Complete Hausa Novels

Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel

Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt

Chapter 33 of 86

"Yaya mubi a hankali muji komai a natse don ni koda yaron nan ke magana bangane komai ba, "toh mamuda idan banbi a hankali ba garaje zanyi?

"Yo ko zafi nayi ina zai kaini kana ganin y'anda ya zagaye mana unguwa kamar masu laifi kaduba ma kota har a katanga suna leko mu irin wannan bala I har ina?

"Mama na Meye wanna ina kikeso ki jefa mu shikuma wanna don girman Allah ina kika tsinto shi? Abarikin? Ku Kuma haka Zaku kare a jajubo mana masifa ita maryam ta makale tace sai soja kema ji me kika kwaso,

"Mamuda daga gani wannan yaron bazaiyi mutunci ba, don haka ka dauketa kawai ku wuce zango idan andaura Aure Sa dawo da mijinta

'Yaya ai wanna ba shawara mai kyau bace ai ko birnin sin zamuje banjin wannan yaro bazai biyomu ba Kuma ai nida natafi da ita ni kwabata zatayi ruwa,

"Kai samaila dama kanada zainabu sai ka hakura kawai da mama na, "Aa mamuda banson Abinda kakeyi meyasa kakeson rabashi da y'ar uwar shi?

Tashi kawai baban Zango yayi ya saba malum malum tareda gyara zaman hula" toh nidai nafada muku inkuma dai nine waliyin Yasmin to ban daura mata Aure da kowa sai in wanna sojan yazo yace ya fasa zancen Auren ta don haka ni nayi gida Saude Allah bamu Alkhairi,

Ya wuce kawai batareda karawa waigowa ba, baba zuba mata ido kawai yayi kafin yace "tashi ki wuce ai ke kanki kinzama Abin tsoro Fatima Kuma nasan komai da sanin maryam zamu gauraya da ita,

Ciki ta wuce tarasa me ke mata dad'i tarasa madafa tarasa ina zata tsoma ranta tana hango bacin randa ya tafi dashi ya mugun tsaya mata a rai,

*****************
Bayan ya tashi aiki ya nufi gidan su dama Hajiya tasan da zuwan shi don haka ta shirya mai dish Kala Kala da kanta ta jera mai a dadduma ya iso da tawagar shi kamar gwamna,

Saida ya koshi ya fara bata hakurin rashin zuwan shi da wuri, "aa bakomai nasan aiki ne ya rikeka, riko hannun ta yayi cikin damuwa,

"Akwai magana kenan yau don nasan ka tun kana yaro daka rikeni hakan akwai babbar magana, "eh mama akwai, ina cikin damuwa , narasa mafita bansan yazanyi ba,?

"Tell me what to do kaina ya kulle, "kayimin bayani badai matsalar wurin aiki bace ko? "Akan yarinyar da nakeso ne, ya fara yimata bayanin komai akan YASMIN, Amma banda zancen Auren ta ya boye wannan,

Hamdala tafarayi kafin tace kai nagodewa Allah yau kaine ke zancen Aure? Lallai wannan yarinya ta ciri tuta Ashe soyayya ta da ita akwai Abinda Allah yaboye,

Kai nayi farin ciki sosai baba na Allah yasa rabonka ce, ya Amsa da Amen, yaushe zakuje nema min Auren ta?

"Banson garaje Ai gobe zankira kannin mahaifinka sai muyi magana inyaso sai mu tsara komai,

"Don Allah kar ya wuce jibi zuwan su 'ya ciro ATM ya mika mata gashi asiya komai da ake bukatar kaiwa akwai kudi sosai a ciki zasukai 2milion idan basu isa ba kifadamin inturo muku Wasu,

Sakin baki kawai Hajiya tayi tareda mamakin d'an nata yau ba mafarki takeyi ba kuwa? Muhammad ke son Aure kuma cikin sauri haka? Lallai mahakurci mawadaci

Allah ya ma wannan yarinya Albarka ita kam koda Asiri YASMIN tayima MA tana farin ciki da hakan kuma sai takara mata kudi takaiwa malamin,

Ma kuwa a gidan ya yi wanka ya shirya domin yanada daki na musamman, ya sallami yaranshi kafin ya fito cikin shigar manyan kaya shadda ce fara kar ya murza hula kamar wani sabon Ango ya fito yana zabga kamshi fadin haduwar da yayi bata bakine,

Waya ya dauka yakira tareda bada umarni kai tsaye,
"Mu hadu a Unguwar Dosa da wannan motar harma da kayan cikin duka,

Ya fita Hajiya nakara godewa Allah da Yau take ganin irin wannan farin ciki,

***************
Yasmin dai yau a daki ta wuni bayan tafiyar ismail , ya gama yi mata bori ko kallon shi batayi ba kuma tasan da bai bullo da zancen Auren Zainab ba bazata taba yimai hakan ba,

Yama raina mata hankali Wallahi kuma ta shirya ko baba zai Yanka ta bazata taba y'arda da Auren shi ba,

Baba kuwa yakasa cewa komai ya zubawa sarautar Allah ido yaga ta ina wannan rikici zai kare?

Karfe takwas na dare YASMIN ta samu tsalki ta sheko wanka tareda yin Alwala ta shiga dakinta ta shirya kanta tsab cikin wata rigar baccin ta guntuwa dai dai guiwa tareda daura zani ta Dora hijabi tareda tada salla,

Tana sallamewa baba ya kirata falon su ' ta zauna kamar wadda tayiwa sarki karya gefe guda tareda dukar da kanta,

"Mama na kimun bayani ina sauraren ki " me kikeso ki fadamin? Kema bazaki Auri d'an uwanki ba kike nufi? Dake da y'ar uwarki kun gama watsa min tsarina baki daya ko,

"Haba malam yakamata ka barwa Allah wannan lamari ita maryam da kake magana Ina zamukai wa innan rabon kana ganin cikin shekara biyu Yara biyu ai sai mu yarda da yin ubangiji,

"Haka ne saudatu yanzu kina so ki fadamin bansan Allah keyin komai ba kome? "Toto yanzu nasan komai ma da sanin ki sukeyi tunda ba danginki bane shiyasa kike zuge ya'yan ki su ki Auren shi ko?

"Haba malam ya zaka fadi haka bayan kasan irin y'anda na reni ismail da hannu na kamar ni na haifeshi bai dace wannan kalma tafito daga bakinka ba,

Toh kusani keda Yasmin indai nine mahaifin ta to bazata taba Auren wannan yaron mara tarbiya ba, ya mike fuu ya fita,

YASMIN tashiga tashin hankali najin yau saboda ita iyayen ta na misayar yawu, abinda bata taba jiba tsawon rayuwar su,
Kuka taji ya kwace mata mama ta kalleta,

"Toh Allah ya biyaku ya'yan Albarka Wato dai kullum sai kunja mun magana idan zancen Auren ku yataso haka y'ar uwarki tayi kema gashi Abu yazo gab shine kika bullo da naki iya she gen,

"Kuyi kokari Kuyi Auren ku inda kukeso ni kuma sai ku kashe min nawa kunji nagode muku, itama maryam yanzu zankirata inji don nasan da sanin ta komai ya faru,

Kukan tane ya Kara sauti tareda girgiza kai cikin Kuka" mama don Allah kiyi hakuri Wallahi ni ban turoshi ba kuma Aunty batasan komai akai ba, ni wallahi na yarda da Auren ya'yan karkuyi fada akaina don Allah,

.
"Tashi kije ni nagama magana kuma, tashi tayi kamar wadda kwai yafashe mata ta nufi dakinta,

Baba na fita yaci karo da motoci sababbi dal a kofar gidan daya fara sai kuma ja y'ar Kara ma mai shegen kyau kirar Volvo sabuwar fitowa ya tsaya cak tareda makakin ko suwaye a ciki,

Fitowa MA yayi daga cikin farar ga kayan jikin shi farare yayi mugun haduwa ga kwarjini da haiba da ya cika ko Ina, baba bai gane shiba saida ya matso tareda mika Mai hannu,

"Salamu alaikum baba barka da dare' baba ya Amsa cikeda ganin girman yaron yace wa kake nema yaro?

"YASMIN nine dazu nazo da safe "toto nagane soja ko? "Eh baba sunana Muhammad Abdullah, to Sannu muhammadu bismillah shigo,

Tana kwance ta Dora wayar ta saman kirjinta tana tunanin rashin kiranta da yayi yau kardai fushi yakeyi da ita?

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.