Complete Hausa Novels

Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel

Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt

Chapter 2 of 86

" and you I will del with you letter, ya nuna Emanuel da hannu kafin ya wuce ciki, binshi sukayi da kallo domin sun saba da halin shi na wulakanci don haka kowacce ta kama gabanta kafin ya jona su da mugayen kuratan yaran shi,

Wanka yayi kawai ya haye gado domin ya sauke farali a office kuma bayajin yunwa he just need to rest before going out,

______________________
A zaune suke a barandar kofar apartment dinsu suna shan iska shida iyalin shi kana ganin y'anda yake tarai rayar ta kasan Akwai soyayya mai karfi a tare dasu,

Gefe daya d'an karamin yaron sune ke wasa akan d'an keken shi na yara,
Kara shigewa tayi jikin shi tsam,

"Ya Akayi ne farin cikin Ahmed? Murmushi tayi tareda fara yimai shagwaba,

" wallahi na matsu Yasmin batazo ba inaso inga babana Baban Auwal, "k'arki damu maman Auwal dina komai yazo karshe insha Allah,

Tsayuwar mashin din da ya dakko ta yasa tayi saurin mikewa tareda rugawa da gudu ta rungume ta,

Itama cike da zumudi ko akwatin ta bata d'auka ba ta rugo suka rungume juna cike da so irin na yan uwan da suka mugun shakuwa da kuma son junan su,

Daka gansu kaga jini daya saidai Yasmin tafi Maryam kyau nesa ba kusa ba duk da ita din kyakkyawa ce sosai Amma Yasmin tafita don ita farinta har wani daukar ido yakeyi,

Yarinyar kamar Aljana ga jikinta dai dai da ita, saida suka gama murnar su sannan ta kalle ta " ina babana?

"Wallahi baba ya tafi zaria Anki rashi wurin aiki shiyasa nazo ni kadai Amma yace shi zaizo daukata,

Wani iri tayi domin taso ganin mahaifin nata sosai tasa rai, tsaye yayi tareda nan nade hannu yana zabga murmushi domin ganin Abinda sukeyi,

Shi ya matso tareda Sallamar mai mashin din ya kallesu to mushiga daga ciki idan kun gama murnar ni ko gani na kanwata batayiba wannan karon nayi fushi,

" lah yayana wallahi tsabar murnar ganin rabin jiki ko boy dina Bangani ba sai yanzu ta ruga tareda rungume shi tsab "I miss you my boy,

Ta fada with so much excitement yayi dariya shima yaron kamar ya ganeta

A kan kujerun da suka tashi ra zauna tareda zubawa kofar katon gate din ido,

" Aunty ina bunsurun can gidan? Saurin rufe mata baki tayi "kiyi shiru kar Baban Auwal ya jiki wallahi kina zagar mai oga,

" ai Aunty ban taba ganin namiji mai d'an banzan son mata ba irin shi wallahi ana fadan sojoji na kwashe kwashe nashi karshe ne,

Shiyasa bana ko kaunar ganin shi A Rayuwata I hate him to the extend,

"Ikon Allah wai maikarfi na bara ina ruwanki da bawan Allah da baruwan shi da harkar mutane kuma bai ko San Allah ya tsiroki ba Amma kinsa mai ido,

" ai Bazai ma San daniba har abada d'an iskan mtsww ta mike tareda nufar cikin gidan domin maganar shi kawai tasa ranta ya baci,

Dariya kawai Maryam tayi domin tasan halin y'ar kanwar tata, ta shiga ciki itama,

Tare sukaci Abinci suna hira atsaka nin su kafin ta fito mata da tsarabar da takawo ma yaron ta na kayan wasa da kuma kayan sawa masu kyau,

Sai su kubewa da Daddawa da sauran kayan gargajiya irin na bahaushe daga mama domin tasan basa samu a bariki,

Saida tayi wanka ta shirya cikin kana nan kaya San nan ta dora after dress akai domin tana son tafita tasha iska a wajen gidan dama ta saba duk tazo nan ne wurin zaman ta tana karewa bariki kallo,

Yaron ta ta d'auka ta fito tana tafiya a hankali kamar bataso hannun ta rike da wayar ta hot 8 ta zauna tana karewa gidajen kallo kafin ta sauke akan katon cikin su wato na oga kwata kwata,

Emanuel ne ya fito daga gate din hangota da yayi yasa ya zo da sauri bakin shi har kunne,

"My friend don come, ya fada with so much excitement da jin dad'in ganin ta domin sun saba sosai kuma shine ummul khaba isin da yasa ta kara tsanar M.A domin shike bata labarin komai,

Washe mai fararen hakoran ta tayi cike da jin dadi tace " yes woo friend how are you?

"Fine mam hope you are not going back and leav me here again? " yeah I will but I will spend one month here with my friend, ta fada tana dariya,

Da yake ba wani kan gado gareshi ba ya ce "come escort me na oga send me' itama kan narawa tace ok Am coming

Ciki ta koma tareda janyo hijabi ta dora akan kayan jikinta ta saba yaron ta akafada tace Aunty zamuje yawo da EMA,

Kallon ta tayi kafin tace " keda EMA ko sai gyaran Allah kun hadu kun dace wallahi,

"He is very funny and friendly wallahi inajin dad'in hira dashi Akwai shafta " kodai gulma ? Keda yayanki ba ruwana

Fita tayi tana dariya sunyi tafiya mai nisa yana gabza mata labari da kuma Abinda ya faru dazu shida ogan shi yaja ya tsaya tareda dora hannu aka,

"Ewo I don die I forget wetin oga tell me wo ' come mo we go back and ask him, kallon shi takeyi cike da mamakin wautar shi ko waye ya dauke shi a aiki oho,

Da sauri sauri suka juyo domin yasan yayi laifi karya kara wani,

Shikuwa M.A da ya dauki lokaci yana jiran Emanuel ya kawomai sako yaji shiru kuma yanaso ya fita dole ya fito ya tsaya sanye cikin tree quarter da t-shirt na Como flag yayi masifar yin kyau ga wani Annuri da haske dake bayyane a fuskar shi,

Isowar Ahmed wurin shi yasa ya fara mai magana cike da takaici, " you have to find better cook for me I don't like this guy at All can you imaging him letting Kate and that stupid girl chioma in my house?

Dariya Ahmed yayi kafin yace "oga sun cika naci ne wallahi bebs din nan naga ka gama yayin su Amma sunki hakura,

" ni bansan me yasa duk Yarinyar da na sake mata fuska sau daya ba sai ta nace min, "farin jini ne oga, Ahmed ya fada cikin dariya,

" kodai rashin class I hate that kind of girls, "am idan mun fito daga gidan Hajiya zamu biya unguwar shanu inason inyi renewing wasu'

Yafada tareda yin wani tsadadden murmushin shi mai kyau, dariya Ahmed yayi " oga Karfa mu samo wasu karfen kafar kuma kuma kasan zuby ta kusa zuwa karka hada rigima,

Dariya yayi sosai tunawa da zubyn tashi da yayi domin tsohuwar budurwar shice kuma itace y'ar gidan ministern kudi Yarinyar naji da kyau da gata sun dade tare da juna suna Kwasar muguwar soyayya atsaka nin su,

Bata kaunar ganin shi da ko wacce mace duk da itama tana nata Rung's din a kasar wajen da take karatu,

Karaso wa sukayi itada Emanuel suna Kwasar dariya, tunda suka matso yake kallon ta yana mamakin wace mahaukaciyar ce take hira haka da Emanuel gata daga gani kamar tanada hankali,

Tana hango mijin yayar tata da wani a wurin tayi saurin tsayawa daga nesa domin tasan da shine ogan nasu da ake fada kuma wannan ne karon farko da ta fara ganin shi fuska da fuska,

"Amma anyi kyan dan maciji ta furta a hankali tareda zabga mai harara da kuma tsaki, w'anda ya ganta sarai domin kallon ta yakeyi sosai batareda ya cire idon shi akan taba,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.