Complete Hausa Novels

Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel

Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt

Chapter 5 of 86

Daga gefen kitchen din step da zai kaika upstairs din ne she wish zata iya hawa saman shima taga tsiyar dake ciki,

Maganar EMA ta dawo da ita ta bishi cikin kitchen din da ta kira Aljanar mace domin tana mugun son ganin kitchen a tsare ga wannan ya tsaru kamar a turai komai na bukatar macen data San kan kitchen Akwai a ciki,

Ajiyar zuciya ta sauke tareda ku durin idan zatayi Aure haka zata tsara nata insha Allah,

Da taimakon EMA ta hada komai ta shirya musu lafiyayyar miyar kuka da taji namomi zuku zuku aciki sai kamshin garlic da citta ke tashi domin sunada komai na Amfanin gargajiya da Alama ogan nason harkar gargajiya,

Shi kuwa EMA baki har kunne sai zuba yake mata kamar kanya har ta matsu tabar gidan tana kammalawa tace zata wuce ya rakota sai godiya yakeyi kamar ya ari baki,

"Tank you friend you save me today from my oga suna bude kofar shigowa wata sisi ta shigo kyakkyawa ce ba laifi ga wanka iya wanka domin less din jikin ta kadai zai nuna ma kudi sun koka Anan,

Komai na jikin ta kudi ne har Bangle's da jakar hanun ta Abin kallo ne sai walwali take tana zabga kamshi,

Wani irin kallo suke watsawa juna domin kowa na hango kyan kowa ita Yasmin Yarinyar burgeta tayi domin tana son mace mai daukar wanka kuma wannan tayi ba karya,

Ita kuwa zuby wani irin hade fuska tayi tana mata wani irin kallon ke wacece kafin ta bude baki cikin masifa tace,

" Emanuel who the hell is this? Tuni jikin shi ya fara rawa "sory madam na my friend I call her ne to help.......

" quiet ke kuma kiji nan nan gidan mijin da zan Aura ne ban y'arda ko wacce mace ta shigomin cikin shiba ni na tsara gidana kuma banason mace na rabar shi

Kinzo da kazaman kafar ki har cikin gidana to kar in kuma ganin ki daga yau stay away from my husband house,

Me neman kuka ai jikin Yasmin har rawa yakeyi ta gyara tsayuwar ta dakyau harda jijiga jikin da saida zuby tayi Addu'ar Allah yasa Muhammad bai taba ganin wannan Yarinyar ba,

"Ke wacece da zaki zo har cikin falo na kina min ihun wai gidan mijin ki lallai karuwan cin ki ya girma

" kin shigo min gidan Aure har kinada gut da zakice wai gidan mijin ki to ni Matar shi ce sai ki jira ya Auro ki kafin Kizo kiyimin gadara kuma yanzu kibar min gida kafin inhada ki da kuratan sojojin dake wajen gate din nan,

Wani irin tsuma jikin zuby ya farayi tuni hawaye suka wanke mata fuska wani irin kishi ne ya tokare mata kirji,

Kafin ta iya bude baki tayi magana kawai Yasmin ta turata waje ta datse kofar har tana huci kamar da gaske gidan tane,

EMA suman tsaye yayi ya dora hannu akai ya zama kamar statue duk da ba hausa yakeji ba yasan what ever Yasmin is saying is not right at All

"Chineke me friend na oga love wo na him girl friend she come from abroad you don kill me......

Tuni yafara paret tsaki ta yi tareda bude kofar ta leka taga ta tafi ta fito tayi wucewar ta gidan y'ar uwar ta ko ajikin ta,

A zaune yake a cikin office dinshi sanye da kakin shi yayi wani irin kyau a ciki gefen shi pistol ce da kuma system din shi har ma dasu tabs din shi akan table din ya dora kafafun shi dake sanye da boot dinshi masu sheki akai,

Kanshi a sama yana tunanin maganar shi da Momyn shi jiya, ta shigo cikin office din kamar yaki ta buga kofar jikin ta na rawa,

Har saida yayi saurin mikewa cikin hanzari ya janyo pistol dake gefen shi, ganin fuskar ta yasa yaji ranshi ya mugun baci,

.
Komawa yayi ya zauna kawai batareda yace mata ci kanki ba ta fara magana, " ka kyauta Muhammad na kiraka yakai sau uku jiya kaki daga min waya,

Bayan na fada maka zan dawo a jiya baka damu ba sannan d'an wulakanci na iso ko ka neme ni......any way nagano matsalar wato Aure kayi Muhammad bayan tafiya ta bayan kayi min Alkawarin Aure yanzu duk halaccin da nayi ma irin sakayyar da zaka biyani da ita kenan?

"All......." Quite don't you there couse me ke kika Ajiye ni ? Auren ki nayi ni nace ki jirani ? Na fada miki sai ke zan Aura ? How thare you banged into my office like this?

"Duk Rung's din da kikeyi a can na sani kar ki rena min hankali kuma Aure da kike magana....
Shiru yayi tareda kare matse fuska " eh nayi Aure kiyi Abinda zakiyi kuma yanzu kifitar min a office kafin inyi loosing control inci ubanki a nan '

Wani irin kuka ta fashe dashi kamar zata hadiye zuciya ta juya zata fita tana rufe baki yace "wait, tsaya wa tayi cak domin tayi tunanin hakuri zai bata,

" stay away from my wife and my house, da gudu tafice bako waiwaye duk inda ta wuce yaran shi kallon ta sukeyi domin kowa ya Santa dashi kuma sun San irin y'anda oga,ke mugun ji da ita to yau me ya faru,

Tana ficewa ya zauna kan kujera yana fitar da huci kamar kumurcin maciji yana tunani ko wace shegiya ce ta shigo mai gida har zuby ta ganta,?

Zaici uban Emanuel yau sai ya kulle shi don uban shi, baiso ya ma zuby haka ba Amma ai tasan bayason mace tayi mai gadara da rashin da'a shi yasa ya mata haka amma zai lallashe ta letter,

Intercoms ya danna Ahmed ya shigo saramai yayi ya koma gefe yana jiran umarni "ka hada min connection din TV inason inga wace ce a gidana?

" ok sir domin Akwai connection da yake ganin komai dake faruwa a gidan nashi Abinka da zamani,

Janyo tan din dake gaban shi yayi danna kawai yafara viewing Abinda ya faru na yau
Ahmed zare idanu yayi waje lokacin da video ya fara aiki,

Goshin shi ya dafe cike da kaduwa "wannan Yarinyar zata kashe ni waya aiketa gidan oga,?

MA kuwa tagumi yayi yana karewa karfin halin ta kallo mamakin ta ya mugun cika shi,

" og a....... Ahmed ya fada bakin shi na rawa zai bashi hakuri yayi saurin daga mai hannu tareda da nuna mai kofa yace ya fita kawai,

Jikin shi yayi sanyi ya fita shi kuwa ya kalli video din yakai sau uku yana repeat din shi dressing dinta yake karewa kallo har zuwa y'anda ta baje mai cikin kitchen ta hada mai miya a natse cikin kwarewa da kuma tsantsar tsabta,

Stop yasa dai dai lokacin da ta jijiga jikinta a gaban zuby zata zabga masifa d'an karamin bakinta ya tsurawa ido har zuwa lips din masu sheki da kuma idanun ta masu kama da fish lashes dinta sunyi zaro zaro ga gefen fuskar ta suma akwance tana sheki da Alamar taji gyara,

Samun kanshi yayi da jin nishadi karfe sha biyu ya bar office yace su tafi gida shima bai San dalilin shi na son komawar ba kasan cewar shi mutum mai son Aikin shi baya son wasa ko kadan,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.