聽 聽
[12/1, 15:42] 80k: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

92

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

聽 Tunda Dad ya fita ya barta d'akin Kulthum Ajiddeh聽 bata sake cewa聽 komai ba, angle ta samu daga gefe ta zauna a takure, duk bayan minti d'aya sai ta duba wayarta tana jiran tsammanin k'iran, a hankali siraran hawayen ke bin fuskarta, rayuwarta a baya take tunawa, tun ranan da ta fara ganin Abutturab a school Allah ya d'aura mata sonshi, babu irin wahalar da batasha ba dan kawai ya fara koda kallonta ne amma yaqi, babu irin nacin da batayi akanshi ya nuna duk baisan abinda takeyi ba, gashi ko aboki d'aya bata tab'a ganishi tareda ba, shekarar da zai gama ita tana third year, sosai hankalinta ya tashi ganin har zai gama ya tafi, shawara ta yanke kawai na ta sanar da Mum, at first mum bata biye mata ba saida taji ko d'an waye shi d'in, lokacin ne Mum tace mata ko sau d'aya ta samu ya bud'e bakinshi yayi mata magana daga nan zasusan abin yi, baza ta manta ranar da suka shirya itada friends d'inta akan in taga ya shigo makaranta ran sunday ta shige gaban motarsa ba ya bigeta ko dan yayi mata magana ne, tunda duk Sunday a school yake yinta kuma babu mutane da yawa, hakan kuwa sukayi ranan Sunday babu mutane da yawa school, daidai ta hango motarsa ta tashi ta shiga drive way shikam da ya taho sam bai lura da ita ba, kiiiii ya taka brake, da hanzari ya fito, ranshi b'ace zai fara yiwa maishi fad'an rashin kula, sai a lokacin ya gane mace ya kad'e, duk nacin da take mishi baisa ya gane wacece ita ba, baki ya bud'e zaiyi magana ta fashe da wani irin kuka, babu sautin da yafi tsanar jin irin kuka bare na mace, duk masifar da ya kwaso kasa k'arasa yin ta yayi, kuka take sosai tana yarfe hannuwa dukda ba wani ciwo taji ba, d'aukarta yayi ya sata mota, friends d'inta na daga gefe sukayi mata signalling zata wuce, ido d'aya ta kashe musu alamun taji dad'in accomplishing mission d'inta, murna fal cike ranta tana jin ta jikinshi kamar lokaci yayi ta zama a haka, a mota ya sakata yace mata sannu daga haka ya fara driving, asibitin da yake zuwa can ya kaita aka dubata sukace bata wani ji ciwo ba amma sam taqi yadda ta taka k'afar, ya tausaya mata ganin yadda take kuka, Wheel chair yayi requesting da a bata, badan taso ba ta zauna Kai, sai da suka fito yake tambayarta makaranta zai kaita?, tace mishi kada ya damu ya kaita gidanta, yana tsaye bai shiga gidan ba yasa tayi waya aka zo aka shigar da ita, yana barin wajen da mortarsa
ta daka wani uban tsalle, tayi hugging kawayenta, take ta bugawa Mum ta fad'a mata duk yadda abin ya faru, tun daga lokacin suke asiransu kanshi, wasu suyi tasiri wasu baza suyi ba, lokacin da yazo mata da zancen aurensu suma ne kawai batayi ba sbd dad'i, kamar a mafarki takejin lbrn, tasan Aliyu baya mata son da har zaice zai aureta, son da yake mata baifi 2% ba cikin 100% d'in da take mishi, tsoron kada wani abu ya sa ta rasashi ta shiga neman maganin mallaka, duk inda tasan za a bata abinda zaisa Aliyu ya sota ita kad'ai har abada saida suka zagaya itada su Mum da Aunty Jainaba, wani hawaye mai d'umi ta share daga fuskarta tana ci gaba da tunani, tunda ta zauna Kulthum ke kallonta, a hankali taji muryarta tace "Komai yayi zafi maganinshi Allah, ki fawwalawa Allah dukkan lamuranki shi zai miki jagora", wani iri taji maganar kamar ma ba da ita akayi maganan ba amma sanin su biyu聽 ne kad'ai d'akin yasa ta gane da ita take, bata kulata ba har lokacin, da dare ma haka Ajiddeh bacci kad'an tayi, washe gari ne ganin yanayin Ajiddeh duk ya canja tace "Hauwa tunane tunanen nan da kuka duk da kikeyi matsala zasu k'ara miki, ki samu ki sassautawa kanki, bance ni ba ko inason sanin matsalarki ba, a ah, ki samu wani amintacce da kika yarda dashi kika san zai baki shawara mai kyau ki fad'a mishi matsalarki zaki samu sauk'i a ranki, ko da mahaifiyarki ce ko mahaifinki, zasu fahimceki ko da wacce iriyar matsala kikazo musu, kallonta kawai Ajiddeh keyi ta kasa ce mata komai, batasan komai game da matar ba amma daga yanayinta tasan bazata cutar da ita ba, tashi tayi ta fice daga d'akin tayi side d'in Mummy, masu aiki ne sukace mata Mummy tun da asussuba ta fita amma tace kada a bari ki fita ko inane, wani kallo ta jefeshi dasu kamar in tayi niyyan fitan zasu iya hanata, juyawa tayi ta koma side d'in can, a hankali ta fara magana ta shiga zayyanowa matar abinda ke damunta, matsalarta da kuskuren da duk ta aikata, batace dai asirin kisa sukayiwa Batuul ba, tace kawai na zubda ciki ne da kuma barin gidan sukayi mata

聽 聽 聽 聽 Da asuba shi ya fara tashi, bai tada Batuul ba dan yasan bacci bai wani isheta ba, kwanciyarta ya gyara mata snn yayi wanka ya zira jallabiya ya fesa turarukanshi masu sanyin k'anshi ya fita zuwa masallaci, a masallaci ya had'u da Abui da Sadiq, Bayan an idar da Sallah snn suka gaisa, Abui yana tambayanshi ya jikin Batuul ya amsa mishi da "Alhamdulillah taji sauk'i", Sadiq ma ya gaisheshi yayi mata ya jiki daga haka suka shigo gida kowa yayi side d'inshi, a hankali ya turo k'ofar d'akin,聽 da mamaki ya kalleta ta kunna bedside lamp tana zaune kan abin Sallah riqe da Qur'an tana karanta Suratul Qasas cikin muryarta mai dad'i, Ido ya lumshe ya bud'e snn ya shigo d'akin tareda mai da k'ofar ya rufe, tunda yake da Ajiddeh bai tab'a ganin ta tashi Sallah batareda ya fad'a mata ba, ko ya fad'a sai lokacin da ta ga dama take tashi tayi, da sauri ya kawar da tunanin Ajiddeh yayi da sauri, daga gefenta yazo ya zauna, godiya ya dinga yiwa Allah cikin ranshi da ya bashi Batuul, a zuci yana bin duk ayoyin da take karantawa, kamar yau ya fara jin Qissoshin Annabawa dake cikin surar jin yadda take karanto shi, har saida tayi kusan rabi snn ta rufe ta shafa addu'o'inta ta maida Qur'anin kan bedside drawer, a hankali ta juyo ta kalleshi tace "Ina kwana", wani farin ciki yakeji a ranshi da ganinta, ji yakeyi kamar ya d'auketa ya kaita wajen da babu kowa, inda babu abinda zai sameta sai farin ciki, ido ta d'an wara ganin yana kallonta bai amsa mata gaisuwarta ba tace "Yaa Abu ina kwana", sai lokacin ya lumshe ido ya bud'e yace "Waye malamin da ya koya miki Qur'an?", cike da farincikin tuna mata malamin da baza ta tab'a mantawa dashi ba tace "Malan Ahmad shine malami na, mey yayi?", ta fad'a tana d'an yatsina fuska yace "Har Tajweed duk shi ya koya miki?", ta kad'a kai tace "Har komai ma shi ya koya mana dukkanmu dasu Ahmad da Sa'eed", yace "Ya complete sunanshi yake and yana ina yanzu?", tunanin mesa yake son sani a hankali tace "Sunanshi Ahmad Abu Hamira Daiba, su Ahmad sun san聽 inda yake, nasan har yanzu yana koyar dasu", a hankali ya janyota jikinshi yayi wrapping duka hannayenshi jikinta yace "In na bashi kujerar Hajj da Umara this year yayi?", da sauri ta shiga k'ok'arin juyowa taga dagaske yake nufin abinda yake fad'i amma bai saketa ba saima k'ara gyara mata zama da yayi ya d'aura fuskanshi kan wuyanta, duk da hijab a jikinta bai hanata jin d'umin numfashinshi dake sata jin wani a iri a jikinta ba, da k'yar ta iya bud'e baki tace "Dagaske?", yace "Kuma a bud'e mishi Tahfeez, inaso in princess ta girma ya koya mata", ya fad'a tareda sauk'e聽 hannunshi kan cikinta, "Inaso in ta girma itama tana min irin k'ira'arki", wani irin juyawa tayi ta rungumeshi sosai, yana jin yanayin bugun zuciyarta, shima d'in sake rik'ota yayi, kamar mai jin tsoron abinda zata fad'a tace "I love you", ido ya lumshe ya bud'e yana jin kamar kullum ta zama magana da zata fito daga bakinshi, ta d'ago da sauri tana kallon fuskarshi tace "Yaaa Abu tun yanzu ka fara sani farinciki, am scared yayi min yawa and mayb you might change nan gaba", kallonta kawai yakeyi for seconds ya kasa ce mata komai, da k'yar ya iya samu yace "Baki yadda da son da nake miki ba ko?, baki yadda I can forsake duk wani farin ciki nawa for you to be happy ba ko?", kunya ce taji ta kamata, lafewa tayi jikinshi hannunta kan k'irjinshi tana jin yadda yake heaving a hankali tace "Na yadda, bana so ne yayi min yawa", bakinshi ya d'aura kan nata ya rufe mata baki, saida ya d'ago yace "You deserve all happiness, ki kwantar da hankalinki kinji, you have got me for yourself", shiru tayi lafe a jikinshi, d'agata yai cak ya kwantar kan gado yace "You need sleep, kwanta kiyi bacci", ya shiga k'ok'arin cire mata Hijab d'in dake jikinta zai gyara mata kwanciya, kai ta girgiza mishi tace "Yaaa Abu da sanyi, I don't want to remove the hijab", bai ce mata komai ba har saida ya cireshi sannan ya rungumota jikinshi ya ja musu duvet yace "I will keep you warm", murmushi kawai tayi tana tuna ranan da sukaje gidanshi a London yanda yayi keeping d'inta warm har ta gama duk abinda zatayi, a hankali ta matsa jikinshi ta gyara kwanciyarta, cikin kunnenta ya rad'a mata "are you still cold?", juyowa tayi tana fuskantarshi da kyau tace "Will you always keep me warm all the time?", ya saka hannayenshi duka biyun yana zagayeta yace "Always and forever", daidai lokacin ta tuna da Ajiddeh, tana son ta tambayeshi ina take tana tsoron kada ya sake mata fad'a kamar na ranan, a hankali taji yace "Yaushe zamu koma gida?", idonta a lumshe batareda ta bud'esu ba tace "Nanfa?", yace "This is Ammah's house", ta zumb'uro baki tace "Ni I want to stay here", yace "No gidanki kuma fa, wa zai zauna ciki?", tace "Inada gida ne ni?, d'ayan ai gidanta ne, d'ayan Kumar kace na love of your life ne", dariya yayi yace "So baki manta ba?", tureshi tayi daga jikinta tace "Ni kam ka dena min dariya, a nan zan zauna", yace "Toh bud'e idonki in fad'a miki wacece love of my life d'in?", kamar yana ganinta ta murgud'a mishi baki, juyo da ita yayi yace "Plsss mana, ki bud'e idonki in fad'a mki gidan waye?", a hankali ta bud'e idonta suna had'a ido tayi maza ta rintse su, dariya yayi ya d'agota yace "Fatima get up and listen, gidan nanfa nakine, I built it for the woman I will love, I designed everything for her, banida ra'ayin k'ara aure, I want to live with just a single wife and then Allah yayi Hauwa baza ta zauna gidan ba, then it was you, tun lokacin da akace zan aureki a raina nasa gidan zai zama naki, I then programmed everything ya koma naki, censor and all but God so kind you turned out to be the love I wanted, the love I wanted to give and take and there the house is yours, kinga sai mu koma ko tunda kinada gida, only I and you have access to wannan gidan", jin shirun yayi yawa a hankali ya k'ira sunanta bata amsa ba, da wayarshi ya haska yaga bacci take, murmushi yayi tareda pecking goshinta ya gyara mata kwanciya suka kwanta bacci

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.