Complete Hausa Novels

Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel

Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt

Chapter 65 of 86

Wani irin kuka ta sa Mai Kara "yanzu bazamu ganshi ba? "Sai sun kaishi resting room in sun gama dubashi, kutaya shi da Addu a kawai mama, "innalillahi wa inna ilaihirraji un, hajiya keta mai maitawa, wuri ta samu ta zauna Yasmin ma ta zauna har wani jiri takeji yana neman kadata, yanzu shikenan baban Amla ya rasu wayyo duniya duk da batada halin da mijin nata yake cikiba Amma ta mugun tausayawa Maman Amla, matsowa yayi yace ta aramai wayarta zai kira maryam,

Shiya fada mata halin da ake ciki tareda bata umarnin zuwa da breakfast saboda su hajiya , hankalin maryam ma yatashi ta kira su baba ta fada musu suma, kafin kice me Asibiti ya cika taf da Y'an uwa da abokan arziki harda Y'an Uwan shi duk sunzo kowa sai Addu ar Allah yasa suga Alkhairi sukeyi, yasmin dai tayi kuka hartaba uku lada sai lallashin ta akeyi "kidaina kukan nan haka kinga bake Kadai bace ga tea an hada miki kisha karki fadi kijama mutane wata damuwar,

Hajiya keta lallashin ta mama ce tace barta hajiya tunda batada hankali tazama yare bazaki tayashi da Addu a ba zaki zauna kina kuka ko shine zaisa ya warke ko kuma kaddarar shi ta canja, "bita a hankali Saude, baba yafada yana maijin tausayin y'ar tashi, wasa wasa har karfe goma ba su sashi a idoba ga kukan ta yaki tsayawa kowa dake wurin ita yake tausayawa domin kukanta irin mai ban tausayin nan ne, jiya ta gama waya dashi yau akirata ya na cikin mugun hali ba Abinda take tunawa irin Alkawuran da yake mata kwanan nan "baby ina dawowa zamuje muma baby na shopping baby yafara kicking? Kullum maganarshi kenan babyn shi da kuma kewar ta,

Shafo cikin tayi tareda runtse idanun ta tayi magana a cikin zuciyarta "insha Allahu babanka zai tashi ya zai yi wasa dakai my baby, duk hankalin su yagama tashi ganin har shabiyu ba wani magana sai likitoci ke fita da shiga masu kaki, sai kusan karfe daya suka kira Ahmad, yashiga saida ya dauki lokaci ya fito ta tashi da Sauri ta nufeshi "Lafiya baban Auwal? "Alhmdulillah kuzo keda mama ku ganshi basa bari mutane na shiga ciki ko yanzu na rokesu ne da kyar, cikin sauri ta wuce ko hajiya bata jiraba, saidai tundaga farkon dakin jikinta yayi mugun sanyi ganin sojoji Kala Kala a jere kowane da tashi matsalar wani ba hannu wasu ba kafafu wasu kuma bama Susan inda kansu yakeba,

Wallahi Y'an uwa duk wadda tasan 44 gefen Y'an lfy dole idan har ta taba shiga saita koka sojoji ne daga meduguri sai ka musu kuka kaga mutum da ranshi ya rasa kafafu ko wani bangare na jikinshi saboda bautawa kasar shi wallahi kutaya sojojin mu da Addu a suna cikin hadari a Rayuwa wata ma mijinta zai mutu shekara guda bazata sani ba Wasu ko gawar su ba agani, Allah yasa mudace,

Kamar wadda kwai yafashe mata takasa karasawa wajen datake tunanin MA dinta ne akwance hannun shi a nannade ga kanshi ma haka duk fuskar shi a kunbure kamar bashiba wani irin jiri yaso yarda ita hajiya ta rikota tamau duk da batada karfi, takarasa da ita cikeda karfin hali, kuka ne ya kufce mata ta rufe bakinta domin akwance yake kamar gawa ko motsi bayayi ga oxygen a hancin shi batasan lokacin da ta sulale a sumeba, da taimakon Ahmed suka fita da ita saida aka bata gado a wani word din suka daura mata drip tareda Allurai kafin ta farfado, ta zabura ta kuma sa kuka "mama ku ciremin ruwan nan zankoma wurin shi inganshi ya farfado!?

Mama ma idanun ta sun ciko sosai don ta bata magun tausayi Aunty maryam kam saida tayi kuka ganin halin da mijin y'ar uwar tata ke ciki, "kiyi hakuri yasmin Kici wani Abu kinga kodan cikin ki likita ma fada yayi yace harda rashin cin Abincin ma ya janyo miki jiri, ki kwantar da hankalin ki da izinin ubangiji zai samu lfy, "mama bakiga halin da Muhammed ke ciki ba tafada tana wani irin kuka, kiyi hakuri kinfi mahaifiyar shi Sonshi ne ki kwantar da hankalin ki KO zata samu kwarin guiwa kina kallon tsohuwar nan akwai tawakkali da karfin imani,

Haka suketa mata Nasiha saida ruwan ya kare suka matsa mata tasha ruwan tea mai kauri saidai tana gama sha tafara kelaya Amai saboda yunwar da ta shigeta, maryam ta kuma hada mata ta sha kadan, ta mike ita dai zata koma wajen shi, sun canja mai daki saboda gudun hayaniya sunason idan ya farfado suga aikin da sukayi mai akai KO anyi nasara, dakin ta koma duk da nurses din sun so hanata ta shige tareda zama kusa dashi ta riko hannun shi mai lafiyar ta dora a saman cikinta tareda fara yimai magana a hankali, "my sugar please katashi babyn ka na son ganinka gashi yafara motsi, ina kewar ka please ka tashi bazan rika complain nagaji ba daga yau KO sau goma zakayi,

KO motsawa baiyi ba haka ta cigba da zuba mai sambatu daga karshe ta dora kanta saman hannun mai Lafiya, kallon kirjinshi fari tayi mai suma luf luf a waje ba Riga a jikinshi sai dogon wandon kaki kawai saboda kana nun ciwon dake kota ina a jikin nashi, duk da yana cikin ciwo muscle dinshi na nan sai Kara kunbura da sukayi , wata nurse ce ta matso tareda cewa "madam please karki dame shi fa bamason ana mai hayaniya,

Itadai kokarin janyo zanin rufarda ke gefen gadon takeyi ta rufemai kirjin shi don wani irin kishi takeji yanda nurse din nan ke kalle mata miji ba Riga, "noo please madam he needs a fresh air so that the wound will heal quick, anki abarshi a buden shegiya wato ta kare Mai kallo, tafada cikeda masifa itadai nurse ba Hausa bataji Ashariyarda ake lafta mata ba ta juya ta fita tana mamakin yanda Yasmin keda mugun taurin kai taki KO bari ta kula da wannan handsome guy din duk dama wai bai da Lafiya baima san me akeyiba,

Sai kusan dare mutane suka watse anyi fama da ita ta tafi KO wanka tayi taki sallah kawai take matsawa tace sai ya farfado zatayi wankan hajiya tace abarta tunda Ahmad na kusa tunda shima bawai an sallame shi bane kawai ganin ciwon ogan nashi yafi nashi dole ya mike , gadon dake gefen nashi ta kwanta wayarta ta kunna da tun zuwanta bata koma kantaba gaba daya ta kasa bacci daga karshe ma dadduma ta haye tafara nafiloli, wajen karfe shabiyu ya bude idon shi, a hankali yakebin dakin da kallo ya hangota a zaune a sallaya, motsawa yayi domin kanshi da bakinshi sunyi mai nauyi sosai,

Saurin tashi tayi ta nufi gadon da sassarfa, idon shi dake cikeda ciwo ya zuba mata domin sunyi mugun ja da Alama yanajin ciwo sosai Amma yakasa cewa komai sai ido, " baban baby kafarka Alhmdulillah tafada cikeda farin ciki ta riko hannun shi sai wani irin hawayen farin ciki ke fita " Alhmdulillah kafarka Sannu my sugar, tafada ganin yana juya kai ta zabura batareda tsoran komai ba tafita, a nan ta samu likitan dake on duty ta kirashi jikinta na rawa,

Yana zuwa ya saramai "tank God oga you are fine girgiza mai kai kawai yayi ya duba shi tareda zare mai oxygen din yace " madam congrats oga is Alright saidai raunin jikinshi da hannun shi da aka dora sai ankula kar aikin ya lalace, godiya tayimai yace zata iya bashi KO ruwan tea ne saboda yasha drugs dinshi, jikinta na rawa ta bude kayan tea da aka ajiye musu manya ta hada mai dama akwai katon plask ta zuba ruwan zafin tareda Ajiye hijabin ta domin likitan ya tafi, ido kawai yake binta dashi kayan baccin jiyane a jikinta,
Masu santsi Riga da wando dogo rigar Mai hannun shimi ce KO bra babu a juk8nta,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.