Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 72 of 124
Kai tsaye d'akin Batuul yaje da ya koma gida, kwance ya tadda ta tana bacci abinta hankali kwance, daga ita sai d'an bum short da crop top ta takure waje daya ga xanin ta a gefenta, yafi minti biyu tsaye yana kallonta daga baya ya janye idonshi ya bud'e closet d'inta ya Ciro mata dogon hijab, hannu yasa cak ya d'auketa, baki ta bud'e zata sa ihu ya matseta jikinshi, ajiyar zuciya ta sauk'e jin k'anshin turarenshi tayi lamo jikinshi sae dae gabanta faduwa yake, har sai da ya kaita mota sannan ya bud'e ya direta ya jefa mata hijab d'in da ya d'auko mata shima ya zaga ya shiga daga gefen driver ya tada ya bar compound d'in, kallonsa take a tsorace sae dae ta kasa cewa komae, a hankali ta saka Hijab dinta da ya jefa mata. 馃挅馃æŒÂBATUUL馃挅馃æŒÂ
57
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Driving yake ba tare da yace mata komai ba, duk ta takure cikin motar a tsorace, ga sanyi da takeji dan gaba d'aya wajen sai traces d'in snow ake, a hankali ta juyo kanta daga kallon waje ta kalleshi, wani irin kallo da ya sakar mata yasa tayi saurin d'auke kanta, idonta har ya cicciko, kanta ta kifa kan k'afarta ta sake k'ank'ame jikinta sabida sanyi, bata d'ago ba har sai da taji yayi parking tukunna ta d'ago kanta a hankali, inda ya kawo su tabi da ido tana kallo, xaro ido tayi ganin irin gidan dake gabansu, bud'e k'ofar motan yayi ya fita ya fara tafiya, bata yi yunk'urin fita daga motan ba har saida ya juyo yaganta zaune har lkcn, wani irin kallo ya watsa mata, sannan ya dawo ya bud'e motan, bata jira yace komae ba ta fito, ya kama hannunta, yana tafe tana binshi a baya, kalle kalle Batuul ta shiga yi ganin irin gidan da ya kawo su, don rabin gidan duk glass ne, sosai gidan ya mata kyau, duk wanda yayi designing gidan yayi k'ok'ari, baki ta tab'e da ta tuna shima d'in architect ne fa, amma gaba d'ayanta a tsorace take, stairs yabi da ita ya nufi d'akin da aka zuba kayanta, da mamaki tabi kayan da ido, ta d'ago kai tana kallonsa, kallonta yayi shima snn ya d'auke ido ya xauna ya fixgota ita ma ta xauna daga gefensa, wayarsa dake hannunsa ya kunna yayi danne danne snn ya mika mata, sai da ta kalli fuskanshi taga shima ita yake kallo sannan ta karb'i wayan a sanyaye ta kara a kunnenta, muryan Ammah taji tana cewa "Bitti ya gida?", a kunyace tace "Alhamdulillah Ammah, ina yini?", Ammah tace "Alhamdulillah Bitti, kinga kayanki sun iso ko?", sai da ta kalli Abu, taga kallonta yake sannan ta gyad'a kai kamar Ammah na gabanta tace "Ehhh Ammah, gasu nan na gani", Ammah tace "Yawwa akwai wani kwali a ciki anyi packaging, ki bud'e yanzu in miki bayanin abubuwan ciki da yadda zakiyi amfani dasu", "toh tace" sannan ta mik"e ta isa wajen da kayan ke ajiye, a hankali tace "Ammah kwalin ba d'aya bane, suna da yawa", Ammah tace "Ehhh k'aramin ciki zaki bud'e, manyan duk turarrarukanki ne ciki", tace "toh Ammah", karasawa tayi inda k'aramin kwalin yake ta shiga k'ok'arin bud'e kwalin, kasa bud'ewa tayi harda sauk'e numfashi, a hankali ta juyo ta dubi Abu dake zaune, kallonta shima yayi yaga tayi rau rau da ido, ganin yaqi cewa komai ta juya taci gaba da kiciniyar bud'e kwalin, d'an murmushi yayi ya mik'e ya isa inda take, k'anshin turarenshi da taji yasa tayi Saurin juyowa, kamin ta tashi yazo ta bayanta ya mik'o hannayenshi daga gaba kan kwalin, sama sama ta rik'a jin numfashinta jin sauk'ar numfashinshi kan wuyanta, still tayi har ya gama bud'e kwalin, bai bar bayan nata ba sai ma sake kwantowa da yayi, jiki a sanyaye ta d'auki wayan ta maida wayan kunnenta, sai da Ammah ta gama mata bayanin komai sannan sukayi sallama, wasu ma duk ba fahimta tayi ba jin numfashinshi na sauk'a jikinta yana sending shivers to her spine, a hankali ta shiga k'ok'arin tashi daga wajen, hannayenshi yasa ya zagaye waist d'inta ya sake matseta jikinshi, babu abinda zuciyanta keyi sae double flips lkci daya jikinta ya dau rawa, bakinshi ya kawo daidai kunnenta, a hankali kamar me rad'a yace "nan zaki bar kayan naki har sai ranan da matata ta yadda ki zama co_wife d'inta, batace mishi komai ba sai ma hawayen dake dad'a taruwa idonta, jin tayi shiru yasa ya juyo da ita, hawayen da ya gani idonta yasashi yin murmushi yace "kukan meye zakiyi kuma?", lumshe idonta tayi hawayen dake tare ciki ya shiga gangarowa, murmushi yayi yasa hannu yana goge mata hawayen da ya zubo mata, hannunshi ne ya kai kan lips d'inta masu d'umi, wani irin shock taji yabi spine d'inta kuma har lokacin bata bud'e ido ba, a hankali ya shiga zagaye lips d'in nata da hannunshi, har ya sunkuyo ya kaj bakinshi dai dai nata har tana iya jiyo sauk'ar numfashinshi kan fuskanta, kirjinta sai heaving yake, ta kuma ki bude ido, ko me ya tuna sai kuma ya mike ya kamo hannunta, sai a lokacin ta iya bud'e idanuwanta ta ganshi tsaye, mik'ar da ita yayi, ba musu tabi bayanshi har sai da suka sauk'o k'asa, sai da suka shiga kitchen ya sake mata hannu, wani irin breath taking view ta gani ta glass d'in kitchen d'in, a hankali ta shiga k'arewa kitchen din kallo, babba ne sosai, komai na aiki akwai ciki sai kitchen island daga tsakiya, wani smile ne da bata shirya yi ba yayi escaping lips d'inta, babu abinda tafiso rayuwarta irin kitchen mai kyau da girma, yana kallon fuskanta yace " You like it?", bata san lokacin da ta shiga gyad'a mishi kai ba, murmushi yayi yace mata "cook something light, am famished", bata ce mishi komai ba ta shiga matsawa daga gabanshi, farin ciki fal ranta ganinta cikin dream kitchen d'inta, dogon hijabin jikinta ta take ta kusa fad'uwa yayi saurin rik'eta, k'ok'arin cire mata hijab d'in ya shiga yi, sai lokacin ta tuna da kayan dake jikinta, maza tayi ta rik'e hijabin, tace "No pls" kallonta yayi da lumsassun idonshi da yasata saurin sadda kai k'asa, a hankali ta bud'e baki tace "Yaa Abu kayan are too small ka bar min", bai bi ta kan maganan da take fad'amishi yaci gaba da abinda yake, kai ta shiga girgizawa zata fara hawayen nata tace "Yaaa Abuuu akwai sanyi wllh", har sai da ya janye hijabin jikinta, gaba d'aya jikin nata yabi da kallo daga ita sai d'an bumshort fari da sky blue crop top, lumshe ido yayi ya bud'e ganinta haka tsaye gabanshi, a hankali ta d'ago kai suna had'a ido tayi saurin sadda nata k'asa cike da kunya ganin irin kallon da yake mata, kasa motsawa tayi daga wajen, wani abu yaje ya danna ya k'ara temperature kitchen d'in to a higher degree, dawowa yayi gabanta ya daga mata kafada yace "you can start now, na rage sanyin", kasa motsi tayi ta tsaya, sai da ya sake mata magana tukunna ta juya jiki a sanyaye tayi hanyan fridge, waje ya samu ya zauna kan kujerun island d'in kitchen d'in, babu wani abun amfani na girki cikin fridge d'in daga fruits sai fresh milk da su cheese da kayan lashelashe, rufewa tayi ta koma gun cabinets d'in kitchen d'in, tuna fish ta fiddo da pasta da duk abubuwan da zata buk'ata ta shiga had'a Tuna spaghetti, duk inda tayi idonshi na kanta, a takure take aikin gaba d'aya, ga sanyi da takeji har yanxu, duk da bai kai na d'azu ba, lura yayi da yadda take shivering tana aiki, tsam ya mik'e ya shiga unbuttoning rigarshi, batasan ma me yake ba tana ta aikinta har ya gama sai jin mutum tayi ya rungumeta ta baya, a tsorace ta sauk'e ajiyar zuciya har sai da ya jiyo hakan, anya Abuturrab din da ta sani ne wannan kuwa, what is he doing haka, a kunne ya rad'a mata a kunne "this will help control d cold, I will keep you warm, don't you worry" bbu yabo bbu fallasa yayi maganar, lamo tayi jikinshi tana jiyo k'anshinshi me ddi da dumin jikinsa, ido ta lumshe sannan ta bud'e a hankali, fuskanshi ya d'aura kan gashin kanta da ke ta k'anshi, tana manne jikinshi a tare suka gama girkin, duk kamshin girkinta da na jikinta ya sauke masa kasala, Batuul kam k'asa gaskata cewar Abuturrab din da ta sani ne wannan a jikinta, is he this caring dama ko kawae yana da wata manufa ne a kanta, she just can't tell.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.