Complete Hausa Novels

Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel

Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt

Chapter 10 of 86

Zuba mata ido yayi kafin ya mike kawai ya nufi dakin su Maryam din tana ganin shi ta zabura jikin ta na rawa "Maryam baki y'arda da zabi na ba ko?

Kina so ki watsa min kasa a ido har zaki iya aiko uwar ki wurina ta fada min bakyason dana sai wani bare kuma soja

" toh shi kenan kije ki Aure shi Amma ki sani ba hannu na a ciki kuma bada yawu na ba kuma na gode wa Allah da yasa bake kadai bace Yata don haka zan hada mama na da Ismail nasan ita bazata bani kunya ba,

Wani irin kuka tasa jikin ta na rawa "baba kayi haku.." Ki yimin shiru kuma ranar Aurenki da nasa ba fashi kije ki nemi wani uban ya daura miki Auren Amma nidai kin gama zama a gidana,

Ya fita Abinshi ranshi matukar bace ya kira Yasmin tareda neman Alfarmar ta y'arda da Auren Ismail,

Abin yazo mata a bazata Amma kodan ta taimaki y'ar uwar ta dole ta y'arda, saidai ta nemi Alfarmar Baban ta ya barta ta karasa karatun ta kafin ya mata Auren ya kuma Amince,

Gefen Ismail kuwa ba wata matsala domin shi a yanzu tuni dama yafara son Yasmin din don Bazai iya furtawa Baban bane don haka canji yafi yimai dadi sosai,

Baban su Mahmud shine yayi ruwa yayi tsaki har aka daura Auren Maryam da Ahmed kuma mahaifin ta yace bashi baita kuma karta tako mai gida bai kuma y'arda kowa yayi hulda da ita ba duk da irin lallashin da kanin nashi yayi ta yi Amma fur yaki,

Shiyasa Yasmin take sato jiki tazo wurin y'ar uwar ta , sai bayan ta haifi Auwal ne baba ya fara sakko wa jin labarin ta kuma samun wani ciki ba tareda d'an ya shekara ba yasa ya fauwala wa ubangiji yasan cewa rabon haihuwa ne sanadi da yanzu yayi jikoki a kan titi,

Wannan shine d'an taka'i taccen tarihin Abinda ya faru sai kuci gaba da biyoni domin jin yazata kaya da Auren Yasmin din taku"

*Matar soja*
[8/30, 2:56 PM] Feenerh Wrtr: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
_*BARIKI*_
_Auren soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

_written by fenerh_
Maman Ammar

*Dedicated to*
Fiddousi mainasara

(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

7&8

Maryam batasan wainar da ake toyawa ba saida Maman Amla ta zo gidan da kanta tana uban kuka,

Har kasa tasa guiwoyin ta tana rokon Maryam don Allah su bar mata mijin ta gaba daya yace idan bai samu Yasmin ba itama zata barmai gida,

Abin ya bama Aunty Maryam mamaki ganin ko a jikin Yasmin yasa tasan Akwai wata akasa tayi saurin kallon y'anda ta juya musu baya,

"Yasmin meke faruwa ? " AUNTY ki tanbaye ta ita data zo miki gida da kuka , kuma tasan banbacin karuwan gida dana bariki yau ba boka ba malam mujiya kwakwal war mijin mace idan tayi wasa kuma wallahi tayi gidan su,

Baki Maryam ta saki kafin ta lallashi Maman Amla ta tafi tareda kwantar mata da hankali bayan ta rakata "ki kyale Yasmin haka take kuma tanada wanda zata Aura d'an uwan mu ne kawai ta daga miki hankali ne,

Wani dadi taji tareda ba wa Aunty Maryam hakuri akan zagin ta datayi " kiyi hakuri Maman Auwal bazan kuma fitina dake ba insha Allahu,

Koda ta shigo gidan kasa ce mata komai tayi saidai idanu kawai don tasan halin y'ar kanwar tata idan ta matsa sai yanzu tace zatayi mata yaji gwara ta bari idan tayi niya zata fada mata da kanta,

*tushen labari*
2years back,

Tafe suke a kan hanyar su ta dawowa daga makaranta sanye suke a cikin fararen kaya da d'an karamin hijabi sai bakin low pass a lamar dai malaman jinya ne su

Kyawa wane su sosai duk da kana ganin su kasan yaya da k'anwa ne Amma Akwai shakuwa mai girma a tsakanin su

Saidai kanwar tafi yayar nesa ba kusa ba kuma kirar jikin su Akwai banbanci domin Maryam nada jiki kadan ita kuma Yasmin jikin ta d'an dai dai ne,

Zasuyi matukar burgeka idan kaga y'anda suke tafiyar su kamar wasu kawaye,
Motace tasha gaban su fara tas kirar Lexus sukayi saurin tsayawa cak,.

Fitowa yayi sanye cikin kakin shi yayi matukar yin kyau kanshi ba hula ya fara basu hakuri,

"Y'an mata Kuyi hakuri na tsayar da ku akan hanya, wani irin mugun kallo Yasmin ta watsa mai " kadai yi niyyar kashe mu Allah ne baiyi ba saboda ka ganka soja to Allah ya fika , ta furta tana mai murguda mai baki,

Saurin riko hannun ta Maryam tayi Alamar ya isa mana, dariya yayi ya kalli Maryam "kibawa kawar mu ko kanwar muce hakuri naga tanada tsiwa,

" kayi hakuri ba komai ta rikota suka kama hanya da niyar wucewa yayi saurin shan gaban su " don Allah meye sunan ki ? Ya fada yana kallon Maryam, ta fada mai kai tsaye yayi "suna mai daraja don Allah wane unguwa kuke ne yau nakai kwana uku ina ganin ku a dai dai nan hanyar kuma saboda ku nake biyo wa yau nakasa hakuri ne a yimin uzuri inzo gidan k....

...karma ka fara wallahi don Aunty nada mijin Aure ni kuwa ko maza sun kare ban Auren soja don haka bamu hanya ko inbangaje ka wallahi,

Finciko hannun Maryam tayi sukayi gida batareda ta kuma kallon inda yake ba, Maryam na wai wayen shi domin gayen ya matukar burgeta ga kakin ya karbeshi sosai,

Shiga motar shi yayi ya rika binsu har saida yaga gidan su ya koma barrack w'anda su kuma suna isa kofar gidan su sukaci karo da Ismail wato w'anda. Maryam din zata Aura,

Karo na farko da taji takaicin Amince was Auren da iyayen su keda burin hadawa,
Tasowa yayi yana musu barka da zuwa,

Yasmin ce tayi carab tace " ai wallahi ya sama'ila idan baka dakko mu sai anyi ma fashi a hanya wataran kaga wani mayen soja yau ya biyo ma mata,

Dariya yayi "kai Yasmin kin cika mita nasan meye matsalar ki daga yau na gama interview dina ni zanrika dakko ku insha Allah,

Maryam dai wuce wa tayi batare da ko gaishe shi ba, yasan halin ta na rashin son magana don haka bai cika damuwa da shariyar ta ba,

Karfe takwas na dare suna zaune a tsakar gidan nasu dai dai na rufin Asiri aka aiko ana kiran Maryam, saida gaban ta ya fadi ganin irin kallon da Baban ta yayi mata kuma suna matukar tsoron mahaifin nasu bayason wasa,

" Maryam waye kika bashi izinin zuwa gidana bayan kinsan kinada miji a kasa? "Wallahi baba bakowa, " to bari inga kowaye,

Yana fita Mama ta ce "Yasmin waye yazo wurin y'ar uwarki? " mama ni yazan San ko waye ? "Nasan tare kuke ai koma waye zaki sani,

" nidai bansan waye ba, "to ku kiyaye kafin ku hadu da fushin babanku Kunsan burin shi akan ku ita kuma tasan tanada mijin Aure don haka ta kiyaye,

Shiru kawai sukayi har Baban ya dawo ya ce wani soja ne wai sunan shi Ahmed ya mun bayanin wai yana son Maryam ne toh nabashi hakuri bayan nayi mai bayanin tanada mijin Aure,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.