Complete Hausa Novels

Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel

Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt

Chapter 63 of 86

Juyowa tayi tareda rungume shi, "yanzu ma bazamu kuma yin waya ba sai kadawo? "Noo nasa an kara service a wurin kullum zamuyi waya yanzu ai bazan iya zama Banji muryarki ba sai jini na ya hau gashi inaso inrikajin lafiyar baby na,
Ok tashi muyi wanka yunwa nakeji, sauka yayi bakomai a jikinshi ya dagata cak sai bathroom bajewa yayi ya bubbude a tub din yace ita zatamai wanka, haka tafara wankeshi yana lumshe ido tareda yawo da hannun shi a ko ina najikinta, dakyar tasamu tayi escape suka gama wankan haka suka fito yana layi domin jinshi yake kamar ma baiyi komai ba Amma yasan inyace zai kara zai cutarda babyn shi,

A dakin ta kawo musu komai suka karya sannan ta shirya cikin wata shigar na purple code less mara nauyi Riga da sket ya zauna cif a jikinta ta murza dauri Shima ya fito cikin farin yadi mai shara shara kana hango farar singlet din shi yayi kyau yana baza kamshi, yace ta dakko gyalenta zasuje malali sugaida hajiya, cikin farin ciki ta ce tom tareda ciro farin mayafi da gyale harma da jaka, ta kara fesa jikinta da turare yana tsaye ya zuba mata idanu, wani farin ciki yakeji domin yasan yayi sa ar mata ga kyau ga kuma nasaba don ta cika mace ciki da waje,

Rikota yayi suka fito ta sallami baba jummai tace sai sundawo cikin sabuwar motar lefen ta daya fara suka shiga yace yau ke zaki tuka mu ina gefe,, tace tom muje, ta murza key ya zuba mata ido kamar ya cinye ta, ta fita a gate din suka dauki titi " kaifa zaka rika nuna min hanya bansan ta ina zamu bi ba, gyara zama yayi ya zuba mata ido tareda janye gyalen daga kafadar ta ya mayarda hannun shi wurin da yakeso, "ina tuki nefa karka sa in watsar da mu a titi Kasan ba wani iyawa nayi kamar kaiba, "uhm sai mu tafi tare mu duka Kici gaba da tukin ki kawai kibarni inyi wasa da kayana, haka yaketa motsata yana lumshe ido har suka isa Lafiya tareda taimakon shi, katon gate din sojoin suka bude mata ta kunna kai tuni suka fara saramai ya wani hade gira bayan ya gama lalibeta a cikin mota matsowa yayi kusa da ita,

"Baby hajiya zata gane kin gama more mata yaro a mota kinga yanda nakoma, yafada yana mai manna mata jikinshi a gefen ta, ido ta zaro "baka gajiya ne wai kai,? "Indai da gidan dadi ne bana yi muje ciki ma kibani gaskiya bazan iya hakuri nida Abuna ba, "you are jocking? "Am not, tasan ba karamin Aikin shi bane zai aikata, tundaga kofar main falon sukafara jiyo hayaniyar Y'an matan na hajiya, ya hade fuska yakara rike mata hannu gam duk da tana kokarin yasaketa, "stay still ko indaukeki gaban hajiya dole ta natsu, suna jin sallamar shi suka shiga taitayin su, gaba daya suka zubawa matar tashi ido tuni kowacce ta raina kanta, sunga kyau haduwa da kuma wayewa dole ya rika musu kallon Y'an kauye kuma munana akoda yaushe tunda yanada indiya,

Da ruwan masifa yafara "wato ku kullum kamar akuyoyi Sam bakwa girma ko, yafada yana watsa musu mugun kallo, itadai neman wuri tayi ta zauna bayan ta samu ya saki hannun ta, zamewa sukayi kowace ta kama gabanta shi kuwa zama yayi kamar zai shige jikinta "muje side dina mufito kafin ku gaisa da hajiya baby, nidai bazan iya wannan Abun kunyar ba ni nasan kunya idan kasaba yi a gidan mu nan bazan yarda ba. Dariya yayi, baby saidai kar akuma kin manta ranarda nazo na kwakuleki a gidan nan kenan,..

Kafin tayi magana suka jiyo muryar hajiya "oh ni baba na ka kawomin yata kuma kabarta a falo ka tsareta da shirmenka ko, shagwabe wa yayi kamar karamin yaro "hajiya nace muje dakina na gaji inason tausa taki, matsowa tayi tareda riko hannun ta tana cewa "mara kunyar banza da wofi taki taje taso kinji mu shiga ciki y'ar Albarka kiyi hakuri kinji da halin baba na, "kai hajiya yau ni zaki y'ar ki kama wannan ko da ban kawota ba ai, "ai Kasan batada kafa ko batasan hanya ba, juyowa tayi ta mai gwalo yace "lalala ni kikewa gwalo zamu hadu a gida,

"Sai inrike ta a nan dama gobe zaka koma tashi yayi yabi bayanta, " kice zamu kwana tare kenan ba inda zanje kuwa, saida suka shiga dakin ta ta zame kasa tafara gaisheta tayi saurin dagata tashi y'ar Albarka Allah ya miki Albarka Fatima Allah ya Albarkaci zuri arku, ta Amsa a hankali, kanta a duke da kanta ta kawo mata kayan motsa baki Shima ya shigo, "wai yau nine bare aka ware ni, ka fita magana zanyi da suruka ta katafi dakin ka a gyare yake, "bakin shi ya turo. "Kai hajiya to tazo muje mana tare, nace ka fita ta tashi ta raka shi tareda maida kofar ta rufe, yayi dariya daman yasan kaunarda ke tsakanin hajiya da Yasmin tunfarko tun batasan cewa zata zamo matar shiba,

Zama tayi ta fuskance ya da kyau, "dama naso sai yatafi insa akaini gidan naku muyi magana akan babana Fatima nasan Kinsan komai dake faruwa, yanzu kinfini kusanci da babana kece matar shi duk yanda zakiyi a matsayin ki na matar shi ki taimaka mai Allah kuma ya raba shi da sharrin matan banza tunfarko sakacin shine, da yasaki jiki da yarinya mara tarbiya tayi sanadin fadawar shi harka da matan banza, Nagode wa Allah ma da baya wasa da salla baya shaye shaye da illar da zata yimai ba kadan bace don malamin dake bashi taimako yafada min anyita jifarshi da sihiri Kala Kala don dai yayi riko da ibada ne Abun baiyi wani tasriri a jikinshi ba amma wannan shedaniyar yarinyar ina kan kai kukana a wurin ubangiji Allah zai mana maganin ta cikin ruwan sanyi, kiyi hakuri haka Allah ya tsara Rayuwar shi tunfarko saidai mu tayashi da Addu a,

Shiru kawai tayi domin tanajin matukar bacin rai duk lokacinda ta tuna da Rayuwar shi ta baya wadda take kokarin taba farin cikin su a yanzu, hajiya ta fito mata da wani Dan madai daicin galan, ki rika shan wannan baida illa ga cikin ki Amma zakiji dadin Amfani dashi Zuma ce hadin Sudan nasa aka kawo muku keda yayyin ku ta ciro wata gumba mai kwakwa da su gyada da Aya tace kirika damawa da nono duk basuda illa kuma ko shekara zatayi bazatayi komai ba, godiya tayi. Sosai tareda jin matar ta kara shiga ranta ta diddila da murfi ta sha tareda karawa domin zumar harda dabino tanajin gardin ta sosai , tace kisha a hankali saboda zaki duk da batada damuwa Amma kodan gudun tashin zuciya,

Kunya taji kadan ta rufe Domin ita dadi tayi mata kodan kwadayi zata sha ta, ta tanbayeta ya Y'an Aikin ta sunyi? "Eh kawai baba na ce ta tsaya kodan su gyaran gidan da girkin sojojin dake gidan " to Aikin bazai mata yawaba ko za a karo wata tsohuwar ne inbakya ra ayin Y'an matan, "aa itama ta isa zandauketa gobe mu koma BARIKI kafin ya dawo, "ai ba damuwa duka gidan ki ne, inkina bukatar wani Abu ki fada sai atanadar miki, godiya tayi sosai tana kara godewa Allah da yabata uwar miji ta gari, wayarta tayi kara ta daga ganin sunan shi ne yasa taki dagawa,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.