Complete Hausa Novels

Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel

Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt

Chapter 9 of 86

Kwana biyu Abin ya tsaya mata arai sosai har wani zazzabi ke shirin kamata gaba daya tayi sukuku da ita Yasmin tayi tanbaya har ta gaji Amma ba Amsa,

Shima gefen shi hakan take domin ya mugun damuwa soyayyar Maryam ta yi mai mugun kamu bayajin zai iya hakura da soyayyar ta gashi baida ko numbar wayar ta bare yaji muryar ta,

Damuwa tayi mai yawa har takai ga ogan shi ya tanbaye shi lafiya?

Jin juna suke kamar yan Uwa ko Abokai don haka bai boye mai komai ba " hmm saboda mace kake hana kanka natsuwa? Toh ita y'ar gidan uban waye da Baban ta zai ce ya bawa wani ita?

"If you really love her get her pregnant sai muga y'anda zata Auri wani kaga dole su baka ai, kallon ogan yayi " sau daya fa nasamu damar magana da ita,

"Ina gidan su yake ? Suna unguwar Dosa ne " ok karka damu I will help you get her,

Bayan sati daya ta dawo daga makaranta ita kadai ce saboda Yasmin bata jeba tana fama da ciwon ciki, ta fito daga cikin school din nasu dake tudun wada,

Ganin motar ranar a gaban ta yasa tayi saurin daga idanun ta ta zuba mai yana zaune a cikin motar kamar zai cinyeta da idanu,

Kafin ya fito ya dawo dayan gefen da take tsaye ya bude mata tareda bata umarni, "ki shiga Muyi magana Maryam,

Ba musu ta shiga tareda rufe kofar da yake tinted ne bamai hangosu,
Ya shiga shima tareda riko hannun ta da yakusa sata suma saboda wani irin shock da taji,

Wannan ne karon farko da wani namiji ya taba rike mata hannu haka
" Maryam ya kira sunan ta dago kanta kawai tayi idanun ta na cikowa,

"Kinga halin da soyayyar ki ta jefani' ko Abinci bana iya ci kawai tafiya nakeyi Amma bana cikin hayya cina Maryam bazan iya hakura dake ba banason wani ya Aure ki I want you,

Ki taimaki marayan Allah k'arki sani cikin gararin Rayuwa, kuka ta fashe dashi da yasa baisan lokacin da ya rungumota zuwa jikin shi ba gaba dayan ta tadawo kan kafar shi,

Wani irin rudewa yayi jikin shi ya fara rawa, " Maryam ki Aure ni don. Allah, ya dago fuskar ta ya zuba mata ido "kina sona?

Kai ta daga mai kawai " to ki fadawa baba ni kikeso ya barni na Aure ki zakiyi farin ciki, "bazan iya ba '
Ta furta mai. A hankali, Ajiyar zuciya ya sauke

" zan koma wurin baba yau bazan iya hakura dake ba ina sonki sosai ko bakyason Aure na?
",inaso, ta fada kissing goshin ta yayi kafin ya maida ita mazaunin ta kamar wata baby ya gyara belt din sit dinshi,

" muje inkai ki gida, tace "aa kar baba ya ganni a motar ka kabarni zan hau napep, " aa bazan bar matana na hawa motar haya ba, ya hau kan titin batareda ya saurare ta ba,.

Tun daga nesa ta hango mahaifin ta a kofar gidan jingine da jikin y'ar karamar civic dinshi yana magana da Ismail, wani irin faduwa gaban ta yayi ta fara juya kai "don Allah mu koma kaga baba da ya Ismail a tsaye,

Jin sunan w'anda takira yasa ya bude motar cikin fushi ya nufesu Dukawa. Yayi ya gaida Baban kafin yayiwa Ismail wani irin mugun kallo,
" Ahmed Kaine yau a gidan mu ya aiki, baba ya fada tareda bashi hannu,

Yace "Alhmdulillah naga Maryam ne a hanya na rage mata hanya nakawo ta gida yafada yana nuna mai Maryam din data fito jikin ta narawa ta gaida Baban nata dake. Binta da kallo,

Ismail kuwa dukar da kanshi kawai yayi batareda yace komai ba,
Gaishe su tayi ta shige jikin ta narawa,

A tsakar gidan ta tarad su suna hira Yasmin tayi filo da kafar Mama, ta gaida mama ta wuce da sauri cikin dakin su,

Yasmin ce ta mike tareda binta dakin " Aunty lafiya? "Me kika gani? " naga kin shigo a sittin ne ko kallo na bakiyi ba,

"Ba komai ya jikin ki? " naji sauki, ya lectures yau me Akayi?
"Ki duba jakata ina zuwa in watsa ruwa zafi ta fada tana fita dakin zuwa waje,

Tanajin Shigowar Baban nasu ta ki fitowa cikin bandakin domin tasan sauran saidai maganar da taji yanayi ce yasa ta fashe wa da kuka, saurin rufe bakin ta tayi da hannu kar su jita,

" nace Ismail ya fara shiri watan da zamu shiga zandaura musu Aure da Maryam, yake fadawa mama,

"Alhaji bayan kace sai sun gama school of nurse din kuma me yasa ka canja Shawara?
" gani nayi Maryam na shirin kaini ga kunya shiyasa nace zanyi mata Auren ita Yasmin idan ta kammala sai tafito da miji tayi Auren,

"Allah yasa Alkhairi tafada batareda lamarin yayi mata dad'i ba saidai halin girma irin na iyayan my mata nagari da kara yasa bata nuna maiba,

Ita kanta Yasmin jikin ta yayi sanyi duk da tasan wannan ne burin Baban su a Rayuwa hada Auren Maryam da Ismail,

Alhaji lawal mai turare shine sunan mahaifin nasu shi dan Asalin garin Zango ne su biyu iyayen su suka haifa shida kanin shi Mahmud sun taso cikin kaunar juna har lokacin da Alhaji lawal ya kammala karatun shi ya fara aiki da ma aikatar nipost dake nan Kaduna ya dawo cikin gari tareda Auren Matar shi guda daya da kuma d'an kanin nashi tilo,

Tun Ismail na karami Allah ya dorawa Alhaji lawal kaunar yaron tun ma bai haifi nashi ba, kuma d'an uwan shi ya mallaka maishi halas malak

Mama saudatu ita ce Matar shi daya mai halin kwarai ta rike shi Amana tun bata fara haihuwa ba har Allah ya bata haihuwar Maryam,

Bayan shekara biyu Allah ya kuma bata Fatima wato Yasmin kenan kasan cewar ta ci sunan kakarta ta wajen uba,

Rashin son maganar Maryam ya faro tun tana karama zaka d'auka kurma ce shiyasa ma bata fara karatu da wuri ba har saida Yasmin ta isa shiga makaranta aka hada su,

A gurguje sunyi karatun su tundaga primary har matakin secondary kafin su shiga makarantar koyon Aikin jinya wato school of nurse,

Wanda a nan ne suka hadu da Ahmed bayan maganar Auren ta da Ismail tayi karfi sosai,

A haka kwanaki ke tafiya har lokacin da baba yasa ya yi a lokacin Maryam duk ta tsiyaye a tsaye tsabar tunani da damuwa kullum mahaifiyar ta tanbayar ta takeyi duk da tana kara irin ta y'ar farko Amma saida ta cire kunya ta sata a daki,

"Ki fada min Abinda ke damun ki nice mahaifiyar ki Bakida wanda ya fini kuka tasa mai cin rai kafin ta bude baki " mama Ahmed nakeso banason ya Ismail ki sa baki baba ya barmu Muyi Aure dashi ina son shi sosai,

Shiru mama tayi tareda zuba mata ido tama kasa cewa komai tasan cewa maganar babbace tunda duk karar Maryam ta bude bakin ta fada lallai kuwa tana son shi sosai,

Tashi tayi fita dakin megidan ta sameshi ta zauna cikin ladabi,

Baban Ismail Alfarma nake nema don girman Allah, juyowa yayi sosai ya zuba mata ido "ina jinki saude wace irin Alfarma ce?

" akan zancen Auren nan ne don Allah ka hada Ismail da Yasmin tunda ita batada w'anda takeso ka bawa Yarinyar can zabin ta,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.