Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel
Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt
Chapter 15 of 86
Saurin komawa tayi ta zari Allura batareda ta taba shiba ta tsira mai, kamar ta tsikari dutse ko motsi baiyi ba,
"Kingama kenan? Ya furta a hankali wanda yayi dai dai da karasowar zuby a kidime'
" me zangani haka? Baby lafiya ? Me wannan Abar takeyi a cikin gidan nan?
Ko juyowa baiyi ba bare ya bata Amsar maganar ta
Yasmin mai jira tayi wata irin dariya tareda matsowa kusa da zubyn cikin renin hankali "Bakida Amfani ne shiyasa ya kirani inzo intaimaka mai,
" kuma bari kiji gaskiyar zance a gaban shi "ni Matar shi ce idan ma ya fada miki wani zance na daban ne kika kuma y'arda dashi ke kika jiyo,
Nasaba ganin dubun ki a cikin gidan nan basu dameni ba bare ke don haka ki tattara koma tsan ki kibar min gida
Ai dai kingan mu har cikin gidan su da idanun ki don haka bana son ganin kafarki a cikin gidan nan again,
Ta juya cike da girgiza irin na na hada wuta zata fita, zuby da Yarinyar ta gama kaita bango ta wani irin fisgota ta kamar kara,
Wata y'ar karamar kara tasaki da saida ya zabura zaune ya zuba ma ikon Allah ido domin Abin Yarinyar yafara wuce tuna nin shi,
" ke karamar y'ar iska waya koya miki bariki
Ke y'ar gidan uban waye ?
Fisge hannun ta tayi tareda gogewa tace "Allah ya isa kinje kin gama iskan cinki zaki tabamin jiki mai tsarki,
Wani irin wawan marin da saida taga tagwayen taurari ya ziyarci fuskar ta batareda ta shirya ba,
Wani irin rudewa M.A yayi tareda saurin tare Yasmin dake shirin zubewa a kasa kuma yayi dai dai da Shigowar Ahmed rike da flask a hannun shi na tea,
Jikin MA na rawa yace " zuby how dare you? "Ya zaka tsaya tanbaya ta bayan komai a gabanka ya faru ,
" get out "" ya buga mata wani irin mugun tsawa saida ta zabura tayi baya da sauri "Ahmed get her out of my house before I killed her right here,
Hajiya Yasmin kuwa d'an karamin suman wucin gadi tayi kafin ta dawo hayya cinta tasaki wani irin kuka,
Ta fara kok'arin burgima jinta a jikin mutum yasa tayi saurin zabura ta mike tana gyara hijabin ta binta yakeyi da kallo mai tattare da ma anoni da dama,
Kana hango tsantsar bacin rai a idanun shi ganin marin da zuby tayiwa Yasmin yasa tuni ya manta da ciwon dake damun shi,
Bubbuga kafa tafarayi " wallahi ya Ahmed saika ramamin kuma yau zan koma gidan mu na rantse bazan y'arda ba katuwar banza ta dakeni,
Kama hanyar fita tayi tana kuka yayi dai dai da Shigowar EMA gidan yaci karo da ita zata fita,
"Friend ya fada da karfi yana kok'arin riko hannun ta " wata uwar tsawa Muhammad ya buga mai if you dere touch her I will cut up your hands
Yayi saurin matsa mata ta fice , komawa yaya ya zube akan kujerar tareda dafe goshin shi, what a drama Queen this girl is unbelievable,
Wani irin murmushi yake saki tareda tuna irin tsirsmai Allurar muguntar da tayi ya shafo wurin yana girgiza kai wace irin yarinya ce wannan?
What an Angel ya furta a hankali yana shafo goshin shi da har yanzu yana feeling hannun ta a wurin,
Bai tabajin hannun mace mai taushin nata ba duk da goshin shi kawai ta taba ya kara runtse idanun shi lokacin da ya tuna fadowar ta jikin shi da zuby ta mareta,
Wani irin harbawa marar shi ta kuma yi yace "this girl is going to end my life for sure, yasan samun ta y'anda yake so ba Abu bane mai sauki,
Yasmin kuwa tana fita ta maida kukan ta tsab tareda kyal kyale wa da dariyar mugun ta " shegiya mai hannun rodi gobe ma ki dawo,
Saurin hade fuska tayi tamau lokacin da ta hango Umar tsaye sanye da kaki yana shirin fita aiki ya hade rai shima ganin gidan da ta futo,
Tana matsowa yasha gaban ta "baki isa ba Yasmin baki isa ki hana zuciya ta sukuni ba kuma kije kina bin oga na yanzu don Allah zaki iya bin oga nine bazaki bani hadin kai ba?
Wani irin bakin ciki ne ya rufe ta tuni taji ranta ya baci fiye da tunani wato shi kallon y'ar iska ma yake mata kenan,?
" eh naga ba sabon Abu bane a bariki kuma ai kowa nason ci gaba idan na bika me zan samu kabarni inbi masu garin in more kabarni inbi maza ba mazan Hajiya ba mijin tace,
Ta girgiza jiki tareda yimai gwalo kuma wannan jikin kwalelen ka ta juya a guje tayi cikin gidan,
Maryam ta tareta "lafiya Yasmin wannan irin gudu? Dariya tayi " nida mijin makociyar ki ne, rike baki Maryam tayi "nidai Allah ya rufa min Asiri dake Yasmin,
" Allah ya rufa mana Asiri dai taji muryar mijin ta dake shigowa, "me ya faru Baban Auwal?
Shigewar ta tayi kawai batareda taji korafin shi ba, " kanwata zatasa watara na a kulle ni ko inrasa aiki na'
Ya fada mata duk abinda ya faru har na kwanakin baya duka, Maryam tace "oh Allah Yasmin bata girma ya Ismail nada aiki wallahi,
" Yama kirani yana zuwa yanzu bari infada mata, ta fada tareda shiga dakin nata, har ta tube ta daura guntun towel zata shiga wanka,
Zama tayi gefen gadon tareda zubawa jikin nata ido" Yasmin wane mai kike Amfani dashi ne naga jikin ki na kara fresh?
"Mai na daya ne har yau dove ba canji product din yayi wallahi " Hmm ya Ismail ya kirani yace yanata kiranki wayarki a kashe,
"Oh na manta da zan fita na kashe kinganta nan ta fada tana d'auka tareda kunna wa,
" to ki shirya yana nan zuwa yanzu, wani irin tsallen murna tayi domin Allah ya sani Akwai shakuwa mai karfi a tsakanin su
"Wayyo d'an Uwa zai zo dariya Maryam tayi " Yasmin kinason shi sosai ko? Shiru tayi na d'an lokaci "ina sonshi irin na yan Uwa kuma yana matukar bani tausayi wallahi ya cika hakuri kina ganin da aka fasa Auren ku ba w'anda yaji ko maganar shi kuma nasan ya damu,
Shiru Maryam tayi kafin ta mike " ki shirya ki fito kuma don Allah Yasmin ki rage daukar magana kuma ki tuna wallahi badon sanadi da dalili ba baki isa ko kofar gidan Muhammad kibi ba don haka ki kiyaye,
Ta fita, binta da ido tayi tareda cewa "Ai sai dai innabar barikin nan zanfita a hanyar shi kuma wannan Umar din sai na kunna mai gobara a gidan shi zai gane,
Karfe tara ranar sukayi shirin tafiya aiki bayan ya sha magun guna domin yaji karfin yin Aikin shi convoy dinshi na Jere suna jiran shi ya fito cikin shigar shi ta green kakin shi akoda yaushe,
Hannun shi rike da Beret mai dauke da logon gauraka a jiki bayajin shi dai dai har yanzu Amma kasance war shi oga kwata kwata dole ana bukatar shi a office,
Dai dai lokacin Yasmin ta fito daga cikin gidan sanye da riga da sket na purple Atanfa da kuma jan gyale tayi wani irin kyau Kamar ka sace ta,
Taku take dai dai fuskar ta a sake a kamun tana cikin farin ciki ta ja ta tsaya a kofar gidan tareda daukar waya tana duba hanya batareda tako kalli kofar gidan ba,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.