Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel
Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt
Chapter 8 of 86
Tsayawa tayi cikin daure fuska "aini ban ma San kanada Aure ba da ban saurare ka tun farko ba kuma indai wannan ce Matar ka wallahi ban Auren ka don ba tun yau ts saba Zagina ba don haka ka kama kanka dani kafin in hada ka da yaya na,
" what is happening? Taji muryar Ahmed saurin juyawa tayi wurin shi "Yauwa ya Ahmed ka shiga tsakani na da wannan mutumin yasa min ido ka man iyaka dashi ko dole ne in soshi tayi shigewar ta cikin gidan batareda ta ko saurari Ahmed din ba,,
Muhammad da ya fito daga gidan shi har ya shiga cikin motar shi yaga duk Abin da ya faru yana hango su daga cikin motar har Fitowar Ahmed da wucewar ta ciki,
This girl is unbelievable meke damun ta ta hada shi da budurwar shi yanzu kuma miji da mata bayan sun gama shan soyayyar su,
Isowar Ahmed cikin motar yasa shi dawowa cikin dogon tunanin da yakeyi gaida shi yayi cikin respect irin nasu na sojoji sannan aka rufe motar suka kama hanya,
Sai bayan sun isa office ya kirashi office, " Ahmed meke faruwa ne dazu I saw everything me ka fadawa Umar? Me yake tsakanin su da sister ka?
"Oga wai yana sonta ne kuma yanzu tace ya fita hanyar ta ni ban gane me ke faruwa ba shima nace ya jirani har mu dawo gida Muyi magana domin nasan halin Yasmin,
" Yasmin'''' ya furta sunan can kasan zuciyar shi sunan ta Akwai dad'i sosai,
Ka fada mai karya kuma gangan cin zuwa gidanka tunda tace ya kyale ta ba a so dole don haka warn him before I do something about it
"Ok sir I will do so , ya sallame shi tareda maida bayan shi bayan kujera ya runtse idanun shi yana wani irin murmushi " what a woman Yarinyar nan me take nufi da rayuwar suda ta shigo bariki ?
*I don't no kuci gaba da biyo ni,"*
*UMMU AMMAR*
[8/30, 2:56 PM] Feenerh Wrtr: 🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
_*BARIKI*_
_Auren soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
_written by fenerh_
Maman Ammar
*Dedicated to*
Fiddousi mainasara
(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)
тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.
INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/
FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/
TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09
7&8
Maryam batasan wainar da ake toyawa ba saida Maman Amla ta zo gidan da kanta tana uban kuka,
Har kasa tasa guiwoyin ta tana rokon Maryam don Allah su bar mata mijin ta gaba daya yace idan bai samu Yasmin ba itama zata barmai gida,
Abin ya bama Aunty Maryam mamaki ganin ko a jikin Yasmin yasa tasan Akwai wata akasa tayi saurin kallon y'anda ta juya musu baya,
"Yasmin meke faruwa ? " AUNTY ki tanbaye ta ita data zo miki gida da kuka , kuma tasan banbacin karuwan gida dana bariki yau ba boka ba malam mujiya kwakwal war mijin mace idan tayi wasa kuma wallahi tayi gidan su,
Baki Maryam ta saki kafin ta lallashi Maman Amla ta tafi tareda kwantar mata da hankali bayan ta rakata "ki kyale Yasmin haka take kuma tanada wanda zata Aura d'an uwan mu ne kawai ta daga miki hankali ne,
Wani dadi taji tareda ba wa Aunty Maryam hakuri akan zagin ta datayi " kiyi hakuri Maman Auwal bazan kuma fitina dake ba insha Allahu,
Koda ta shigo gidan kasa ce mata komai tayi saidai idanu kawai don tasan halin y'ar kanwar tata idan ta matsa sai yanzu tace zatayi mata yaji gwara ta bari idan tayi niya zata fada mata da kanta,
*tushen labari*
2years back,
Tafe suke a kan hanyar su ta dawowa daga makaranta sanye suke a cikin fararen kaya da d'an karamin hijabi sai bakin low pass a lamar dai malaman jinya ne su
Kyawa wane su sosai duk da kana ganin su kasan yaya da k'anwa ne Amma Akwai shakuwa mai girma a tsakanin su
Saidai kanwar tafi yayar nesa ba kusa ba kuma kirar jikin su Akwai banbanci domin Maryam nada jiki kadan ita kuma Yasmin jikin ta d'an dai dai ne,
Zasuyi matukar burgeka idan kaga y'anda suke tafiyar su kamar wasu kawaye,
Motace tasha gaban su fara tas kirar Lexus sukayi saurin tsayawa cak,.
Fitowa yayi sanye cikin kakin shi yayi matukar yin kyau kanshi ba hula ya fara basu hakuri,
"Y'an mata Kuyi hakuri na tsayar da ku akan hanya, wani irin mugun kallo Yasmin ta watsa mai " kadai yi niyyar kashe mu Allah ne baiyi ba saboda ka ganka soja to Allah ya fika , ta furta tana mai murguda mai baki,
Saurin riko hannun ta Maryam tayi Alamar ya isa mana, dariya yayi ya kalli Maryam "kibawa kawar mu ko kanwar muce hakuri naga tanada tsiwa,
" kayi hakuri ba komai ta rikota suka kama hanya da niyar wucewa yayi saurin shan gaban su " don Allah meye sunan ki ? Ya fada yana kallon Maryam, ta fada mai kai tsaye yayi "suna mai daraja don Allah wane unguwa kuke ne yau nakai kwana uku ina ganin ku a dai dai nan hanyar kuma saboda ku nake biyo wa yau nakasa hakuri ne a yimin uzuri inzo gidan k....
...karma ka fara wallahi don Aunty nada mijin Aure ni kuwa ko maza sun kare ban Auren soja don haka bamu hanya ko inbangaje ka wallahi,
Finciko hannun Maryam tayi sukayi gida batareda ta kuma kallon inda yake ba, Maryam na wai wayen shi domin gayen ya matukar burgeta ga kakin ya karbeshi sosai,
Shiga motar shi yayi ya rika binsu har saida yaga gidan su ya koma barrack w'anda su kuma suna isa kofar gidan su sukaci karo da Ismail wato w'anda. Maryam din zata Aura,
Karo na farko da taji takaicin Amince was Auren da iyayen su keda burin hadawa,
Tasowa yayi yana musu barka da zuwa,
Yasmin ce tayi carab tace " ai wallahi ya sama'ila idan baka dakko mu sai anyi ma fashi a hanya wataran kaga wani mayen soja yau ya biyo ma mata,
Dariya yayi "kai Yasmin kin cika mita nasan meye matsalar ki daga yau na gama interview dina ni zanrika dakko ku insha Allah,
Maryam dai wuce wa tayi batare da ko gaishe shi ba, yasan halin ta na rashin son magana don haka bai cika damuwa da shariyar ta ba,
Karfe takwas na dare suna zaune a tsakar gidan nasu dai dai na rufin Asiri aka aiko ana kiran Maryam, saida gaban ta ya fadi ganin irin kallon da Baban ta yayi mata kuma suna matukar tsoron mahaifin nasu bayason wasa,
" Maryam waye kika bashi izinin zuwa gidana bayan kinsan kinada miji a kasa? "Wallahi baba bakowa, " to bari inga kowaye,
Yana fita Mama ta ce "Yasmin waye yazo wurin y'ar uwarki? " mama ni yazan San ko waye ? "Nasan tare kuke ai koma waye zaki sani,
" nidai bansan waye ba, "to ku kiyaye kafin ku hadu da fushin babanku Kunsan burin shi akan ku ita kuma tasan tanada mijin Aure don haka ta kiyaye,
Shiru kawai sukayi har Baban ya dawo ya ce wani soja ne wai sunan shi Ahmed ya mun bayanin wai yana son Maryam ne toh nabashi hakuri bayan nayi mai bayanin tanada mijin Aure,
Wani iri taji har cikin ranta zataso ace ta Auri wannan bawan Allah mai suna Ahmed ya tafi da ita lokaci daya gashi ita bamai iya magana bace,
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.