Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 63 of 124

Karfe biyar saura suna xaune ita da Samantha da wata Linda sae 'yar uwarta yar Nigeria Aisha, ba karamin farin cikin haduwa da Aisha tayi ba ko ba komae ta samu 'Yar uwa a makarantar, sae dae ita a hostel take, fitowarsu lecture knn suna ta hiransu ita kuma tana duba textbuk din hannunta, wani guy ne ya karaso inda suke yana kallonsu yace "Hi" duk suka amsa bnda Batuul da bata dago ba, xauna wa yyi daga gefenta yana kallonta yace "Assalamu alaikum!" D'agowa tayi da sauri tana kallonsa, sae a snn ta ga bahaushe ne me kyau, sunkuyar da kai tayi ta amsa masa sallamarsa, da harshen hausa yace "Ya lecture 'yar uwa" tace "Alhmdllh tnxx" ya d'an yi murmushi jin ynda ta amsa masa yace "Am Shaheed Mukhtar by name, yhu?" Wayarta ne ya shiga ring ta mike tana kallon screen din tace "Srry Shaheed, I will be on my way ynxu" kallon Aisha dake ta kallonsu tayi tace "Plss ki d'an rakani outside gate, driver ya xo dauka na" bata jira cewar Aisha ba ta shiga yi ma su Samantha sallama, daga nn tayi gaba da sauri Aisha ta bi bayanta, binta da kallo Shaheed yyi yana murmushi, sae da suka yi nisa Aisha tace "me yasa xa ki yi masa hka Fatima, kinsan waye Shaheed kuwa, a vry popular guy a makarantar nn, he's so intelligent, course din mu daya, nd he is in his final year, ni na yi mamakin ganinsa wllh, don bin sa 'yan mata ke yi ba shi ke bin su ba" Batuul tayi murmushi tace "Gskya ne" tana ganin motar Abuturrab ta gane ta juya tana kallon Aisha tace "Toh sae gobe idan Allah ya kai mu, thnk for ur company frnd" murmushi Aisha ta mata ta gyada mata kai, Batuul ta juya ta nufi motar, duk a xaton ta driver ne, har xata bude baya sae kuma ta fasa ta bude gaba, ido hudu suka yi da shi, ta sunkuyar da kanta, yace "Baki ga daman d'aga call din ba knn" shiga motar tayi ta rufe ya tada motar suka bar wajen, a hnkli tace "Ina yini?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Lfya lau" sae da suka kusa gida yace "Ya lecture" kmr an tilasta sa tambayar don can ciki yyi ta, ta kallesa tace "Alhmdllh" yana gama parking ta bude motar ta fita, sae dae bata yi gigin tafiya ba ta jira har ya fito, sae da ya shiga gaba ta bi bayansa, Ajiddeh na kwance falo ta kure Ac tana kallo sanye da kananun kaya as usual, a hnkli Batuul tace "Ina yini" Ajiddeh ta d'an saci kallon Abuturrab, ganin kallonta yake yasa tace "Lfya lau" sama Batuul ta nufa, ajiye wayarsa dake hannunta da long notes din da ta siya a makaranta tayi ta kwanta tare da lumshe ido, ta kusa minti goma kwance snn ta mike ta cire watch din hannunta da jewelry ta cire doguwar rigar jikinta xata shiga bayi tayi wanka, bude kofar dakin taji anyi ta juya a rikice suka yi ido huda da shi, xaro ido tayi ta durkushe wajen, ya dauke kai ya juya da sauri ya fice daga dakin.
[8/22, 2:18 PM] .: 馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

48

By phartiemarhk

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Yana fita ta mike da sauri ta rufe k'ofar 膹akin, har lokacin jikinta b'ari yake, she wasnt expecting anyone, komawa tayi ta zauna daga bakin gadon hannunta zagaye a k'irjinta duk kunya ya isheta, tafi minti biyu a haka daga baya ta mik'e ta fa膹a toilet, ta da膹e cikin bath tub 膹in kamin ta fito, a hankali ta lek'o kanta dan tsoro takeji kamar zataga wani a 膹akin, ganin babu kowa yasa ta k'arasowa cikin 膹akin, akwatinta na kayan shafa dake gefe ta cicciro wa膹anda take buk'ata ta shafa ta maidasu cikin akwatin, gown 膹in atamfa holland bak'a mai manyan patterns 膹in ja da purple ta saka, bata 膹aura 膹ankwalin ba , comb ta ciro daga cikin kayanta ta dawo gaban mirror ta shiga taje gashinta, sai da ta gama ta ha膹eshi in a bun, tunanin shirya kayanta dake cikin akwati a closet 膹in 膹akin tayi, bbu b'ata lokaci ta tashi ta bu膹e closet 膹in, tana bu膹ewa taga electric burner a ciki, sai da ta karka膹e k'uran wajen tukunna ta shiga jera kayayyakinta a ciki, sosai ta shiga gyaran 膹akin, har bedsheet ta canja wanda ta gani a cikin closet 膹in 膹akin, cikin lokaci ka膹an ta gama gyaran 膹akin ta kunna burner ta saka sandal woods, babu abinda 膹akin keyi sai k'anshi, sai da taga 膹akin ya koma yadda takeso sannan tayi ajiyar zuciya , fa膹awa tayi kan gadon tana maida numfashi, idonta ne ya fa膹a kan wayarshi da ya bata dake ajiye kan bed side drawer, hannu tasa ta dauko wayar, ta d'an tabe baki ta shiga gallery duk hotunan Ajiddeh ne wayar wasu da shigar mutunci wasu kuma bbu kyan gani, k'an wani hotonsa da yyi shi kadae yana xaune office ta tsaya tana kare ma kallo, yyi mugun kyau sanye da suit blue da fadin shirt daga ciki, murmushin sa me rikita Ajiddeh yyi a hoton Lol, Batuul tayi tsaki hade da tabe baki ta wuce hoton, wani hoton ta kuma gani yana sanye da farin 3qtr da farar polo, ainahin kyansa ne ya fito a hoton, ita kanta ta san yyi kyau amma hkn bae hanata kyabe baki ba, ajiye wayar tayi ta juya abun ta ta rufe ido kmr me shirin bacci.

Abuturrab na fita daga 膹akin dama dakinsa ya wuce, direct toilet ya shiga yayi wanka, tsakin da baisan dalili ba ya riqayi har ya fito daga toilet 膹in, sweatpant grey da farar shirt ya saka, zama yayi gaban system 膹inshi yana dudduba abubuwan da zaiyi, bayan wajen thirty minutes ya mik'e tare da jan 膹an siririn tsaki ya fita daga 膹akin dan ya fara jin yunwa, ko coffee ne zuwa zaiyi ya ha膹a kamin ya samarwa kanshi abinda zaici, tunda ya fito daga 膹akinshi yakejin wani k'anshi mai da膹i, lumshe ido yayi yana shak'ar k'anshin, sauk'a yayi k'asa yayi hanyan kitchen, Ajiddeh na kwance nan inda ya barta ta tasa bowl 膹in Tacos a gaba tanaci, 膹auke kanshi yayi cike da haushinta ya wuce cikin kitchen, coffee maker ya nufa ya ha膹a sannan ya fito, sama ya koma yayi hanyan 膹akin Batuul don ce mata ta fito ta samawa kanta abinda zataci, tun kamin ya kai ga shiga 膹akin yakejin k'anshin nan na da膹a k'aruwa, a aljihunshi ya fiddo makulli ya bu膹e 膹akin ya shiga, a figice ta mike daga kwancen da take dan tasan saida ta rufe k'ofarta kamin ta kwanta, lumshe ido yayi ya bude ya shiga bin 膹akin da kallo ganin yadda ta gyara shi yayi kyau, abinda dakinsa bae samu daga Ajiddeh ba, tashi tayi daga kwancen da take ta zauna tana kallonshi, kyab'e baki yayi ya k'arasa shigowa cikin 膹akin, gashin kanta da yasha gyara yabi da kallo, ita kam wasa ta shigayi da zoben hannunta zuciyanta na bugawa taqi 膹agowa ta kalleshi, kyab'e bakinshi ya kuma yi ya 膹auke idonshi daga kallonta yana da膹a bin 膹akin da kallo yace "abincin da zakici sai ance ki fito ki nemawa kanki?, ko dan ki samu na fa膽a wa Ammah cewa bana baki abinci", bata ce mishi komai ba kuma bata 膹ago ta kalleshi ba, sipping coffee 膹in dake hannunshi yayi yace mata "in kin gama zaman sai ki sauk'o ki nemawa kanki abinci don baki taho da Cook daga Nigeria ba", daga nan ya juya har xae fita ya dawo ganin wayarsa gefensa ya dauka, gabanta ne ya fadi tunawa da tayi a gallery take, kunna wayar yyi ya ga hotonsa, kallonta yyi yace "Ohh hotona ma kike kallo knn," dariya yyi yace "Lallai kina da wahala yarinya, xa ki iya kishi da matata?" Ji tayi kmr ta rusa ihu don takaici sae dae bata iya ta ce masa komae ba, yyi murmushi yace "Ae kam da kin gamu da aiki" daga hka ya fita daga 膹akin, bayanshi ta bi da kallo tareda da fadawa kan gado tana kukan takaici.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.