Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel
Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt
Chapter 58 of 86
Wata irin zabura yayi tareda mikewa tsaye ya zubawa Yasmin ido "what? Ciki' ya fada tareda zama yana kara janyota jikin shi "tell me baby ciki gareki? Duk ya rude ya gigice "ciki Aunty ciki takeda shi cikina? Am going to be a father,,? Tasan zaiyi farin ciki Amma bata tama tunanin farin cikin shi zai kai har haka ba, ya manta da Aunty maryam tuni ya rungume ta tareda Dora hannun shi a marar ta cikin kidima "Tnk you baby tank you tank you Wasu irin hawayen farin ciki ya ke fitarwa ya zabura cikin rashin Abinyi ya saka hannun shi cikin wandon shi ya zaro duk kudin ciki ya zubewa Aunty maryam a kasa Aunty kiyi manage zan kuma ganin ki idan na natsu,
Aunty Abin ya mugun burgeta irin wannan farin ciki sai kace akan shi aka fara haihuwa, zama yayi tareda rungume ta gam "baby me zakici? Kici Abinci baby na ya yi kiba "oh zaki wahala inya yi girma sosai wurin fita please me zaki ci tell me Aunty kibata Abinci don Allah karta yi aiki ko kadan karta wahala, to Abu yazo wurin masuyi fa, inji Aunty, wayar shi ya ciro yafara shedawa hajiya, "mama na Yasmin nada ciki zaki samu jikan da kike ta Addu ar samu a wurina mama zan zama baba, "to sarkin Y'an rashin kunya ina fatan ba gaban surukan naka kake tabargaza ba? Sosa keya yayi tareda kallon Aunty maryam yace "Aunty maryam ce kawai hajiya, to tunda ciki yasamu sai ta tare karta haihu a gidan su KO kuma ta dawo gidana sashen ka da zama, "zanzo muyi maganar yanzu,
Ajiye wayar yayi bayan ya gama kiran sauran Y'an Uwan shi suna mai tsiya, hajiya dai tafi kowa farin ciki d'an baban ta Alhmdulillah Allah ya kawoshi lfy, Aunty dai kama kafarta tayi ta fice tareda mijinta, suka nufi gidan su don Oga yace shifa yau yana gefen Yasmin zasuyi raino, mama dai ta rufawa kanta Asiri ta yi zamanta dakinta Amma bata tsira ba ya bita tareda sallama ta fito yace "mama baby ciki takeda shi zan zama baba don Allah mama ki kulamin da ita zanje inga hajiya indawo bataci Abinci ba gashi Aunty maryam ta tafi barracks da Ahmad nace mutafi tare taki yarda muje mama kisa mata ido karta yi aiki,
Ikon Allah mai karfi na bara, yau tana ganin ruwan rashin ta ido Allah dai yasa malam baya gida da Yau zatasha mitar surukinta baida kunya duk da yau ta shaida haka ya gama sanbatun shi ya fita bayan ya koma ya gama bata warning, "karki wahalar min da baby please ki jira bazan dade ba zandawo me kikeso inkawo miki? Shiru tayi kawai don ya gama bata kunya don tanajin yanda yake sakin layi gaban mama, saida ya bude shaffen cikinta ya bata kiss tareda cewa "baby yaushe zai girma cikinki yai kato? Itadai ya isheta wallahi ranta ma ya fara baci don ita yama daina damuwa da ita tun ba aje ko ina ba soyayyar ta koma kan cikin da ko kosawa baiyi ba, daure fuskar ta tayi tamau ya zauna "come on baby please karki sa damuwa ki cutar min da ciki please, "katafi don Allah kaina zaiyi ciwo tafada cikeda kufula, "ok ok sorry bari inje sai nadawo ya tashi ya fita,
Dawowa yayi "aramin key din motarki Ahmad ya tafi da tawa, Nuna mai Jakarta tayi ya bude tareda yin dariya ganin agwaluma a ciki, "mai ciki an fara kwalama, tayi mai banza ya dauka ya tafi cikeda wani irin farin ciki gaba daya ya manta da wata Abu wai sha awa farin cikin da yake ciki tuni ya mantar da shi wannan shafin,
Gidan su ya wuce kawai, a can suka gama tattauna komai kafin ya dawo bayan hajiya ta bashi sakon danbun naman kaza mai yawa da kuma soyayyun kajin ya kawo ma Yasmin din, saida ya biya bakin dogo ya jido mata su lemo dasu kankana da duk kayan da yasan zasu kara mata kuzari da lafiyar jiki ya iso da kaya Niki Niki,
Lokacin baba ya dawo ya fara tanbayar ina Auwal yau baiyi mai Oyoyo ba, "ai yabi uban shi suntafi BARIKI, baba yayi dariya "to sun shigo kenan? Don yasan dole tare zasu zo da uban gayyar, ina ita yasmin din take? "Tana ciki inaga bacci takeyi tunda an hanata motsi saboda kar d'an so ya wahala, "bangane ba wane irin Dan so ina d'an yake? "Au kai fa bakasan zaka samu jikaba tom ciki take dashi kuma tun muna gani da idanun mu ka bashi matar shi su tare bazan iya shirgin rashin kunya ba, "tofa ciki to bari yazo ya kwasheta su tafi tunda haka suka zabi nasu Auren ya kasance gashi mamuda ya kama ya kashe mata kudi kamar ita kadai ce ya, "ya kuma rage tsakanin ku yanzu, suna maganar ya iso,
Cikin girma suka gaisa da baba ya mai fatan Alkhairi tareda Addu ar Allah ya kara tsaresu yace Amen, "Amm tom sai ku shirya tarewa zuwa jibi zan kira uwarta suzo sai a gyara mata gidan ta ko, "ai baba ba wani Abu da za a saka a gidan na gama sa komai kuma gidana zamu zauna saina dawo zamu zauna tare a BARIKI Amma yanzu Unguwar rimi zamu tare, "yanda duk kuka tsara Abinku ba damuwa matarka ce Amma maganar kaya ku nemi inda za a zubasu baza a yi hasarar dukiya ba tunda anriga anyi hasarar dukiya an siya, toh baba mungode Allah ya kara girma da Arziki, Amen yace tareda yimai fatan Alkhairi a Rayuwar su da kuma rokon Allah yakara karesu,
Baccin ta taci sosai ta koshi bayan taci d'an waken da mama ta jefa mata da yaji cucumber da kayan miya harda dafaffen kwai taci sosai tasha magani shiyasa ta more idonta ga Kasan zuciyar ta tana farin cikin ganin farin cikin zuciyar ta mijin ta Abin Alfaharin ta, wani Annuri fuskarta ke fitarwa, jin ana shafa cikinta harzuwa saman kirjin ta ta bude idonta a hankali ta sauke akan kyakkyawar fuskar shi, "Sory for waking you up ina gaisawa da lovely daughter na ne "Kasan mace ma zan haifa kenan? "Insha Allah zaki haifamin baby girl mai kama dake baby da suma irin taki, tashi tayi tareda zuba mai ido "wai Zuma ta ko kewata bakayi kana zuwa ta cikin ka kakeyi ko, ta fada tana tura baki cikin shagwaba, "oh no ni na isa baby wallahi ke Kinsan ina sonki fiyeda komai a duniyar nan kuma wannan cikin yafada yana dora hannun shi saman cikinta bansan yanda zankwatan tamiki yanda nakejiba, wallahi bazan so ko guda ya sauka akanshi ba I love you so much dole inso duk abinda yafito a jikin ki,
"Saboda farin cikin samun wannan babyn ko Abinda ya kawoni banyi ba don banason in wahalar dashi, harara ta balla mai "oh duk saboda babyn ka harda jarabar ta ragu? Kai naji dadi kuwa Allah yasa har sai na haihu, "what? Hmm jibi zaki tare baby don haka ba wani sauri da zanyi duk da ina matse farin cikin da kika bani ya rage min komai, shiru kawai tayi ta zuba mai ido don ta lura ya zauce akan wannan d'an tayin cikin, "baby gobe zamuje muyi wa baby shopping ko? "Wai me yasa kadawo ne ba yanzu katafi ba, ai Inba bani iyali na akayiba yanzu kika fara gani na a nan gidan, shigewa yayi jikinta tareda cusa hannun shi ta Kasan rigarta ya fara lalubarta a hankali, ta riko hannayen shi "meye haka zaka wahalarda baby fa, "oh come on ba wani Abu zanyi ba just play kwantar da ita yayi tareda hade bakinsu wuri daya yafara bata wani irin salon da bazata taba iya kawarda kanta. Ba,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.