Complete Hausa Novels

Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel

Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt

Chapter 53 of 86

MA bai samu kanshi ba a yau saboda shirin tafiyar su tunda ya koma office suke kaida kawowa naganin sojojin shi sun shirya sosai domin tunkarar mugayen barayin, Y'an Uwan shi ma koda suka kirashi zasu kai kayan motoci kawai ya bada yace aje a kaisu gidan,
Kamar shine ke shigowa Unguwar motocine guda goma a jere guda biyu sababbi wa inda aka zubo kayan Aciki sauran kuwa Y'an Uwan shi ne tareda escorts din shi dake take mai baya,

Kasan cewar falon baba yafi girma nan suka bude musu aka gyara Aunty maryam ma tazo suma sun hadu harda Zainab din ismail tazo domin tarbar kayan yasmin Y'an Uwa sun shirya musu tarba irin ta Al Ada, mama hindatu uwar gayya tuni ta mike tareda musu tarbar girma su Aunty Halima dukan su sukazo kawo lefen na kanin nasu guda daya tal, sunyi matukar yabawa da tarbar girman da suka gani daga gidan na su yasmin,

Umarni Babba yaya ta bada aka fara shigo da akwatuna, sojojin ne suka rika jido su ana jera su a tsakiyar falon tuni tsoro ya rufe su ganin Anshigo da saiti shida kuma ana kokarin shigo da na bakwai ai tuni mama hindatu da Wasu tsoffi suka fara rangada guda suna shewa "Allah mai iko ya' tayi goshi tubarkallah, saida su yaya Halima suka fitoda key na sabbin motoci guda biyu suka Ajiye masu bayan manyan gana most go guda uku na kayan sa lalle,

Ai su mama tuni sun rasa ta cewa sai kallo kayan ma sun rasa Wanda zasu bude sai karamar kit guda daya da su yaya Halima suka mikawa mama hindatu "ku adana wa innan gold dinta ne a ciki, ai tuni mama hindatu ta karbe tace sosai kuwa kodan mutane wannan basai annu nasu ba gaskiya, ga motocin ta can a waje za a wuce mata dasu gidanta idan kungani, ai guda kamar zasu cire kunnen mutane a ranar, saboda farin ciki ganin kayan,

"Ina Amaryar tamu take ne? Suka tanbaya, "ai ta gudu tunda ta gano kan zancen, "dariya sukayi saikace a kauye Aida ta tsaya munga matar Autan hajiya, bayan ma mara kunyar ya gama dauketa saida ga baya yace wani biki Ai baban hajiya sai a hankali ba ruwan shi da kunya sai kunyi hakuri da surukin ku, "aa kubarshi zamanin sune watarana sai labari,
Sun yi hira sosai kafin sutashi tafiya cikeda kayan soye soye na Y'an kawo lefe manyan robobi da kuma carton carton na drinks dai dai karfin su sukayita godiya batareda sun raina musu ba kudi dai suka ki karba sukace basai sun basuba wallahi Allah dai ya karo musu d'an kon zumunci tareda zaman Lafiya a tsakanin ma auratan,

Bayan sun tafi su mama suka baje kayan abin ba a cewa komai ko lefen Zara sai haka don kayan ciki kawai sai sun girgiza mutum bare gwalagwalan da aka zubo, fada bata bakine ai, su baba kam kasa cewa komai sukayi, mama hindatu ce tace a fadawa mijin kawai ya kwashe kayan ya kai gidan ta yafi gudun mutane ko Barayi tunda anriga ansan tayi aure basai An tsaya kiran mutane suzo ganin kaya ba

Baban zango yace "haka ne har motocin ma ai zasu kawo mana Barayi BMW ce fa daya kuma crv4 ce ina zamu Ajiye su anan a biyo dare don haka zan jira zuwan shi sai ya kwashe su, baba dai cewa yayi kaya sunyi yawa anyi riya "baruwan ka yaya matar shi ce duk Abinda yayi mata yanzu bamuda ta cewa don kowa ya shaida sun tara tunda ya dauketa na tsawon sati guda, "tabbas kuwa kilama da rabo, inji mama hindatu,

Ita kanta Yasmin ta tsorata da irin dukiyar da aka kawo mata wai lefe takasa cewa komai tasan MA na matukar sonta kodan irin rawar kafar da yake nunawa akanta ya isa ta gamsu 100% yana mata so mai tsanani da ace ya Aureta domin manufa ne da yanzu da yasamu Abinda yakeso da tuni ya barta kamar sauran mata , wani irin kaunar shi taji ta kara ratsa ko ina na jikinta ta koma dakinta ta kwanta tareda rufe idanun ta "me zata yimai domin farantamai itama? Me zata yiwa MA yasan cewa tana mai so kila fiyeda ma Wanda yake mata, gaba daya tunanin shi ya shigeta bataji shigowar Aunty maryam ba saida ta dafata ta tashi zaune tareda rungume Aunty maryam tasa mata kuka,

"Ikon Allah Meye na kuka kuma keda zaki yi farin ciki yasmin, "Wallahi you are very lucky samun miji irin Oga MA sai an tona kinga motocin ki kuwa yanzufa motocin ki uku yasmin ko sarkokin ki kawai sun isa su sai gidan mu uku Amma duka ke Kadai ba Abinda zanfada miki Yasmin sai dai ki kara hakuri tareda yimai biyayya akan duk Abinda bai kauce hanya ba

"Aunty nasani wallahi me zanyi mai infarantamai rai yau Aunty? "Zokiji ta fada mata tana mai mata rada a kunne ido ta dago tareda zaro ido Aunty su mama fa,? "Ki share kawai baby kije gobe fa zai tafi, shiru tayi kawai kafin ta zabura ta ciro wata Riga da wando damammu rigar ta na dauke da rubutu mai kyalli an rubuta lucky me da manyan harafi rigar ta kamata sosai fara sai kuma wandonta pencil baki yana sheki ta cikin shi golden wajen kuma net ne baki ya hadu sosai duk cikin siyayyar da sukayo A Abuja ne data tanada domin yimai Ado, ta gyara kanta dakyau tareda feshe jikinta da turaruka masu mugun kamshi Aunty maryam ta fito da wani Abu ta bata ungo ki matsa da sauri miski ne mai hadi zaki bani lbr idan kin dawo,

Matsawa tayi ba musu dontayi kudurin farantamai rai a yau koda zata mutu kuwa sai ta nuna mai tana Sonshi itama a yau tayi wanka da turaruka Kala Kala tayi light make up tareda saka hijabi mai gyale tasaka plat shoe da jakarshi mai kyau Aunty maryam ta ci wow sis kinganki kuwa matar M.G MUHM'D Abdullah kinfito as matar officer dinki, tace muje intake miki kafin su mama su gane zaki fita, "idan suntanbayeki ina inafa? "Zance kina gidan kawata har yanzu baki dawoba ai ba Wanda yaga shigowarki bayan sunfita ta d'an tsaya tayi shiru, "Aunty ya hana ni hawa mashin fa, waya fada miki mashin zaki hau, ganin yaya ismail a gefe yasa maryam ta karasa tareda gaidashi tace Gata nan yaya, dama ta gama tsara komai yazo yana tsokanar ta "Amaryar general muje inkaiki ranki ya dade tunda ankwala ni da Kasa,

Kunya taji sosai ganin ya manta komai har yana shirin taimakon ta wajen farantawa gwarzon mijin nata bazata manta dashi ba a Rayuwa, shiga tayi Saida suka fara tafiya ta fito da wayarta ta kirashi, ringing daya ya daga, "my only wife, yafada cikin gajiya, "kana ina ne? "Office Amma yanzu zanje gida inyi wanko dole inzo inganki kafin intafi gobe
Me zandafa maka? Tafada kai tsaye, "Anything from my wife zanji dadin shi yunwa nakeji gashi na gaji baby tunda nabar wurinki wanka kawai nayi na koma aiki haryanzu gashi ina kai,
Ok saikazo ta fada tareda katse kiran, saida ya ismail ya Ajiyeta tareda tsokanar ta ya wuce Abinshi,
Kofar gidan ta nufa cikin natsuwa sojan dake kofar gate din cikin sauri ya bude mata tareda Sara mata don yaganeta itace matar ogan, don yanzu basa yarda kowa yashiga saida izinin mai gida wannan kuwa basu isa su hanata ba su jawa kansu,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.