Batuul Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 78 of 124
Batuul ta kusa minti sha biyar xaune kan gadon bayan fitarsa ga yunwa da taji ta fara ji, mikewa tayi daga karshe tana share hawayen fuskarta ta nufi closet dinta, shiryawa tayi cikin y'ar gown mara hannu purple mai kyau, tana kkrin fiddo hijab da xata daura kan kayan ya shigo dakin, still tayi gabanta na faduwa, dad'da'dan kamshin turarensa ya cika dakin, a hankali ta juya tana kallonsa ta ga tsayawa yayi bakin kofar dakin yayi folding din hannunsa yana kallonta, maxa tayi ta dauke kai ta ciro hijab dinta xata sa yace " Drop that!" zumb'uro baki tayi tace "Ni sanyi nake ji" murmushi yayi yace "Did you just pout?", maza tayi ta maida bakin da ta zumb'uro ta girgiza Kai, karasawa yayi ya fizgo hannunta ta kusa fad'awa kanshi, bata ankara ba sae ji tayi ya hade bakinsu, sai da yayi kissing d'inta son ranshi sannan ya saketa, yana kallon idonta dake xub da hawaye yace "if you pout again, I will do more than this", hannunta ya kama tana hawaye suka fita daga dakin suka sauka downstairs, makullin motarsa ya dauka a palon sannan suka fita, shi ya bud'e mata motar ta shiga sannan ya zaga nashi side d'in, sai da ya tada sannan ya rik'o hannunta ya fara driving, a hankali yace "kin ma ci abinci yau kuwa?" Kin cewa komae tayi, yayi murmushi yana driving dinsa, har suka isa babu wanda yace komai sai murza hannayenta da yake cikin nashi, ganin gaban gidan da yayi parking yasata yin murmushi don haka kawae take son gidan ita dae, juyowa yayi ya dubeta ganin yadda fuskanta yayi lighting da murmurshi, hannu yasa ya juyo fuskanta tana kallonshi, a hankali ta sauk'e idonta kasa, giranshi ya d'aga yace "My wife's house, don't be over joyed being here uhh?", baki ta tab'e ta had'a rai ta janye fuskanta tareda bud'e motan ta fita, shima d'in murmushi yayi ya bud'e ya fita.
馃挅馃æŒÂBATUUL馃挅馃æŒÂ
63
By phartiemarhk
Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*
Had'e rai tayi tareda zumb'uro d'an bakinta ta tsuke shi tayi gaba ta bar sa nan tsaye, sai da taje bakin k'ofa ganin k'ofar glass d'in rufe yasa ta tsayawa, rau rau tayi da ido ta juyo xata kallesa suka kusa cin karo, sadda kanta tayi k'asa zata juya ya saka hannunshi waist d'inta ya juyo da ita, fuskanshi dab da nata har tana jin numfashin sa na brushing jikinta da kamshin turarenshi mai dad'i, ya dan wara mata ido yace mata, "mey ya hanaki shiga, ai na fad'a miki its my wife's house, ni kad'ai keda access to it, da kinace zaki iya bud'eshi ne", bakinta ta zumb'uro mishi ta d'auke kai zata juya, hannu yasa ya juyo da kanta yana kallon fuskanta yace "Did you just pout again", kai ta shiga girgizawa da sauri dan ita bata ma san tana yi ba cikin murya kamar zatayi kuka tace "Yaa Abu banyi ba, kayi hakuri", murmushi yayi ya d'auke idonshi daga kanta sannan ya jawo hannunta sukayi k'ofar gidan, hannunta ya d'aura kan security lock d'in dake mannne jikin bangon, k'ofan ne ya bud'e da kanshi, da mamaki ta kalleshi, smirking yayi tareda d'age mata girarshi d'aya, kauda kanta tayi kamar bataga abinda yayi d"in ba, hannunta ya kamo cikin nashi su shiga, tur jewa tayi nan gun taqi motsi, da mamaki ya juyo don ganin mey ke damunta, dawowa yayi gabanta yana kallon fuskanta yace "Are you okay", tsuke bakinta tayi ta juyar da kanta, hannunshi yasa ya juyo da fuskan nata tana fuskantar shi yace "Hey!, talk to me, what's wrong with you", raurau tayi da idonta taqi ce mishi komai, sassauta muryanshi yayi yace "mey ke damunki wai", baki ta sunkuyar da kanta cikin sanyi tace "you just said I shouldn't be overjoyed being here, its your wife's house, so why asking me wats wrong?", abinda ta fad'a da yadda tayi maganan ne ya bashi dariya amma ya dake, had'e rai yayi yace "and what does that have to do with entering in, in zaki shigo ki shiga, you are wasting my time", hawaye ne ya shiga taruwa idonta, juyawa tayi zata bar wajen, yasa hannu ya fixgota, cak ya d'agata ya rungumota, ko'k'arin sauk'a ta shiga yi daga jikinshi tana wuntsila k'afafu, matsetata yayi k'irjinshi sannan ya sunkuyo daidai kunnenta yace "if I should slap you right away, ina miki wasa ne", lamo tayi jikinshi ta rintse ido tana shak'ar k'anshin turarenshi mai dad'i, bata bud'e ido ba sai da taji ya direta kan lallausan gado, a hankali ta bud'e lumsassun idanuwanta ta sauk'e kansa, ya kwanta gefenta ya lumshe ido, kyakkyawan fuskanshi ta tsurawa ido, lumsassun hazel like idanunshi da lashes yabi ya kwanta, sai chiseled nose d'inshi, da d'an k'aramin plumpy pinks lips d'inshi, tab'e baki tayi ta d'auke Kai a ranta kuwa haushin kanta taji na kallonshi da ta tsaya yi bayan bama wani kyau bane dashi, a hankali ta sake juyowa bayan kamar 3mins, har lokacin yana kwance kuma bai bud'e ido ba, Idonta ne ya fad'a kan broad k'irjinshi da buttons d'inshi na sama guda biyu da suka bud'e, gabanta ya fadi ba kadan ba, a hankali ta dinga jin abu na yawo spines d'inta, rintse ido tayi dan batason cigaba da jin abinda take jin, samun kanta tayi da son jinta kwance jikinshi, ita kanta ta rasa gane dalilin hakan, ta kuma runtse ido xuciyarta na double flipping, dai dai lkcn da ya bude nasa ya juya yana kallonta, a hankali ya mirgina kusa da ita ya dagota ya mai da ita kan faffad'an k'irjinshi, kamar wacce akayi electrocuting a firgice ta bude ido ta yunk'ura xata sauka daga jikinsa, kamin ta sauka taji ya sako hannayenshi a waist d'inta ya dad'a rungumota jikinshi, ajiyar zuciya ta sauk'e tareda yin lamo tana jin yadda heartbeat d'insu ke gudu lokaci guda, hannu yasa
kan gashinta ya warware k'ullin da ta yiwa gashin, ya d'aura fuskanshi kan lallausan gashin nata yana shak'ar k'anshin da sukeyi mai dad'i.
Ajiddeh kam tun a airport tayi magana da Mummy tace mata suna Ndjamena, tana sauk'a airport a Nigeria ta sake booking wani ticket d'in da zai kaita har can d'in, awanta shida tana zaune kamin jirgi yazo suka tafi ko cikin gari bata shiga ba, taxi ta tara ya kaita har hotel d'in da su Mummy sukace mata sunyi lodging, kai tsaye ta wuce d'akin da suke bayan ta sallami d'an taxi, knocking k'ofar d'akin tayi ta tsaya tana jiran a bud'e mata k'ofa, Yaa Zee ce ta bud'e mata k'ofan, babu yabo babu fallasa suka gaisa tun daga bakin k'ofa, Mummy da Aunty Jainaba ne zaune d'akin hotel d'in, k'arasawa tayi itama ta zube kan makeken gadon tana maida numfashi, takai minti biyu a haka sannan ta mik'e daga kwancen da take tana kallon Mummy tace "Mum sannunku", sannan ta juya ta dubi Aunty Jainaba dake kallonta itama, murmushi tayi mata tareda mik'ewa tana k'ok'arin rage kayan jikinta tace "Mummy duk abinda zamuyi cikin kwana biyu zamu gama dan cewa zaiyi zai biyoni, dan da k'yar na samu ya hak'ura bai biyonin ba, jarababbe, dan haka yau da gobe ayi komai mu koma da wuri", baki Aunty Jainaba ta tab'e tace "Dan shi sarkin k'wak'war mata ai sai ya biyo kin, kwana biyun da zakiyi shine harda wani kuzo tare, ai ko da yaxon ma kuma babu abinda zai hanamu tahowa", Yaa zee ce ta taho riqe da can drink da ta d'auko fridge ta bayan ta rufe k'ofan, zama tayi tana kallon Mum tace "mummy kinsan mutumin nan appointment yake badawa, in bakazo ba time ya wuce sai dai a sake booking, Ku shirya mu wuce tun wuri kamin time d'inmu ya k'ure muyi asara, ba musu su Mum aka hau shirin tafiya, lokacin Ajiddeh ta fito cikin toilet d'aure da towel har ta watsa ruwa, itama shirin ta hau yi, suna gamawa suka fito waje, taxi suka tare sukayi mishi kwatancen inda suke son zuwa, babu b'ata lokaci ya fad'a musu amount d'in da zasu bashi sannan suka d'au hanya, tafiyar awa uku suka isa, driver ya tsaya dab inda suka mishi kwatance, gidane d'an madaidaici mai kyau, gabanshi da bayanshi kuma duk jeji ne, da mamaki Ajiddeh ta juyo tana kallonsu tace "nan ne gun?", kai suka kad'a mata a tare, cewa tayi "ca nake wajen wannan mutumin zamu koma na kwanaki", Aunty Jainabace tace "wa?, wa zai koma wajen munafikin nan, ai kud'inmu kawai yacinye babu wani aiki da ya iya, macuci ne, bok'an k'arya", (Lol boka ma harda na k'arya da gaskiya, Allah ya tabbatar damu kan shiriya), Ajiddeh ce ta ciro kud'in ta baiwa mai taxi kud'inshi, yana tafiya suka shiga knocking, mai gadine ya bud'e musu gate d'in gidan bayan ya gama yi musu tambayoyi sannan yayi musu jagora har palon gidan, palone babba, babu komai ciki sai carpet da aka shimfid'a su wasu throw pillows, wani farin dattijo ne zaune yana sanye da farin kaya da dogon farin gemunshi, gefenshi kuma littafai ne tuli guda, a tare sukayi sallama, saida ya amsa musu sannan suka shigo daga ciki suka samu waje suka zazzauna, shi ya fara yi musu magana kamar haka, "nasan abinda ke tafe daku baki d'ayanku, Keh!", ya nuna Yaa Zee yace "senator Gamji ke son aurenki amma yana da mata ku kuma baku son mai mata, ita kuma wannan", ya nuna Ajiddeh yace "tabbas akwai wani al'amari tattare da ita mai rikitarwa da ni kaina na kasa fahimta, abune babba da ya shige min duhu na kasa gano komai game dashi duk iyawata, kuma shi wannan abun na tare da ita dan har ya faru ya k'are sannan ba alheri bane gareta", a tsorace suke jin bayanin malamin da abinda yake fad'a musun, a d'arere mummy ta kalli malamin tace "Allah gafarta malan, wane abune haka har zaifi k'arfinka, mu nan munyi maka alk'awari daga miliyan goma har zuwa hamsin zamu iya badawa in dai aikinmu zai yi yadda mukeso, Allah gafarta malan, a taimaka a dubo mana wannan abun dake shirin jawo mana matsala", wani shu'umin murmushi yayi yace "ai ni d'in nan duk abinda kikaga banyi shi ba a fad'in garin nan toh tabbass babu mai iya yi dan ni keda iko ga kowanne aljani da muke amfani dasu, dan haka ku kwantar da hankulanku, anjima da yamma za a fara aiki, yanzu haka masauki za a kaiku kamin yamma tayi, su wad'anda za ayiwa aikin kowacce d'akinta daban, ku kuma za a had'eku d'aki d'aya ku da babu aikin da zaku buk'ata, Dan aikin nada son sirri", hakan kuwa akayi, wani d'an saurayi ne ya kaisu d'akunan da aka umurceshi da ya kaisu, y'an madaidaitan d'akuna ne masu kyau ba laifi, Zainab da Ajiddeh aka basu d'ad'd'aya kowannesu sai mummy da Aunty Jainaba aka had'esu a guda d'aya.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.