Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel
Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt
Chapter 7 of 86
Fisge hannun ta tayi cikin fushi tareda matsawa kadan " bana son irin haka fa shiyasa naki kula samarin yanzun nan kai ma zamu bata idan ka kuma irin haka,
"Oh gimbiya sai kace rainon kyauye? Keda nake ganin ki a waye ''ba irin wannan waye war nayi ba don haka saida safe,
Ta juya cike da takaicin rike mata hannu da yayi d'an iska gobe zan cika aiki na in watsar da kai shege,
Kiran ta yake tayi amma ko juyowa batayi ba tayi shigewar ta gida,
Muhammad kuwa tun lokacin da ya haska fuskar ta yaga irin dariyar da takeyi yaji zuciyar shi tayi mai baki ya miki tareda dunkule hannun shi kamar zai daki mutum
Ganin ya riko hannun ta ai tuni ya wuce cikin gidan don ji yayi jinin shi na harbawa kamar zai tsiyaye a jinin shi,
Daga karshe wurin motsa jikin shi ya nufa yafara daga wani heavyweight da ko za a hada mu mu goma baza mu iya daga shi ba,
Saida ya hada gumi kamar w'anda ya fito filin daga ya mike tareda daukar ruwa mai sanyi ya sheka wa kanshi,
Towel ya d'auka ya fara tsane jikin shi dake tsiyaya kafin ya wurgar a zafafe ya jefar ya nufi bathroom ya sakarwa kanshi shower batareda ya cire gajeran wandon jikin shi ba,
Saida ya dauki lokaci mai tsawo a tsakiyar ruwan kafin ya fito daure da towel ya fada gado, bai taba tsintar zuciyar shi so restless ba irin yau meke damun shi ?
Ya rasa me yasa shi jin yanayin da yake ciki kodan sunyi fada ne da zuby? Runtse idon shi yayi gam tareda dunkule Hannayen shi yana maida numfashi mai zafi ji yake kanshi na juya wa,
Jin ankwanta a bayan shi yasa shi saurin zabura ya juyo domin ganin wace shegiyar ce ta isa da har ta shigo mai gida batareda ya kirata ba kuma for that matter har bedroom dinshi,
Ganin fuskar zuby yasa ya d'an yi cool dwan ya maida wukar fadan komawa jikin shi tayi tareda sa mai kuka ,
"Me yasa zaka hora ni haka Muhammad ? Kasan ina matukar kaunar ka me yasa zaka yimun haka ? Na tanbayi Ahmed yace mun kanwar shi ce ba Matar ka ba ce Am sorry baby for what I did,
" a jiyar zuciya ya sauke tareda cireta a jikin shi yace "is ok kinsan banason raini ai " riko hanun shi tayi masu burgeta saboda wasu jijiyoyi da suka shata ko ina kana gani kasan na karfi ne tareda motsa jiki,
Kallon shi takeyi wani iri Kamar hoto domin ba haka yake ba ya canja "meke damun ka Muhammad dina? " waya bata baka rai ? Nasan Muhammad din zubaida ba haka yake ba why the sudden change?
"Ni ba wani canji ke ke ganin haka, " ok ya isa ni dai hakuri nazo bayar wa don haka let me take a bath and come you no I really miss you ta fada tana daga gira,
Saurin tsayar da ita yayi "no need ki koma gida bana bukatar komai sai hutu yau please no aguement,
Sanin hali yasa taja ta tsaya tareda zuba mai ido kafin ta dauki key din motar ta ta fita kawai kafin ya kuma hawa,
Runtse idanun shi yayi gam yarasa meke damun shi ji yake kamar ya mike ya dawo da zuby amma ina yasan zataso ya taba ta shi kuma yagaji da wahalar da jikin shi batareda ya samu Abin da yakeso ba,
" wai haka ne matan suke? To meye zaisa yayi Aure tunda shidai har yau baiji wani Abin da zaisa yace zaiyi Aure ba, sex food what ?
Shidai yasan ko mace goma yakeso a rana zai samu but meye dadi a cikin su duk Abin daya ne shi har yau bai samu ruwan da zai kashe mai kishi ba har yau gobarar cikin shi na ci
Shi mace ma duk wadda ya taba bayajin wani feelings he is just using them to reduced the fluid
__________
Umar ya kirata yafi sau goma taki dagawa Shikuwa a halin yanzu baijin zai iya hakura da ita har dai da yaji irin taushin dake jikin ta yasha cudanya da mata Amma ita da ban ce shi gaba daya ma ya canja akalar zuciyar daga samun biyan bukata zuwa mallakar ta gaba daya Auren ta zaiyi kawai,
A ranar Sam Matar shi bata gane mai ba domin ya mugun daure mata fuska karshe ma ko makwanci yaki hada wa da ita,
Falo ya dawo sai faman text yake turawa Yasmin na lallashi Amma ina tama yi nisa ita a bacci tareda ku durin cin uban maman Amla da safe,
Tana tashi da sakon nin shi tayi karo dariyar mugunta tayi mai kafin ta tura mai msg
_Zamu hadu kafin kaje aiki by_
Ta fara taya y'ar uwar ta aiki tana cike da nishadi w'anda saida Maryam tayi magana "Yasmin me ke faruwa? Nifa ban gane miki ba Sam '
" bakomai Aunty na kawai naji dad'in wannan ziyarar da na kawo muku ne jina nake cikin farin ciki tun zuwa na, Hmm kawai Maryam tace kafin tace....
"Allah yasa ba wani Abun kike hadawa ba , Ameen ta Amsa saida suka kammala Aikin gidan ta fada wanka shirya wa tayi cikin wata riga da wandon Pakistan purple wandon fari tayi matukar yin kyau ta gyara gashin ta mai tsawo tareda dunkule shi gyale fari d'an karami ta yafa ta fesa turare ta fito,
Wani sheki takeyi ga kayan sunyi matukar karbar ta rigar ta d'an kamata ta West ga wandon pencil silipas ts sanya masu d'an tudu ta dauki wayar ta ta kirashi,
A lokacin zaune yake Matar shi sai zuba take amma hankalin shi na kan wayar shi duk da yayi late Amma Bazai taba tafiya bai ganta ba,,
Motoci tagani a kofar katon gate din a Jere hilux biyu da kuma wata Benz Army colour a tsakiya sojoji ne a tsaye da bindi gogi kamar zasu ci babu dauke kanta tayi duk da taji tsoro saida ta kusa kofar gidan na Umar ta kirashi " ka fito ina waje,
Wani irib zabura yayi kamar wani maye ya fito batareda yako kalli Matar shi ba jikin shi na rawa , meke damun Baban Amla ne wai ta fada tareda biyo bayan shi,
Lokacin har ya karaso kusa da ita kamar zai rungumo ta "gimbiya kin sani cikin wani hali wallahi na horu da yawa a Gaskiya kin gama tafiya da zuciyar Umar,
Murmushi tayi na mugunta domin hankalin ta na kofar gidan nashi kuma ta hango Matar shi tsaye ta dora hannu akai hawaye na zuba,
Karaso wa tayi kamar guguwa ta matso " Amma Allah ya isa tsakani na dake wallahi karuwa kawai masu shigowa bariki domin kwace mazan mutane a haka zaku kare tsinan nu,
Wani irin tsawa ya buga mata tareda yi mata tsatstsauran gargadi "hauwa ki wuce kafin yanzu in canja Shawara akan ki wallahi,
Tasan halin shi dole ta wuce cikin gidan tana kuka kafin ya nad'a mata na jaki tana wucewa Yasmin ta juya zata tafi domin burin ta ya cika tasan yanzu can ta matse musu ko ya lallashi Matar shi ko yayi biyu babu,
Shan gaban ta yayi jikin shi na rawa " Yasmin please kiyi hakuri zan ja mata kunne k'arki tafi ki barni cikin damuwa,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.