Complete Hausa Novels

Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel

Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt

Chapter 73 of 86

Ahmad ya matso tareda karbar jakar suka shiga cikin shine agaba kamar d'an gida su baba na ganin su Abin ya mugun burgesu ganin yanda ya dauki kanshi d'an gida ba girman kai, kamshin shi yafara sallama a tsakar gidan kafin suji sallamar shi , gaba daya matan ido suka zuba mishi don da yawa basu sanshiba, Aunty maryam ta matso cikin sauri suka fara gaisawa su mama sai kai da kawowa sukeyi, mama hindatu ce da tafito daki rikeda d'an bokiti a hannun ta tafara Maraba da surukaina ku iso, gaisawa yafarayi da matan kafin ayi musu jagora zuwa cikin falon mama hindatu dakin ba laifi don akwai kujeru harda kayan kallon ta gefe kuma katon deep freezer dinta ne datake sana ointa dakin duk da ana biki tsab yake domin duk yawancin mata na sauran dakunan gidan da kuma tsakar gidan,

Tana kuryar dakin taji muryar shi tayi saurin zabura ta mike zaune tareda dafe kirjin ta ya shigo? Ta fada a bayyane NANA ta kalla dake baccinta ta zuro kafa ta leka ta window tana kallon yanda yake gaisawa da matan har zuwa lokacin da aka shigo dasu ciki, komawa tayi ta zauna tana fargabar Abinda zai biyo baya, shikuwa yagama baza idanun shi a cikin gidan kaf bai gantaba, bayan sungaisa dasu mama hindatu itama mama ta shigo ya musu Allah sanya Alkhairi suka fara zubamai godiya domin baban zango ya fada musu komai, mama hindatu ta kalleshi tace "ka ciri tuta ba yanda yaya baiyi da shi ya koma cikin gari yaki Amma sanadinka ya Amince muna matukar godiya, "bakomai mama Addu ar ku nake nema kawai, mama ta fita ya ce " banga yasmin din ba? " ai tana ciki, Aka kira mama hindatu a waje ta mike tareda cewa Mama ki fito ga mai gidanki duk da nasan kina jin komai, Aunty maryam ta shigo musu da kayan motsa baki irin na biki dasu drinks Zainab ma ta shigo taga Wanda ya taimaketa yarabata da kishiya,

Yasmin kanta ya daure sosai jin godiyar dasu mama keyi kuma gazancen komawa gari da taji mama hindatu nayi to me hakan ke nufi? Ko shine godiyar da baba ya mata a waya,
Aunty maryam ta shigo ciki tace " malama kifito MA na kiranki kafin ya shigo, hijabinta ta mayar ta mike tareda fitowa cikin sanyin jiki, tunda ta fito ya zuba mata ido kamar ya hadiyeta ba ruwanshi da idanun su ismail da kuma yaronshi Ahmad, tashi yayi kawai ya nufeta ganin takasa karasowa yana isa ba westing time ya rungumota su Zainab dake gefen mijinta ta zaro ido tareda rufe wa da hannun ta, Ahmad dariya kawai yayi don yasan zaiyi Wanda yafi wannan, Aunty maryam ta fice Abinta saboda ita suruka ce ai, hannun shi ya dora saman cikin ta " how are you my baby momy ta hanani jin duminka tundazu ko sorry ya dan duka yayi kissing cikin ta zuba mai ido kawai don tasan baiyi ko kashi goma ba a cikin kashi Dari na rashin kunyar shi,

Dariya ismail yakewa Zainab dake rufe ido saboda kunyar Abinda MA keyi da mugun kishin Yasmin takeji don tasan komai akan su har maryam ma kishin ta takeji saidai yau ta yarda shirme kawai take zubawa domin taga mazajen su tasan ko maryam ta wuce da Ajin ismail bare kuma yasmin matar oga kwata kwata tana hango tsantsar soyayyar da MA yake wa yasmin tundaga yanda yake rawar jiki akanta duk ya wani makale mata kamar chewing gum, kokarin raba jikin su takeyi domin matsawa su gaisa da su Ahmad, ya kara kwakume ta a jikin shi suka zauna a kujera daya yana zura hannu ta cikin hijabin ta batareda sun ankareba ita tasan bata isa ta hanashi abinda yakeyi ba tasan ta na hanashi zaiyi Wanda yafi hakan, gaba daya ya gama takurata, gaisawa sukeyi cikeda kunya tace yaya ismail ya gida naga madam ai tundazu, Sannu yaya Ahmad, ranki ya dade ai kibari mu kwashi gaisuwa irin wannan yanga da akewa ogan mu ai dole muyi biyayya, "yazanyi ismail ai tana garani don taga bazan iya mata kishiya ba, fisge Hannun shi dake yawo tayi kan cikin ta ta watsa mai harara harda murguda baki ka auro uku who care? " I care couse nasan sai gidana yazaba filin wrestling don bazaki barsuba and the truth bazan iya hakura dake ko NA one day ba muna gida daya inje wajen wata ke Kadai nake raayin ajiyewa a gidana you are my one and only ba wata saike baby, wani irin dadi taji tareda rungume shi tana bashi kiss a baki gaba daya ta manta da mutane a dakin, dariya ismail ya kwashe da ita "sister irin wannan kishin haka? Ahmad kuwa cewa yayi " madam mudake kokarin karo muku Abokan zama kar aikin ya muku yawa, " kubarmu ya kashemu aikin zamu iya, Zainab tafada tana mikewa don itama badai kishiba,

Haka suka yita hira tsakanin su kafin maryam ta shigo da Leda " ga ankon ki ki shirya muje wurin Amaren suna gidan baba liman, " kai Aunty nida nake shirin tafiya da madam masaukina, gaskiya da sake bawani inda zataje, kallon shi tayi cikin bata fuska karka mun haka please banga Amarya ba fa kuma yanzu aka fara biki kasan Al adarmu taron yau da gobe ne kabarni inshiga cikin Y'an uwa don Allah, "Ayi mana hakuri in low yau da gobe ne kawai, " to Aunty bari inje zandawo zuwa 4 kuje kuma karta wuce can banason yawo naga mazan garin nan akwai kallo, dariya yasa ya ciro bandir na kudi sababbi kusan guda uku ya mika mata gashi idan zaki raba ga sakon Hajiya nan na jiya, godiya tayi tace " please kabayar akawomin jakata da sauran kayana,

Wani kallo ya jefa mata "muje ki karbo da kanki, tare suka fito sun burge duk matan dake cikin mama kanta duk kunyar da takeji yau ta ware ido ta kalli yaran nata biyu rak masu tarin Albarka tareda Kara godewa Allah, tasan ba duk mace keda sa ar da tayi a duniya ba, a waje ma kallon su akeyi har ya bude motar ya fito mata da jakar ta ta kaya kafin ta bude sit din baya ta ciro hand bag dinta tareda daukar wayarta, yana kallon ta jama a NA kallon su saida ta rufe zata juya yace wait, matsowa yayi gab da ita " please be careful karkiyi yawo kafin indawo, and naso muje tare kwadayi nakeji baby, sorry zamu koma gidan mu ai jibi hmm yace kawai yace bye, ya shige ta wuce ciki aka jashi zuwa masaukin shi,

Kayan da Hajiya ta aiko mata tafara budewa taga turarukan wuta a kwalabe masu kyau da kuma manyan gorunan humra masu tsada da kamshi kowane yakai goma ta dauki waya tanajin dadi takira Hajiya, tana dauka tace " ina cewa akiramin ke sai gaki kun isa Lafiya? " momy na Lafiya lau wallahi rigimar babankin nan ya hana inkira tunjiya inkiraki inyi godiya sai yanzu ya bani kayan ma, dariya tayi ai baba na sai shi to kuma kayan Amarya ne kibata banaki bane, " kai momy Nifa? Ta fada tana shagwaba, " banson haka yasmin ki barmata inkin dawo zansa aka wo miki naki kibata duka kinji matar baba, tafada cikin lallashi tace " tom na hakura momyna nikadai, ta kashe wayar ta na jin dadi Aunty maryam da mama da suka shigo suka kalleta farin cikin dake bayyane a fuskar wannan family bata boyuwa,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.