Complete Hausa Novels

Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel

Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt

Chapter 55 of 86

"You are a soldier wife ki zama jaruma so that idan yaran mu sunzo suma su zama jarumai, saurin tashi yayi tareda yaye Abin rufar ya shafo marar ta "baby ina son inga yarana inason inganki da ciki please kibani babban farin cikin da nake jira yanzu, tashi tayi ta shige jikinshi tareda dora lips dinta a bakinshi ta d'an tsotsa kadan kafin ta cire ta zubamai ido yanda yake kan lashe bakin kamar Wanda yasha Zuma ko sweet "Zuma na ni takace bazan iya Rayuwa da ko wane namiji ba nasaba da kai ka Riga Kayi training dina nasaba da mijina mara kunya I can't be with anyone ba wani namiji da zai bani farin cikin da nake samu daga gareka kaine ruhina ina sonka Muhammad so mai girma I tink na fara sonka tundaga ranar farko danafara ganin ka shiyasa nakejin tsanar ganin kowace mace a kusa da kai ko gidan ka, ko lokacin da kafara kissing dina bawai haushin hakan najiba haushin ganin zuby ne a cikin gidan nan ya bata min rai ina da kishin da yafi naka bazan iya jure ganin ko wace shegiya kusa dakai ba Allah zan iya kisan kai akan ka wata rana,

Bakinta yayi saurin kamawa ya tsotsa sosai kafin ya saki cikeda jin dadi, "oh ana sona dama akayita garani ai bansani ba meyasa kike jamun Aji kika wahalar dani kikasani kullum cikin tunani kullum banda sukuni I na hango irin ta asar da zanyi idan aka hanani ke wallahi zan daukeki ba Wanda zai kuma ganin ki, Kinsan har gini nayi miki na musamman yanzu furniture's kawai zasu kawo daga Dubai a zuba gidan na Unguwar rimi, sai nadawo zamuje muyi hutun Amarcin mu a can, "wane Amarci bayan ka shanye romon tun bamu tareba, "waya fada miki ni ko rabin spoon har yanzu ban shaba,

Jin kiran sallar magrib yadawo dasu daga duniyar soyayyar dasuka Lula ta diro cikin sauri, "Zuma bari inyi sauri ba asan fa na fitoba nabar Aunty maryam da jirana, sakko wa yayi Shima yana zubawa kirjinta dake rawa saboda yanda take motsa jikinta, ya matso tareda shafosu, tafiya zakiyi kibarni? Ya fada kamar wani jariri, "Sory honey idan kadawo zamu kasance tare har Abada, sunkutar ta yayi "sai mun kuma wanka kafin muyi salla sai in mayarda ke,

Wanka sukayi ta mayarda kayanta ta saka hijabin ya zubawa jikinta ido tareda kankance ido "haka dama kika fito kuma har wannan gayen ya kawoki ya ganki a haka? "Me nayi? "Kinga yanda kikayi kyau da shigar ga komai ana gani gaskiya nidai gobe zaki fara zuwa koyon moto banason kije ko nan da can da driver kije da kanki idan kin iya kuma banyarda da yawo ba, "ok mijin, tafada tana dariya, ya bata fuska "Am serious niba sakaran miji bane ki boyemin kanki ki kulamin kanki ki tsaremin kanki nabaki Amanar kanki please baby,

"Karka damu ai bazaka dade ba zaka dawo muyi Rayuwar mu tare insha Allah, "pray for me yafada tareda shafo fuskar ta tare sukayi salla ta kawo mai Abin cin yaci sosai itadai fresh milk kawai ta iya sha hankalinta na gida
Saida yayi brush ita kuma ta wanke kayan da tabata kafin ta fito ya shirya cikin kanan kaya yay I matukar kyau yana zabga kamshi suka fito shiya bude mata ta shiga kafin ya rufe ya zagayo ya tayar da motar gaba daya jikin shi yayi sanyi bayason ya mayarda ita saiso su kwana tare Amma yasan bazata soba baya son ya bata mata rai don ta faran ta mishi,

Har suka isa kofar gidan bai iya ce mata komai ba saidai yana driving cikin kwarewa yana d'an waigota a hankali yana kallon ta ita ma dai hakan ne a wurin ta har ya tsaya ta bude motar zata fito ya rikota gam "sauri kikeyi kin gaji dani ko? "Aa banason A gane naje wurin Kane za aga rashin kunya ta "inaso kizama kalar mijinki ki cire kunya idan har ba Aikin sabo zakiyi ba, you are my wife don haka ba wani kunya tsakanin mu koda anganmu ba komai,
Shiru yayi nadan lokaci kafin ya ce "um hope kayan da suka kawo sunyi miki? "Sosai har sunyi yawa ma fa baba yayi fada moto biyu fa kuma ka karo, "uhm ni banida lokacin hawa motocina sai na soja ko na siya bana hawa kinga yanzu inada iyali sai insiya musu Kala Kala su hau idan kinga wata ma kina so just tell me sai akawo miki,

"Dashboard ya bude ya ciro ATM ya saka mata a hannun ta "kirika sa mai a moto gobe za akawo miki kayan Amfanin da kike bukata naci if anything needed just used this and buy ya fada tareda janyo wata ledar a bayan motar "I forget to gave you this, ya mika mata ledar na siya mana waya iri daya idan kin shiga ciki kisaka sim a ciki nayi mata caji cire kwalin wayar tayi ta zuba mai ido wayar da tagani a TV tana burgeta galaxy 20 20, rungume shi tayi tareda godiya, "meye haka don nayima mata na Abu take mun godiya? "Uhm ita matar Ajiya tabawa mijin da bazata gode mai ba? "That's my duty my wife to make you happy banason matata ta rasa komai koda kudina zasu kare kuwa,

"Allah yakara budi, ta fada, Amen wifey, bazan samu shigowa ba but zamuyi waya idan nakoma gida kisa sim din zanje wurin hajiya idan nadawo zamuyi waya, tace "tom kafin ta juya zata fita, ya kuma fisgota bakinsu ya hade nadan lokaci kafin ya saketa yana fesarda numfashi "Sory na zama mayenki bana koshi dake yanzu haka inajin kamar in koma irin dazu you are sweet baby, dariya tayi ta bude motar tana daga mai hannu, yace "wait, daukar ATM din yayi da ta barmai that means bazata dauka ba, "saida ya matsa kusa da ita ya d'an ka mata a hannun ta "yanzu ba da bane ke matata ce you have right over my everything don haka feel free kiyi Amfani da komai nawa, "naga ba Abinda zanyi da kudine what if na kwashe maka kudin ka duka ina fa kashe kudi? Ta fada cikeda tsokana, dariya yayi "oh zaki iya cinye kudin ciki ok "I will see that my current Account hhhh yayi baby idan kika cinye duka inaso inga kinyi kiba kuwa kafin indawo,

Saida ta shige gidan yabi bayanta da kallo kafin ya fada motar ya tafi cikeda jin kewar rabuwa da ita ta mugun lasa mai Zuma mai zaki ta tafi ta barshi da tand'e baki, koda ta shiga gidan gaban ta ya fadi ganin yanda suke baje a tsakar gidan sunata hira, yasa ta dukar da kanta gani ba Aunty maryam da Alama itama ta kama kanta, "yanzu don iskanci yanzu kike dawowa gida Yasmin? Mama ta fara fada "yawon da bakiyi da bakida Aure ba shi zaki tsiri yi yanzu da igiyar Aurenki yanzu da mijin ki yazo nemanki fa me zamuce mai? Ajiyar zuciya ta sauke jin ba agano taba, mama hindatu tace "ya isa yaya Saude tunda gyara taje yi kuma maryam ta fada miki gidan kawarta ne meye na fada,

Hakuri kawai ta bayar ta shige dakin ta saida ta tube kayan jikinta tasa rigar bacci mara hannu Mai silbi batareda ta sa komai ba don zafi takeji, ta dora zani tareda sako hijabi ta fito, gefen mama hindatu ta zauna tace "mama meye akwai yunwa nakeji sosai, "akwai shinkafa da miya kuma tuwo miyar taushe, ya mutsa fuska tayi bataji Abinda take son ciba kitchen din ta wuce ta samu fulawa ta kwaba ta soya wainar fulawa da taji su tarugu da Albasa ta dakko yajin tafarnuwar mama ta zuba ta dakko plate din ta wuce dakinta ta ajiye ta koma dakin mama ta dakko zobo mai sanyi da yaji Abarba dasu cucumber ta koma dakinta ta, saida ta hada wayar da ya kawo mata ta kunna, kamar jira yake kuwa taji ringing, ganin video call ne yake kiranta yasa ta dauka tana dariya tareda janyo plate dinta,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.