Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 98 of 124

81

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Ta kai 10mins tsaye tana jiran ganin Abu ya fito amma har lokacin shiru, jikintane ya k'ara sanyi taja k'afafuwanta ta koma kan kujeran palon, in banda masu aiki dake kaiwa da komowa bata ganin kowa, ko Farida ma bata sake ganinta ba, haka nan ta zauna jigum sai sak'e sak'e take tana warwarewa, can bayan wajen minti ashirin ta jiyo motsi, da sauri ta wartsake daga gyangyad'in dake shirin d'aukarta, k'ofan ta kafawa ido, Abui ne ya fara fitowa kamar kullum yana cikin shigarshi ta girma, murmushin nan na fuskanshi, Ammah ce daga bayanshi sai Abutturab k'arshe, kamar wata mara gaskiya tana hangosu ta mik'e tsaye, a diririce ta bud'e baki da k'yar ta iya gaishesu, Ammah kam ko kallonta batayi ba bare ta amsa mata gaisuwar, Abui ne yace "Lafiya kalau, ya gida ya kuma mai jiki, ashe y'ar uwartaki bataji dad'i ba", murmushi ta k'irk'iro tace "Alhamdulillah, tama fara jin sauk'i", Abui ya kad'a kai yace "Allah ya bata lafiya yasa kaffara Ne", daga haka yayi hanyan waje tareda Abu, itakam tsayawa kawai kallonshi tayi ganin ya fita baice mata komai akan tafiya gidansu da zatayi ba, haka ta koma ta zauna jiki a sanyaye kamar ta kurma ihu, wayarta ta ciro cikin jaka ta kunna ta, kamar jira ake ta kunna nan da nan msgs suka fara shigowa kuma duk yawancinsu daga Mum ne, ignoring d'insu tayi baki d'aya ta mik'e tayi d'akin Abu.

Ammah kam na hawa sama bayan fitansu Abui d'akinta ta wuce kai, Batuul na kwance abinta tana bacci kamar ba itace d'azu ke kukan ba, amma da gani baccin baya mata dad'i, daga gefenta ta zauna tana kallon yanda ta k'ara haske tayi kyau ta rame, hannu ta d'aura saman goshinta taji babu wani zafi, kallon Batuul d'in kawai takeyi tana jin yadda tausayinta ke ratsata, yarinya k'arama da ita amma saida aka samu wani Mara imanin yayi mata wani abin, duniya babu kyau, babu ruwanka da rayuwar mutum amma idonshi yana kan naka rayuwar, in banda rashin adalci da rashin tausayi meye ma Batuul da har za ayi mata asiri, babu komai da izinin Allah sai aikinsu ya lalace, a hankali ta furta "sannu Fatima, Allah ya baki lafiya", sannan ta mik'e ta bud'e closet d'inta ta ciro wani d'an kwalba mai d'auke da ruwan Zamzam ta dawo bakin gadon ta bud'eshi ta tsiyaya kad'an a hannunta ta shafawa Batuul d'in a fuska, wani irin numfashi taja jin ruwan a jikinta, juyawa tayi ta gyara kwanciyarta daga haka taci gaba da baccinta, intercom Ammah ta d'auka ta k'ira d'aya daga cikin masu aikinta, babu b'ata lokaci d'aya daga cikinsu tazo, "inaso ki wanko min Baby cucumber, ki tabbatar ya wanku da vinegar snn ki tafasa fresh milk sai ki jefa cinnamon da cardamom kad'an kada a saka sugar, ki Juyo min a flask, bada dad'ewa ba, snn a d'ora soup d'in offal's", yarinyar dake sanye da uniform d'in cooks tace "okay Ma, za ayi wani abin ne kuma?", Ammah tace "No for now dai babu, ba kun d'ora lunch ba?", yarinyar ta kad'a kai tace "Ehh Ma", Ammah tace "toh shikenan kije ku gama wannan, and be fast", da sauri yarinyar ta amsa ta fice abinta,

Ajiddeh na zaune d'akin Abu duk abin duniya ya taru yayi mata yawa, ta rasa mey ma zatayi taji dad'i, har ga Allah ba son Batuul takeyi ba bare ma a matsayin kishiya amma batason ta zama silar mutuwarta, ko ba kishi musulmace kuma ta san hukuncin kisa kan musulmi, ita inda yadda za ayi kawai ayi koma meye a rabata da gidan amma banda kisan kai, ko haukatata ne ayi, gabanta na fad'uwa take kallon wayan da ta saka silent na ringing, tun d'azu ake k'ira amma ta kasa d'auka, da k'yar ta sa hannu tayi sliding ta kara wayar a kunnenta, tun kamin tayi magana taji muryar Mum na cewa "Dan ubanki tunda yarinyar kanwar uwarkice dole kiqi d'aukan wayata, wlhy Ajiddeh kina jina, kada ki kuskura raina ya b'aci kanki, wani abu ya shiga kanki ne shegiyar yarinya inace akanki nayi sa'ar haihuwa ashe wahalar banza nasha, toh tun wuri kisan abunda kikeyi tun kamin inyi maganinki" Kamar wacce za a jiyo maganan da takeyi tace "Mum mey yayi zafi toh hka, naji kiyi duk yadda kike so amma fa babu ruwana inta mutu, I just want to be happy, yanzu haka mun dawo Nigeria kan ciwon nata muna gidansu Aliyu yanzu haka", kirji Mum ta dafe tace "Naga ta kaina ni Zuwaira, yanzu dan uwarki Ajiddeh kina garin nan shine baki fad'a mana ko kizo gida ba, gidansu miji yafi miki dad'i ko, ina zansa kaina yau dan takaici ni Zuwaira, anya kanki d'aya kuwa Hauwa, lokaci d'aya ki juye ki zama wata sakarya sallamamiya, Wato Bilkisun asirce min keh tayi ko, Ta Allah ba tata ba, duk sai nayi maganinsu daga ita har y'ay'an nata, kuma ki tabbata kinzo gida yau", shiru Ajiddeh tayi tama rasa mey zatace, "Toh" kawai ta iya cewa ta katse wayan, tashi tayi ta fito daga d'akin tayi hanyan d'akin Ammah, saida tayi sallama snn tajiyo muryan Ammah na cewa "Bismillah shigo", tura k'ofan d'akin tayi ta shigah Ammah na zaune kan abin Sallah ta idar da Sallah kenan, waje Ajiddeh ta samu ta zauna tana kallon Batuul dake kwance, takai 5mins kamin ta iya bud'e baki tace "Ammah ya jikin nata?", Ammah ta kalli Batuul dake kwance snn tace "Bacci takeyi tun d'azun, kuma da izinin Allah zataji sauk'i", daga haka basu sake cewa komai d'akin shiru, Farida ce tayi sallama ta shigo, da mamaki ta tsaya kallon Ajiddeh, rabonta da ganinta a d'akin tun satin bikinsu da Yaa Abu, tab'e baki tayi ta k'arasa shigowa, daga gefen Batuul d'in ta zauna tana kallonta da tausayi tace "Ammah ya jikin nata?, ta farka tun bayan fitana?", kai kawai Ammah ta gyad'a mata alamar A'a, Hannu tasa ta kamo na Batuul tace "Allasarki bestfriend , you will get well soon kinji, In sha Allah", tacewa Ammah, "Ammah mu tafi asibiti mana, turawan nan duk ba aikin kirki sukayi ba, a kaita wajen Dr Zakaa tunda gynaecologist ne zai iya duba matsalarta, tunda cikinta take cewa kullum", Har saida Farida tayi shiru kamar baza tace komai ba can tace "Ai ciwon nata bana asibiti bane, Abui sun tafi tahowa da Ashiekh Zai mata addu'a ya gane mana matsalar", k'ululu cikin Ajiddeh yayi k'ara, gani kawai takeyi Ammah tasan abinda ke faruwa, har zufa taji yana tsattsafo mata, Farida tace "Subhanallah, Ammah Jinns ne suka tab'ata?", Ammah tace "tashi kije ki kitchen ki dubamin ko sun gama aikin da na sakasu, kice su hanzarta, banaso ta farka babu komai a kusa", "Toh", Farida tace tasa kai ta fice,

Lokacin dasu Abutturab suka fita kai tsaye airport sukaje d'auko Asheikh, shike tuk'a motar Abui da malamin a baya amma gaba d'aya hankalinshi na
Kan Batuul, wayan Batuul dake wajenshi ya katse mishi tunani jin yana ringing, dubawa yayi yaga ansa Anty with all sort of hrt Emojies, baiyi picking call d'in ba har ya katse, haka a karo na biyu ma bai d'auki wayan ba, uku da rabi suka iso gida, a guest side aka sauk'eshi, saida Abu ya tabbatar komai daidai snn yayi d'akin Ammah, so kawai yake yaga lafiya, a hankali ya tura k'ofan d'akin ya shiga, babu kowa cikin d'akin sai sanyi da k'anshi mai dad'i, har lokacin Batuul na kwance tana bacci, ajiyar zuciya ya sauk'e snn ya k'arsasa shiga, bargon ya janye bayan ya zauna daga gefenta,murmushinshi mai kyau yayi ganin cute face d'inta da ya k'ara haske, a hankali ya d'aga y'ar rigar dake jikinta ya tsurawa flat tummy d'inta ido, hannunshi yakai kai yana shafawa, bakinshi ya kai ya d'ora mata kiss kai a hankali ya furta "Your Mommah will get better soon kinji Lil princess", jin hannu jikinta yasa ta bud'e lumsassun idanunta tana scanning d'akin, murmushi ya sakar mata da yasa itama ta mayar mishi, da sauri yaga ta tashi ta zauna idonta tab da hawaye, tace mishi "Aunty", hannu yasa ya rungumota ya zaunar da ita kan cinyarshi yace "No Fatima kar ki fara, kiyi hak'uri kinji, kinga bakida lafiya, Aunty da kanta zatazo wajenki kinji, keda zaki koma gidanta ma gaba d'aya ko kin mantaa ne", k'ara widening smile d'inta tayi ta d'ago tana dubanshi tace "Bazan koma UK ba?", yana kallon idonta yace "a ba haka kikeso ba, kince in kin bani Babyna zan maidaki wajen Aunty", zumb'uro mishi baki tayi tace "Toh ai nafison gidan Aunty ne kuma kaine kace in na baka Baby zaka kaini", kallon d'an k'aramin lips d'inta da yafiso kawai yakeyi, yadda ta zumb'uroshi tana pouting, a hankali ya d'aura d'an yatsanshi kai yana zagayesu ya kafeta da ido yace "Will you miss me in kin koma gidan Aunty?", kai ta shiga gyad'a mishi da sauri kamar wata yarinya tace "Ehhen, sosai ma, you are kind ai, you have stopped being bad to me", dariya ta bashi yayi murmushi yace "Was I?", tace "Of course , but that was then ai, da fa ko bansan kana waje ba if nayi approaching wajen heart beat d'ina increasing yakeyi, it runs at a faster pace, I thought ma mayune suka kamani, Aunty kuma sai tayi ta cewa banida gaskiya, but daga baya sai ya dena, I don't know mesa?", matseta yayi jikinshi a kunne ya rad'a mata "Its same with me, duk Inda kike indai naje wajen toh I feel that restlessness, shiyasa I don't want you kusa dani but nima nawa ya daina, kinsan mey ya janyo duka haka?", jiki a sanyaye tace "A ah ni ban sani ba", yayi murmushi ya kamo d'an k'aramin hancinta yace "Its gonna be an assignment, shima sai kin nemo reason d'in before in kaiki gidan Aunty", ta kalli idonshi da ya fara canja kala tayi murmushi tace "Toh ai zan tambayi Aunty ta fad'amin", ya d'age girarshi yace "okay..., yanzu malami yazo yayi miki addu'a, kinga hospital duk ba asan mey ke damunki ba, kuma kinga in ya fara kina shan wahala, so we will try na Asheikh, he is a great scholar", tayi murmushi tace "But ai na warke, kaga I can even jump, dama d'azun kawai shine ya fara", ta shiga k'ok'arin mik'ewa zatayi tsalle, da sauri ya jawota jikinshi ya had'e rai yace "Baby mana, you will get hurt, da Babyn dake jikinki", ganin ranshi b'ace itama taji ba dad'i tace "Na dena toh, but ni ai ba baby bace, your other wife is baby, haka kake ce mata itama haka take qiranka", yayi murmushi ya lakuce mata hanci yace "Okay then you are?.....", ya tsaya kamar mai tunani, caraf tayi tace "Am Batuul", kai ya girgiza mata yace "Yeah nasan wannan, I want a name da ni kad'ai zan na k'iranki dashi", tace "Ni bana so just call me Batuul d'ina, nafisonshi", tayi maganan tana barin jikinshi, kamata yayi yace "Wait, ina zaki", tsuke baki tayi tace "Na gaji da magana ka tafi", ido ya wara yace "Yaushe kikayi magana, I was d one talking fa, do you know how much I missed you?", kamin tace wani abu ya had'e bakinsu, tun tana tureshi bataso har ta hak'ura ta biyeshi, jin an tab'a k'ofa yasata saurin turashi amma har lokacin tana jikinshi, Ammah ce ta shigo d'akin, da mamaki ta tsaya kallon Abu da batasan lokacin da ya shigo d'akin ba, raurau Batuul tayi zata sauk'a daga jikinshi amma yaqi sakinta, Ammah ce tace "Kai yaushe ka shigo, yarinyar ba lafiya tana bacci shine saida ka tadata dan neman magana?", murmushin jin kunya yayi ya shiga sosa kai yace "Ammah ki tambayeta bani na tasheta ba, zaune nazo na sameta tana game", Batuul kam nok'ewa ta dingayi wai ita kunyan Ammah, ido ta wara jin abinda ya fad'a, da sauri ta sauk'a daga jikinshi, Ammah tace "Bitti ya jikin, yayi sauk'i kenan", da k'yar Batuul ta iya gyad'a Kai, Ammah ta k'araso gaban gadon tace "Tashi kici wannan zaisa kiji dad'in jikinki, tun d'azu nake jira ki tashi", Ammah ta mik'o mata plate d'in baby cucumber da akayi slicing akayi cling filming, sannan ta tsiyaya mata fresh milk d'in dake ta k'anshin Cinnamon da cardamom, kasa karb'a tayi sai Abune ya karb'a yace "Ammah ai baza taci ba, sai na bata", Ammah ta hararesa tace "Make sure taci, Asheikh ne yace a fara bata, tasha madaran sosai", yace "In sha Allah" daga haka Ammah ta juya ta fita daga dakin, mikewa yayi ya kuma jawota jikinsa ta fashe da kukan karya tana cewa "Ya Abu ni bana son haka gashi kasa Ammah ta gan ni naji kunya" ya wara idonsa yace "So? Ae bari ma ta dawo ta hada mana ruwan wanka in maki" cusa kanta tayi kirjinsa ta rufe ido tana kai masa duka tana kukan karya, ya kai bakinsa a hankali kan wuyarta ya lumshe ido murya can kasa yace "I... I like you..." Da sauri ta bude ido tana kallonsa, ya wara ido ya shafa cikinta yace "Yes I like my baby"
[12/1, 15:42] 80k: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.