Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 17 of 124

K'arfe 6:30 mai shiryasu for prom tazo, sama suka hau da ita 膹akin Farida, tunawa sukayi da ba a kawo kayan Batuul ba, 膹akin Ammah taje ta fa膹a mata ta sameta tana waya, sai da ta jira ta gama waya sannan tace mata "Ammah har yanxu fa ba a kawo kayan Batuul ba kuma tana ta k'iran wayan Aunty not reachable", da damuwa a fuskanta ta tashi tace "toh muje in duba in Sadiq na nan ya kaita ta 膹auko ke kuma sai ayi miki kamin su dawo ko" wayan Sadiq ta k'ira yace mata baya gida, driver kuma sun fita da Abui, k'asa suka sauk'o , Abutturab ta gani a palo da remote a hannunshi yana kallon Fast8 a MNET, wajenshi ta k'araso tace "Abu, zaka kai Batuul gida ta 膹auko abu, tayi mantuwa ne", tsayawa processing wacece Batuul yayi dan yasan babu Batuul a gidan, sai da tace mishi "kana jina", ce mata Yayi "k'awar Farida ko, Ammah babu wanda zai kaita ne, ina drivers 膹in gidannan, ni yanxu ma nake shirin fita", ce mishi tayi "ai sai ka kaita ka dawo sai ka wuce inda zaka 膹in", ba dan ranshi yaso ba yace a ce mata ta fito, Farida ce ta koma sama a guje tace mata ta fito za a kaita su 膹auko, cikin hanzari ta tashi ta 膹auki hijab ta saka suka sauk'o k'asa a tare, Ammah ce tace mata "Bitti maza kije ku dawo da sauri", da toh ta amsa mata ba tare da tasan waye mai kaitan ba, parking space taje taga babu alamun motan da akwai mutum, horn taji daga gefe, anyi wining glass 膹in 膹ayan side 膹in k'asa, wajen wannan motan ta k'arasa , tana ganin Abutturab ne a ciki tace "innalillahi wa inna illaihi rajiun" a fili, "Yaa Abu da kai zamu tafi", mamakin salatin da tayi ya tsaya yi kamar na taga wani mugun abu, bai ce mata komai ba ya sa hannu ya bu膹e mata k'ofa , jiki a sanyaye ta shiga ta zauna, tun kamin ya tada motan yace mata "inane gidan", ce mishi tayi Gwarinpa, Tai Solarin crescent", bai ce komai ba ya tada suka fita daga gidan suka 膹au hanyan Gwarinpa
[8/22, 1:48 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

16

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Suna shiga Tai solarin crescent gidansu ne na uku by the right, maza tayi ta nuna mishi dan sun kusa wucewa, dan tsaki ya ja ya danna horn aka bu膹e musu suka shiga lokacin 6:50, fitowa tayi daga motan ba tare da tace mishi komai ba, shima fitowa ya bi ta da kallo yace "Dake ni drivern ki ne shi sa c'mon sense din ki bae nuna maki ki bude baki kiyi godiya ba koh" bae jira cewarta ba ya nufi masallacin dake jikin gidan don yin sallahn magriba, tsaki batuul ta ja ta kama hanyar shiga gida a xuciyarta tana cewa ae ba ni nace ka maido ni ba dae, shi kam yana zuwa bakin gate ya ha膹u da k'annen Batuul sun idar da sallah xa su shigo gida, gaisheshi sukayi ya amsa musu da smile a fuskarsa ya k'arasa masallaci, Batuul na shiga ta wuce 膹akin Aunty, a kan sallaya ta tarar da ita tana sallah, jiranta tayi sai da ta idar tayi azkars 膹inta sannan ta juya ta dubi Batuul, ce mata tayi " tun 膹azu fa Batuul na aiki Baa Liman ya kai miki kayan shine ya fita ya dawo nace yaje yace shi ya manta ma sam da aiken, kuma Baba na nemanshi a office, yanxu nake jiran Ahmad ya shigo ya kai miki wllh, cewa Aunty tayi "Ammah ce tace a kawoni dan har mai make up tazo" mik'ewa tayi tace bari inje in 膹auki kayan, Aunty ce tace mata mu sauk'a k'asa ai kayan ma suna can ba a hawo dasu sama ba , k'asa suka sauk'a suka k'arasa parlour, akwati ne mai kyau purple da bak'i na victoria's secret ajiye daga gefe, akwatin ta k'arasa ta 膹auka sannan suka fito waje tare da Aunty, "Batuul banda rawan kai a wajen don Allah ki kama kanki, event 膹in dare in banda ma na gama makarantane da bazan bari kije ba, kuma duk inda 10:30 tayi ku dawo gida keda Faridan, ku kula da kanku", "In sha Allah Aunty zamu kiyaye" a tare suka fito compound 膹in gidan da Anty, daga gefen gidan k'ark'ashin wani rumfa na bunu mai kyau da hasken wuta ya haska da farin florescent suka hango su Ahmad suna tennis, tsayawa Batuul tayi taga mutumin dake tare da k'annen nata ya rungume hannayensa yana kallon ynda suke buga tennis din with interest murmushi dauke fuskarsa, bata tab'a ganinshi yana murmushi ba sai yau, mamaki ne ya sata tsayawa dan tana ce ma ya tafi, Aunty ce tace "ba Abutturab bane wannan ko shi ya kawoki dama", juyawa tayi ta dubi Aunty tace "Eh shi ya kawoni" Anty tace "Batuul shine kika barshi a waje ko ruwa ba a kawo mishi ba, ke kam wace irin yarinya ce", cewa tayi "Aunty ban san zai tsaya ya mai dani ba", ganin Aunty da yayi ne yasa shi k'arasowa wajensu, a nutse yace "Aunty ina wuni", da murmushi ta amsa da "lafiya Abutturab, ya gida, mun saka aiki ko, ai bansan kana waje ba da an kawo maka ruwa", murmushi yayi yace "a ah Aunty ba komai, ai ba aiki bane, kuma inaga bata san bn tafi ba," ya k'arashe maganan yana kallon Batuul, k'in 膹ago kanta tayi sai da ya dena kallonta ta 膹ago, Aunty ce tace "toh maza kuje Batuul karki b'ata mishi lokaci, Allah ya kiyaye", tafiya sukayi suka isa inda motar ke pake bayan yyi ma Anty sallama, bu膹ewa tayi ta saka akwatin nata daga baya bayan ya bu膹e da controller hannunshi sannan ta koma gidan gaba ta shiga shima ya shiga ya tada suka tafi, dan tsaki ya ja can kasa a xuciyarta yace " Was i even suppose to wait for her" haushin kansa ya ji ssae, ko da yake wasan da kanninta ke yi ya tsaya kallo, yyi assuring kansa, babu wanda ya cewa kowa komai sai wak'an dake playing.

K'arfe 7:20 suka isa gidansu Farida, sauk'a tayi bayan yayi pakin ta zagaya ta 膹auko akwatin ta, tunawa da abinda yace mata daxu yasa ta hade rae tace "Na gode" ko kallonta bae yi ba ta ja akwatin ta ta yi gaba, yadda take jan akwatin ya gani kamar ta 膹auki wani abun mai girma, 膹auke kanshi yayi tare da jan tsaki har yazo ya wuceta ya shiga cikin gida, bayan shiganshi da minti biyu ta shigo janye da akwatin, mai aikinsu Farida, Fanne ce ta k'araso inda take ta karb'i akwatin tace mata "sannu", da mrmushi 膹auke a fuskanta tace "yawwa Fanne na gode", sannan suka hau sama, 膹akin Farida suka shiga suka sami Farida an mata kwalliya tayi kyau sosai, blue English gown ta saka da black accessories, tayi kyau ba ka膹an ba kasancewarta fara, "Masha Allah kinyi kyau Riri" inji Batuul, murmushi tayi ha膹e da batting lashes 膹inta tace "yeah i know", bata bi ta kanta ba ta wuce toilet tana dariyan ansa da Faridan ta bata, ruwa ta watsa sharp sharp, ta fito tana tsane ruwan jikinta da towel, mai ta shafa da sauri tazo ta zauna a gaban mai makeup 膹in, kayanta ta fara taimaka mata ta saka, red fench floral gown, sannan ta fara mata make up, red matte lipstick ta shafa mata, sosai Batuul tayi kyau, sai da ta gama da fuska sannan ta saka mata accessories 膹inta silver sai red agogo, gashinta ta gyara mata ya kwanto daga gefe, k'asan yayi curls, ba ka膹an ba Batuul tayi kyau, k'arfe takwas da sha hu膹u suka fito daga 膹akin sukayi 膹akin Ammah, tana ganinsu tace "Masha Allah kunyi kyau", a kunyace Batuul ta amsa tace "mun gode", k'asa suka sauk'o suna jiran mai kaisu yazo, Abutturab ne ya sauk'o daga stairs har ya canja kayan dake jikinsa ya saka ralph lauren shirt da blue sweats, k'afanshi sanye da slippers 膹in Fenty, hanyan waje yabi zai fita ba tare da ya kalli palon ba rike da makullin motarsa, mabu膹i k'ofan ya bu膹e zai fita yaji Amma na cewa "Abuu, don Allah ga su Farida nan zaka ajiyesu a Tulip bistro, tunda kai ma fita xaka yi, 8 ma ya kamata su tafi amma yanxu har 8:30, kuma bana so suyi driving da kansu, dare yayi", bai juyo ba saida yaji ta gama, shi bai ma san mey zai cewa Ammah ba, amma ransa yyi mugun baci, wato dae ysu shi ya xama drivern wa ennan yaran, cewa kawai yayi "toh" snn ya sa kai ya fita kmr xae tashi sama, tashi sukayi suka bi bayanshi, har bakin k'ofa Ammah ta rakasu tace musu kar suyi dare kamar yadda Aunty ta fa膹awa Batuul, hasken dake filin gidan ne ya haska Batuul, sai ya k'arawa accessories 膹in jikinta glitters, 膹ago kanshi yayi zai duba ko sun fito idanunshi suka sauk'a kan Batuul, tsayawa yayi yana kallonta da gashinta da yasha gyara sosai iska na swaying 膹inshi, yadda take tafiya yake kallo a hankali kamar baza ta k'araso inda motar take ba, wani takaici ya turnuke shi ya danna horn da karfi, Farida ce ta fara zuwa, shiga motan tayi ta zauna a gidan baya, ganin babu yadda Batuul ta iyane yasa ta shiga gaba dan 膹azu ma ce musu yayi shi ba driver 膹insu bane, k'anshin turaren Batuul ya nuna mishi cewa ta iso, ya dubesu su biyun ya daka masu tsawa yace "ina kuke tunanin zan kaiku haka da gashi a bu膹e kmr wasu mahaukata, ku fice min a mota kuje ku rufe kanku kuma kar wacce ta b'ata min lokaci, it seems kuna wasa da ni ne yau, duk gidan nn a rasa Wanda xae dinga yawo da ku a mota sae ni", Farida ce ta b'ata rai tace Yaa Abu toh Ammah ma bata ce komai bafa, kuma ma ai baza mu da膹e ba", harara ya jefa mata ta mirror ba shiri ta bude mota ta fita da sauri, Batuul dai batace komai ba dan ranta ya gama b'aci saura ka膹an tayi kuka , ta bu膹e k'ofa zata fita ita ma Farida tace "bari in dauko mana" hkn yasa ta koma ta xauna, kafin farida ta dawo Abuturrab ya ja tsaki fiye da sau goma, ita dae Batuul kanta na kasa sae wasa take da xoben hannunta, Farida na dawowa ta mi'kawa Batuul k'aramin jan gyale ita kuma bak'i, suna yafawa yaja motar suka tafi, hanyan Tulip suka bi, sai da ya tsayar da motan ya ce musu "duk iskancin da xa kuyi ku tabbatar by ten kun gama" Farida ta dan turo baki ta amsa mishi da "okay" suka fita daga motan suka shiga Cikin hall 膹in event 膹in, wajen ya ha膹u sosai kowane table kujerun mutum biyu ne da sunayensu a jikin kujerun, Runtown ne akan stage yake wak'anshi na Mad over you, anata ihu, Affan da Farida kujeransu 膹aya , kujeran Batuul ne kawai ita ka膹ai, sai kuma na wa膹anda suka je wajen rawa, suna zaune ana ta yin abubuwa har aka iso lokacin bada award, Batuul ce ta cinye cutest da most classy, Farida most beautiful, Affan kuma Ladies Man, bayan an gama raba sauran awards 膹in ne mutane suka hau wajen rawa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.