Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel
Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt
Chapter 22 of 86
Wani irin murmushin takaici tayi tareda ja baya yau Ina ganin iskanci, "saboda kai waye a wurina da zaka sanya min doka da kuma IkO?
"Nine nafi Kowa isa da iko akanki nafi Kowa right akanki I felt like tun tuni kina tare da rayuwa ta na Kasa sukuni saboda ke bansan meke damu na ba Aure baya cikin tsari na haka ajiye mace daya tal ba ra ayina bane tunfarko amma saboda ke inajin zan iya killace ki ke daya zan iya rayuwa dake kekadai,
("Give me chance) kibani dama I will give you everything idan kuma kin bijire zan gwada karfina don haka zabi ya rage nake,
"Go Ahead ubana Allah ya fika kuma zai kareni daga duk kan sharrin ka yanzu Dan iskancin ka ya rik'a duk karuwan ka sun yima kadan sai ni?
"Bana ra ayin kowace mace sai ke kuma iskancin da kike fada akanki zaifara da wasa nakeyi ba BARIKI ba akanki zanfara BARIKI kisa ido,
"Meye sunan ki na gaskiya? "Ka shafa kaji ta fada tana murguda mai baki harda doguwar tsuka, saidai kafin takai karshe tuni ta tsinto hannun shi a saman kirjinta yana shafa fatar dake waje, wani irin buge mai hannu tayi kafin ta sanya mai kuka,
"Allah zai sakamun kuma sai anyiwa naka kaji inda dad'i, runtse idanun shi yayi yanajin wani irin feelings da ya jangwalowa kanshi,
"Baby ki daina yiwa yaranki baki, "Allah ya sauwake Wallahi ko a mafarki nayi ciki akace nakane sai na zubarda shi kafin in farka,
"Ni kuma ko a mafarki naga likitan da yamun asarar cikin jikin ki sai na dauke kanshi da bindiga muje zuwa,
"Don darajar iyayenka kabani hijabina intafi gida, ba musu ya mika mata ta ce ka bude min kofar,
Tayar da motar kawai yayi "ki fada min gidanku ko in wuce dake gidana daga yau afara zaman dama a matse nake,
Ba musu ta fada mai tana Adduar neman tsari ga wannan mugun bawa a hankali yake driving kamar kar yakai yakeji yanajin D'ad'in moment din wani irin nishadi yakeji,
"Da ma zanje wurin hajiyata intanbaye ta gidan ku kinga Allah naso na naganki cikin sauki batareda bata lokaci ba har Zaki kaini da kanki,
"Zaka gani d'an iska inzan kaika gidan mu,
Ganin ya nufi Unguwar Dosa yasa gaban ta ya mugun faduwa kardai yasan gidan nasu?
"Ina ne layin naku yake? Wani gida ta nuna mai gaba kadan d'an karami ya faka tareda cewa kije tom sai anjima yayi saurin jan motar ya bar wurin saida taga andauki lokaci tafara takawa rike da jakar ta domin karasa wa gidan su,
Saida taje gab da shiga gidan taji yace "ki kulamin da kanki baby bye, ya fada cike da dariyar mugunta wani irin zabura tayi ya shige da gudu gidan, yau Allah ya hada ta da tsinanne,
Juyawa yayi ya nufi inda ya bar motarshi cike da farin ciki ya fada tareda bata wuta ya bar Unguwar duk inda ya bulla ansan wannan wani ne domin motar da kawai yake ciki sheda ce,
***************
Cikin farin ciki ya kwana yau yana juyi a gado yana tuna dramar su da ita wayar shi ya janyo tareda duba lokaci yaga kusan karfe daya na dare gashi Sam bacci ya Kasa daukar shi,
A nan ya tuna da barnar da yayi ja fasa mata waya dafe goshin shi yayi "oh god ya furta kafin ya diro Kasa alwala ya yo ya Tada sallar nafila ganin bacci bazai samu ba,
YASMIN ma hakan take takasa bacci tana mai tunanin karonta da M.A
Wani irin yam takeji a jikinta tunawa da y'anda lallausan hannun shi ya shafo saman kirjinta ta shafa wurin jitake kamar a lokacin ne yake shafawar,
"Kyan d'an maciji zuciya fal zunubi, ta fada tareda runtse idanun ta,
*************
Shirye take cikin uniform dinta farare ta rata ya bakar Jakarta ta yayi mai kyau ta fito saida ta leka dakin iyayen nata ta gaida su baban ta ya ce "Auta har kinfito?
"Eh tace to ungo kudin motar ki idan kuntashi ya mika Maya 2k tayi godiya tareda fita cikin fargaba,
Yaya ismail ta samu zaune a cikin mota yana jiranta,
Ta gaishe shi yana fara a ya Amsa "lfy queen of beauty, Ina kika ajiye wayar ki?
"ta lalace ne jiya ta samu kanta da boye mai gaskiyar lamarin,
Tundaga kofar gate din shiga makarantar tasu ta hango sojoji birjik ta ko Ina gabanta ya fadi ras tuni jikinta ya fara rawa don ita yanzu duk wani soja ma tsoro yake bata,
"Zaki sauka anan ki karasa kinga kofar gate din masu garin sun rufe sai nadawo daukarki, bata cikin natsuwarta haka ta fita kamar wadda kwai ya fashe mawa ta nufi gate din saida ta wuce ciki hankalinta ya kwanta,
M.A ne kwance a bayan motar dake tsakiya tun isowar ta idanun shi NA kanta saida ta shige ya basu umarnin wucewa dama saboda ita kawai ya tsaya a wurin don ya gama binciko tarihin ta kaf yasan rayuwar ta a cikin dabara ya nemi komai a wurin Ahmed batareda ya nuna mai wani Abu ba,
**************
Kusan sati daya kenan
Kullum sai ta samu motocin nan a kofar school dinsu kuma ta ankare da ta shige suke wucewa abinsu nan zuciyar ta taba ta d'an iskan nan ke bibiyar ta,
Yau tana dawowa school ta samu mama da maganar Aurenta, "mama baki kuma cewa komai ba akan magana ta da ya ismail?
Kallon ta tayi "oh ni zamani maganar Aure kikeyi mama na yau naga lokaci dariya tayi kawai batareda tayi ma mama wani bayani ba ,
Shigowar baba ne ya katse hirar ta gaidashi
Ya Amsa tareda cewa MAMAN Yara bakisan meke faruwa da Unguwar nan ba kwana biyu sojoji sai sintiri suke mana a kofar gida ni Abin ya fara bani tsoro ko suna tunanin akwai barayine a Unguwar?
Tashi kawai tayi tareda fita dakin cike da fargaba da kuma tsoro me MA yake nufi da bibiyar ta irin haka sai kace wata criminal gashi Yaya ismail yayi tafiya bare ta fada Mai gaskiya ta fara tsinkewa da lamarin MA,
Hijabinta tasa ta fita waje tareda zubawa motocin ido, zuge glass din motar yayi ya zuba mata idanu yana lafe kamar wani mara lfy ahankali ya bude motar ya fito ya jinginq a jikin motar,
Idanu ta zuba Mai sanye yake cikin kaki green yayi masifar kyau ba hula akanshi ya sha gyara kan fuskar shi shar da ita ga muscles din nan kamar su yaga hannun rigar su fito,
Jikinta na rawa ta karasa wurin shi tana Wai waye cike da tsoron kar baba ya fito ya karasa cikin sauri,
"Baby' ya fada cike da kasala ga yaranshi sai zagaye sukeyi dayan yayi saurin wucewa kofar gidan ya datse
"Don girman Allah ka rufamin asiri kabar Unguwar nan ka daina bibiya ta ka taimakeni ka kyaleni karka jefani a matsala,
"Ai ni kin jefani a matsala tunda kinki barina inyi aikina cikin natsuwa ' taurin kanki zaija inyi abinda ko makotanku sai sunji jiki,
"Me kakeso? Don Allah nidai kafada ka tafi ta fada tana waige "relaxed kulawarki nakeso ki rika bani kulawa,
"Nayarda please kudaina takurawa Al umma saboda ni kutafi "good for you ya fada tareda sanya hannu cikin motar ya ciro wata Leda a motar ya mika mata yace ga waya kina zuwa gida ki kunna duk ranar da nakira baki dauka ba akwai damuwa don bazakiji da dad'i ba,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.