Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel
Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt
Chapter 76 of 86
Iyaye kudaina Al adar kai Amarya kuce wai sai Ankwana an bude kai za a watse wace irin Al adace wannan mazajen da basuda hakuri yanzu suna rawar kafa su shige daga ciki, nafarko ga dorawa miji nauyi idan baida karfi na biyu tsoffi na can na bacci ya kira Amaryar shi susha Amarcin su aikin banza wannan ai muguwar Al adace , ni munkai Amarya muna Y'an mata mijin yakirani gefe muka sirrinta tuni na rako mai ita sai fa safe ta rika tsinema zuri'a mu kab ta kwashe musu Albarka don haka ku daina wani takura kanku wallahi saboda kwadayin shayin gidan Amarya ko banzanr A Ada,
Cikin farin ciki suka tashi tana yin wanka ta janyo kayanta najiya zata mayar ya ce ta tsaya, wata doguwar rigar Abaya mai tsada mai fadi ya bata light green ta hadu sosai irin ta haddadun matan nan ce gyalenta nada fadi sosai don haka tasaka tana dariyar halin shi wato ya shiryama kwanan su kenan, shima cikin material na maza kalar kayanta ya saka fited bai sa hulaba ya dauki mata jaka tareda rikota suka fito, lokacin karfe goman safe mutane sunfiffito a harabar hotel din ko ina suka ratsa idanun jama a kansu, what a perfect couple sunyi mugun match motocin shi na jere ya bude mata tashiga ya shiga shima suka kama hanya ya janyo laptop dinshi ya bude ta zuba mai ido yanda yake aiki cikin aji da natsuwa ya wani kame kamar bashi ya gama mata kuka ba, jin take soyayyar shi na kara narkar mata da zuciya, dole ta zage ta kara rike kayanta kar a kwace mata shi, don ko wace mace dole tasoshi ga kyau ga kudi ga mulki ga kuma iya tarayrayar mace dole mata su like mai,
Su baba na kofar gida da fadawan su domin angano su din sun cancanci hakan don sun wuce da tunanin Y'an Zango irin wannan suruki da sukeda shi sai abin kari suke ci, motocin shi suka tsaya saida ya karasa aikin shi ya rufe tareda ajiyewa ya fita ya zagaya ya bude mata motar don yanzu tariga tagama sabawa da halin shi tasan duk in sun fita tare shike bude mata mota bayan anvude mai, bayason ana bude mata, fitowa tayi ya dakko mata Jakarta suka jera saida ta gaida su baba kafin ya mika mata Jakarta ta wuce ciki sunata sa Albarka baba bakinshi har kunne ganin yanda Autar tashi ta zama kamar sarauniya, zamanshi yayi cikinsu kafin su ismail da Ahmad ma suka iso don su tare suka kwana a dakin ismail dake gidan, baban zango yace ismaila kuje ku karya naku na shago Abin karin tashi kuje muhamdu, to yace suka wuce ismail yafara cewa "Allah yasa ka iya shan koko ranka ya dade? Dariya Ahmad yayi " ai oga yafison gargajiya ko kasan garin yin miyar kuka kanwata ta siye zuciyar oga, dariyar shakiyanci suke mai sosai yace " ai sai na bude restaurant na kuka soup da tuwo da sunan Yasmin saboda history, dariya suketa mai ismail yagama fahimtar cewa wato karamin mutum shine yafi kowa girman kai a Rayuwa ba Wanda ya gaji Arzikiba,
Ita kuwa tana shiga aka fara yimata tsiya abokan wasa " idon ki ke nan manya? "Eh ko idon ya canja ne? Ta fada cikin mayar musu da Amsa don bata jin kunyar komai yanzu yanda mijinta ya dorata kan darasin itama yanzu batasan kunya ba Sam, matsawa tayi ta gaida su mama dake yanka alayyahon wainar da zasuyi yau, " mama hindatu tace " yata kin iso? " eh mama na nakaina ina Abin karya war mu Kubani na Muhammad inkaimai bai karyaba, Ajiye wuka mama tayi ta kalleta " barnan mara kunyar wofi Aike zaki fada mana Abinda ya dace ko, dariya Aunty maryam tayi ganin dramar da suke tace " ke mai miji ankai musu nasu zo ki karya kema, tashi tayi tana dariya mama hindatu tace " banga laifinki ba wallahi mazan zamanin nan kama Abinki y'ar nan kinji, " nagode mama na tafada suka shige falon ta, maryam tace " kin boni kema kin zama kalar mijinki Koda yake ai sai hali yazo daya ma ake haduwa dama kema ba kunyar ce dake ba kalli kinbi miji kunkwana hotel Amma kinshigo ko a jikin ki mirsisi, "toh yace muje sai inki kuma tunda kowa yasan inda naje meye na kunbiya kunbiya bayan gama cikin shi a marata, dungure mata kai tayi ta fita " Allah ya shirye ki wallahi, Ameen tafada tareda bajewa tafara karin ta,
Karfe goma sha daya suka shirya domin zuwa gidan Amarya a lokacin gidan ya kuma taruwa domin taron ranar don yanayin tasu Al adar, Kiranshi tayi tafadamai kafin su fito don gudun rigima lokacin yana dakin ismail yana aiki da laptop dinshi, ta canja cikin wani leshi riga da sket baki mai shegen kyau da tsada ta sako hijabi gudun rigima tayi kyau itada Aunty maryam da wasu mata guda biyu
Ya fito tareda tsayawa yana jiranta, tana karasowa ya matso yana zuba mata ido duk shigar da tayi saita fita daban a cikin mata, matan suka gaisheshi tareda wucewa kadan su basu wuri ganin ya tsare gida, tace "ina ya Ahmad yaban key din motar shi muje da ita da d'an nisa kadan, " ok ko inkaiku ne? "Aa ka barshi yanzu zamu dawo eh kifa shirya gobe zamu koma tunda angama taron, " ok tace duk da ba haka tasoba taso ta zaga dangi,
Key motar Ahmad ta karba ita ta jasu da kanta yana kallon ta har tabar wurin wani irin jin dadi yakeyi idan ya kalleta komai tayi burgeshi takeyi, yakoma yana maijin shaukin ta, su baba ma duk akan idon su suka fito har lokacin da sukabar kofar gidan Aunty maryam na gefen ta matan na baya,.
Sai yamma suka dawo lokacin gidan duk an watse sai su mama da sauran yaran gida da Zainab, ranar sunyi kwanan hira domin dolen shi hakura yayi ya kyaleta saidai Yabada umarnin akwasomai kayanshi a hotel shima zai kwana cikin su Ahmad, duk da basu kwana daki daya ba sunkwana waya abinsu, Su Ahmad sai toshe kunnen su sukayi har sukayi bacci idon shi biyu, haka itama maryam tayi bacci tabarta, yace is better su kwana suna waya da ya kwanta shikadai bazaiyi bacci mai dadi ba,
Haka suka raba dare kafin yabarta ta kwanta ya janyo laptop yaci gaba da aiki har Asuba su Ahmad suka ganshi a inda suka barshi, " oga Kayi bacci kuwa? " Nop ba baby ai ba bacci,
Ismail yace " tom kaji manya masu SOYAYYA lallai kanwata na wuta, harda gobara ma yi takeyi indai my yasmin ce, Ajiye laptop dinshi yayi suka fita domin zuwa masallaci,
Saida yadawo masallaci ya kwanta bacci baitashiba sai karfe goma, yasmin ce ta shigo dakin cikin Adonta ta haye katuwar katifar tareda shige wa jikin shi, "Wake up my sleeping beauty, tana manna mai kiss a baki, a hankali ya bude idanun shi akanta kafin ya karasa waresu ganin ta Bako mayafi, yabata fuska haka kika fito? Hijabinta ta nuna mai, gashi can nacirene kaga kwalliya ta kawai, tashi yayi zaune tareda tallabota kan kafafun shi, " kinyi kyau sosai my beautiful wife, " tank you my lovely and handsome man, dadin maganarta yaji yace baby " Kinsan nifa yanzu haka ina bukata, ya za ayi? In rufe kofar ne? Ta fada kai tsaye " um um kishirya mutafi gidan mu yanzu, " angama mijin Aljannah am ready to go,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.