Complete Hausa Novels

Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel

Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt

Chapter 20 of 86

Wani irin hankadeta yayi tareda mayarda towel dinshi data kwance batareda yasani ba, wani irin kallon tsana ya ke watsa mata yanajin mugun kyamar hada bakinta da nashi fa tayi wani irin tashin zuciya yaji tuni ya bude mouth wash ya kuskure bakinshi saida ya saita kanshi kafin ya sakarwa kanshi shower ya fito yana mai zuba mata mugayen idanun shi masu girgiza maza,

"Why did you kissed me?? Shine abinda ya fara tanbayarta cike da tsawa, ta taso tana kwarkwasa fuskar ta dauke da farin cikin yau ta d'an d'ana miyan da ya dade yana mata rowar shi,

Kokarin shigewa take jikin shi ya watsa ta gefe "kin san banaso why did you do it? Now out before you regret nowing me,

Idanun ta ta watso waje tana Mai tsananin mamakin canjawar shi gaba daya MA ya canja,

"This is not you, "me yasa kakeson ka koreni daga cikin rayuwar ka, bayan kasan is impossible in rayu batareda kaiba, please don't purnished me like this muhammed,

Wata uwar tsawa ya buga mata "zuby out before I loosed my temper, ba arziki ta hada kayanta ta bar gidan kafin ya mata na jaki don tasan halin shi don yanzu ya mata dukan sojoji bakomai bane,

Tana fita ya datse kofar shi ya kuma fadawa gadon yana mai tuna YASMIN "please baby come to me shine kawai ya fito daga bakin shi

He really want her she is the only woman he want right now she is perfect wonderful and amazing,
He can do anything to get her in his life,

YASMIN kuwa Tana fita ta saita kanta
Kafin tashiga gidan tayi Sa a ba maryam a falon saida ta shige dakin ta wurgarda hijabin ta kafin ta fara hada Kayanta,

Tareda kudurin barin barikin baki daya a yanzu Domin ta tsani duk wani Soja ma da mugun halayen shi har mijin yayar tata yau bazata so su hadu ba bare wani d'an iska daban

Cikin sauri ta fada ya watsa ruwa tareda yin brush sosai don ta wanke miyanshi da ya gauraya da nata Tana binshi da Allah ya isa yafi Sau d'ari,

Saida ta shirya cikin sauri sannan ta fito tareda leka y'ar uwarta ta ga Tana bacci ita da yaron ta ta a jiye mata letter tayi waje da saurin ta don bama ta fatan Kara koda second ne a cikin barikin

***********************

Mama tayi mamakin ganin YASMIN a wannan lokacin sai dai Tana tanbayar ta dalili tace tanada project ne a school Gobe shiyasa ta dawo,

Bata kuma tanbayar taba ta ce tazo ta deba abinci taci, "banajin yunwa mama zan kwanta ne kafin akira sallar magrib,

"Aa kinsan kwanciya a irin wannan lokacin batada amfani ki zauna muyi magana,

Zama tayi jiki a sanyaye ta zubawa mama ido, "dama babanku ya so insa kidawo kan maganarki da ismail yanaso a gama komai kafin nan da wata daya kya karasa karatun a dakin ki,

Wani irin bugawa kirjin ta yayi batasan daliliba kawai taji Sam bata farin ciki da lamarin nan yanzu,

"Kinyi shiru ko akwai matsala ne? Saurin girgiza kanta tayi tareda cewa "aa kawai dai naso sai na kammala karatuna ne kafin ayi maganar Auren

"Meye matsalar Yasmin kinfa san halin d'an uwanki ko a gidan wani ne ma shi me iya taimaka miki ne kiyi karatu bare kuma shi Zaki Aura,

"Ina tayaki farin ciki YASMIN Domin ni na rike yaron nan nasan nagartar shi zakiji Dadin rayuwa dashi ke kinsani,

Mama ta dade tana mata nasiha tareda nuna mata halaye masu matukar
Burgewa gameda ismail,

************

Misalin karfe goma tana kwance a cikin dakin ta a katuwar katifar ta hutadda gadon ka waya takeyi da y'ar uwarta tana bata hakurin irin tafiyar da tayi ba sallama sai tanbayarta takeyi dalilin hakan amma amsar daya ce dalilin project,

Da sallamar shi ya shigo dakin ya nemi gefe daya kan stool din mirrow ya zauna tareda zuba mata ido tane wayar a natse, kallon ta yakeyi kamar ya hadiyeta tana sanye da hijabi amma fuskar ta tayi wani irin fresh takara yimai kyau sosai,

Saida ta gama wayar kafin ta mike zaune ta dukar da kanta Kasa tana mai wasa da wayar tata, "sannu da zuwa ya ismail, saida ya sauke ajiyar zuciya kafin ya iya amsa mata fuskar shi cike da annuri,

"Gimbiya sannu kema meyasa baki fadamin Zaki dawo yauba ai Dana zo na daukeki da Kaina,

Murmushi tayi kafin tace "shiyasa ai naki fadama banaso ka wahala,.
Amma naji Dadin dawowarki gida hankalina ya kwanta don gaba daya a tsorace nake kar sojoji sumin kwace nasan su da son mata bare tawa princess dole wani ya k'yasa,

Gabanta ne ya fadi tunowa da abinda ya faru har saida ta daga hannun ta ta shafo lips dinta tana mai tuna yanda ya rika tsotsar su kamar sweet take taji gashin jikinta na mikewa,

Maganar ismail ta dawo da ita hayyacinta, "samari nawa kikayi a barrack? Bako daya ta bashi Amsa "ai bana zuwa ko Ina ya ismail kuma ga ka ya zan saurari wani namijin,

Yaji Dadin maganar tata sosai ya mike "ki huta zamuyi magana sosai Gobe nasan mama ta fara fada miki ko,?

Tasowa tayi tana mai rakashi har saida ta kai gab da gefen part din shi ta tsaya Shima ya juyo tareda zuba mata eyes "baby na matsu ba a daura mana Aure ba Ina bukatar mace a tare dani kuma ban taba sawa raina hakan ba sai ta dalilin ki Ina matukar kaunar ki baby Wallahi in narasaki akwai matsala Babba,

Sun dade yana amayar mata da sirrin zuciyar shi tun tanajin kunya har ta saki jikin ta ta bashi kulawa itama tareda kwantar mai da hankali kafin su rabu,

***********
After a week

Tun karfe takwas yau da MA ya fito yake zubawa kofar gidan ido kasan cewar weekend ne, yau kusan sati ko giftawar ta bai gani ba tun ranar da tabar gidan shi bai kuma ganin taba

Duk ya fita hayyacin shi ya Kasa natsuwa har a wurin aiki baida walwala gashi bazai iya fadawa Kowa cewa ita kawai yakeson gani ba,

Y'an matan shi kuwa ba wadda yake saurara don bai cikin natsuwa bare har yanemi wata mace,

Yaran Shima basa ganewa ogan nasu yanzu haka yagama zubawa gidan ido kafin ya koma cikin falon sai faman sintiri yakeyi,

Ya dauki waya Sau ba adadi yanaso ya tanbayi Ahmed Amma yakasa to me zaice mishi?

Yaron shine fa kar yayi wani tunani akan hakan
Yana hakan Emanuel ya shigo tareda Sara mai cikin girma mawa ko iya Amsa mai baiyiba har ya wuce yayi saurin tsayar dashi,

Ya dawo cikin hanzari tareda kamewa tsaye kem "yes sir, ware is your friend?

"Oh Oga my friend don go back na yerstaday I ask her aunty she tell me say....

"Go ya fada cikin saurin katse labarin jikin shi NA rawa ya mike daga zaunen ya haye sama cikin sauri ya fada bathroom Domin shekawa kanshi ruwa,

Kana nan kaya yasa sunyi matukar karbar shi ya feshe jikinshi da turare tareda daukar makullin motar shi yayi waje cikin hanzari,

Yaranshi na ganin fitowar shi suka nufo cikin hanzari ya daga musu hannu "no need am going a lone ya fada tare da fadawa cikin marcedez benz dinshi kalar army tana sheki ya figeta tareda fita gate din a guje,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.