Complete Hausa Novels

Batuul Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Batuul Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 1 of 124

COMPILED BY
ESHAAT HOUSE OF HAUSA NOVELS DOCUMNTATION.
@08066360176 WASAPP 4 MORE

馃挅馃挐BATUUL

All Thanks to Allah (SWT) for granting me d chance,ability , previledge and knowledge to write this story. I dedicate this book to *KHALEESAT HAIDAR* (Maijidda) ,you have been an amazing writer,you make time for it everyday. You have set realistic goals,embraced the ecstacy of writing. You followed your heart not the market and fame. You don't just Start stories,you finish them,you dream big. You learn the rules,follow the rules and break them because rules are meant to be broken馃槄.Constructive, Criticism,Solicit,Accept and Manage. Put your ego in your back pocket and sit on it. Writing is 脿 Journey, not 脿 destination. Enjoy the scenery and give back to the writing community. WRITE SCARED. Remember you are the master of inspiration, not its Slave. Set your stories Free. Send them into the world .
DON'T SLACK ON THE HARD STUFF.
*PHARTIEMARHK* LOVES 鉂ゐ煉漎ou馃槝

Sanye take da Abaya baqa da yasha aiki da Swarovski stones ta yafo qaramin gyalen abayar ba tareda da wrapping dinshi ba kafarta sanye da slippers din vinci shima baqi mai Swarovski Stones din 脿 jiki .Siririyace sannan ba doguwa ba tana da shape mai kyau irin wanda ake kira figure 8 bata da haske kuma bata da duhu sosai, Irin dai mutanen da ake kira chocolate color ne ko kuma wankan tarwada, dan karamin fuskar ta zagaye yake da dan karamin baki, yayinda Dogon hancinta ya dace da mazaunin sa, Idan tai murmushi kuwa dimlpe dinta yake lotsawa ya Kara hasken annurin fuskar, idanun ta kuwa haka suke tamkar farin wata wajen haske yoh masu iya magana sukace Ga Wata 馃寵馃憟 ga Zara 馃榾,hooo me kr2 Idan nace zan tsaya zayyano kyawun fuskar ta toh Lalle za'a dade ban gama ba, domin dai BATUUL mai kyau ce.

riqe take da iPhone dinta 脿 hannun hagu yayinda dayan hannun take riqe da karamin yaro da bai wuce shekara uku ba, tafiya takeyi 脿 hankali kuma cike da natsuwa sannan ga hadari da ya rufe ko ina, ruwa ko yaushe kan iya saukowa sai iska mai dadi dake kadawa 脿 hankali 脿 filin Idin Ramat square dake Maiduguri ,ta juyo sannan ta kalli yaron dake riqe da Hannunta sannan tace Babich kaga kasa su Mama Sun tafi Sun barmu ko ai shikenan in muka rasa sallah yaron yayi dariyarshi mai kyau yace ai zamuyi sallah har in roqi Allah ya bani irin CLS din Yaa Ahmad tace to kaga muyi sauri sai mu yi sallahn yaron ya dubeta sannan yace yaa Baatul ai kece bakya yin sauri inata Jan hannunki tace toh shikenan zanyi saurin muje mu samesu haka suka karasa har wajen Sallahn daga gefen mata suka samu har an shimfida musu abun sallah sannan suka zauna wata farar mata mai kyau da baza ta wuce shekaru 35 zuwa 38 ba tana riqe da jariri ta juyo ta dubesu tace a ina kuka sami hulan ? Baatul tace Aunty a mota ya bari matar da aka kira da Aunty tace ai ke kika biye mishi da kin barshi yayi sallah babu hula tunda da gangan ya cire, Batuul tayi murmushi tace Aunty ai da yanxu bamajin Khuduban nan da akeyi Aunty tace hakane Baatul ta juya ta kalli wata yarinya da bata wuce sa'arta ba tace Fa'iza kin dauko min jakata da nace ki fito min da ita dan inaso inyi sadaka in an idar da sallah yarinyar da aka kira da Fa'iza tace ehh yaa Baatul na dauko gashi nan ma ta dauko wata jakar Herm猫s mai ruwan toka da kana gani kasan an kashe naira ta mikowa Baatul ta amsa tayi murmushi sannan tace na gode Fa'iza haka suka zauna shiru suna sauraron khuduba har aka gama aka tada sallah Baatul ta dubi Fa'iza tace tunda ba kya sallah ki karbi Aabid 脿 hannun Aunty tace toh Yaa Baatul ta sa hannu ta karbi jaririn daketa wasa sannan ta dan koma gefe su kuma sukayi kabbara suka nutsu dan su nuna godiyarsu ga Allah (swt) da yasa suka gama Azumi lafiya har yasa suka ga sallah.

Ahaka suke Zauna bayan idar da sallah har Imam ya gama hudubar bayan sallah da wa'azi da tunatarwa , nan Dubban jama'ar da suka hallaci sallar suka fara kokarin kama gabansu.

馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

馃挅馃挐BATUUL馃挅馃挐

2

Dedicated to *KHALEESAT HAYDAR*

Agogon batman din dake manne jikin bango ne yayi ticking 6:30 da rabi dai dai na safe tare da yin sauti,

Tashi yayi tare mikewa daga kan lallausan katafaren gadon da yake kwance kai, yana mai karanto adduar tashi daga bacci (Alhamdulillahillazi ahyana ba a dama amatana wa illaihin nushur sannan ya kara dayiwa Annabi (SAW) salati, ya tashi ya juya ya kalli agogon da ya farkar dashi daga bacci yaga har 6:40 tayi, yayi sauri ya karasa toilet din dake manne 脿 dakinshi cikin hanzari yayi sauri yayi brush yayi wanka sannan ya fito daga toilet din daure da towel da kuma wani towel din a hannunshi yana goge fuskarshi da ita har ya karaso gaban wani babban mirror da mutum kan kalli kanshi gaba daya tun daga kai har kafa ya karasa goge kanshi kenan zai shafa mai yaji karar wayarshi na ringing da har yayi kaman bazai dauki wayarba sai kuma ya juya ya karasa inda wayar take, yana ganin mai kiran da sauri yayi maza ya dauka tare da zama sannan ya risina kamar mai Kiran na gabanshi, zama yayi kamin ya kara wayar a kunnanshi tare da cewa Hello Ammah *nda wattu*(ina kwana) daga daya bangaren aka amsa da *k锚lewa s锚lai* (Lafia Alhamdulillah) sannan aka sake ce mishi Abu ka shirya ne yace 脿 ah Amma saura kadan yanzu zan shirya in fito tace yawwa Dan Shehu yace bana karfe takwas za ayi sallah kuma kasan kaine zaka tafi da Abui ya ce *yo dai k锚rma lukin*( toh gani nan fitowa yanzu ) ya katse wayar ya ajiye

Closet din kayanshi ya bude sannan ya dauko wani sky blue din shadda mai kyau da tsada ya saka ya dauko cuff links dinshi na Mandarina duck sannan ya sanya su a hannayen rigartasa tare da dauko hular Rawaram blue mai dan ratsin black brown ya seta ta a kanshi kamar da kan akayi hular ta zauna d'as agogon shi na Fendi ya makala è„¿ hannunshi na dama sannan ya dauki Turaren Tom Ford da Rasasi dake gaban mirror dinshi yafesasu è„¿ jikinshi kamin ya koma gaban coffee table ya dauki key din motar dake ajiye akai da kuma wayarsa sannan ya sako takalminshi baqi na Haven ya fito daga dakin tare da kallon agogon hannun shi yaga bakwai daidai

Saukowa yake daga kan benen cikin kwanciyar hankali da natsuwa har ya karasa sauka ya isa wani kaftareren parlour da girmanshi ya dauki set din kujeru uku, karasowa yayi cikin parlour ya isa wajen wani dattijon mutum mai dan haske yana sanye da kaya na alfarma , sanye yake da farin glass 脿 idonshi, hannunshi kuma riqe yake da remote ya saka tashar Iqra yana kallon yadda musulmai ke nuna farin ciki ga ubangijinsu, gabanshi kuma glass table ne dauke da flask din tea an zuba Kadan a *finjal* ( karamin transparent kofi na shayi) Ya karasa tare da zama dab da kafan dattijon tare da Ce mishi Abui *nda wattu* (ina kwana) *Bara ng锚m锚riaa* (Barka da Sallah) Bara *Ng锚m锚riro* ABUTTURAB (barka dai ABUTTURAB) ka tashi lafiya yace Alhamdulillah Abui sannan yace mishi Jiya na tura Abubakar yace maka an sanar da ganin watan sallah daga *SHEHURI* (palace din sarkin Borno) yace min ka rufe kofa kuma wayoyinka ma duk a kashe yace ehh Abui na gajine jiyan shiyasa na shiga da wuri kauyukan da mukaje kai zakka ne hanyoyinsu babu kyau amma Massa ya kirani ya fadamin that babanshi yace anga wata gobe sallah kuma nasan shehu da kanshi zai qira ya sanar da kai shiyasa ban sauko na fada ba yace ehh tun jiya shehu ya kirani yace okay bari in shiga inga Ammah dan tun safe ta kirani wai ka shirya kana ta jirana yayi murmushinsu na manya yace ai Ammah tun karfe biyar da ta tashi bata koma ba sai da tashi kowa har masu aiki tun karfe biyar suka tashi suna ta hidima yace ai Ammah akwai kokari sannan ya tashi ya sauka daga kan matakala da basu fi biyar ba yabi wata hanya har ya isa kitchen tare da sallama wata mata mai dan madaidaicin jiki kyakyawa fara ta juyo ta dubeshi tare da amsa sallamanshi tace Abu kowa ya tashi 脿 gidannan kai baka tashi ba kuma bana karfe takwas za ayi sallah Abui tun dazu ya shirya yana jiranka, yayi murmushi tareda karasawa wajenta y'a rungume matar tareda da sumbatar goshinta yace mata Ammah barka da Sallah tayi murmushi kamar ba ita ke fada ba yanxu *Baaran锚m* Abu (Barka Abu) suna tsaye a haka wani saurayin yaro fari kyakyawa dogo amma bai kai Abu girma ba ya shigo tare da gyaran murya yace Ammah muna nan fa ta juyo tace Babana har ka shirya ne ya karaso tare da daukan Apple dake cikin basket 脿 kan kitchen Island din ya dan bata rai yace Ammah an manta da damu ana kula da Babban da ya dace ace yana gidanshi yanxu, Abu y'a juyo ya harareshi yace ai sai ka kaini gidan nawa Ammah tace ai gaskiya Sadiq ya fada Abu ya girgiza kai ya fita Ammah ta dubi Sadiq tace muje kuyi breakfast mu tafi masallaci

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.