Complete Hausa Novels

Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel

Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt

Chapter 3 of 86

" she is very beautiful but psycho daga gani kyan ne kawai Amma batada hankali,

"Oga I forget wetin you sen......" You are mada Emanuel give me my money ' ya furta cike da jin haushi ya fada motar shi tareda kallon Ahmed "let go before I do something bad here,

Fadawa motar yayi tareda tayarwa domin shine zaija motar ogan na gefen shi yana matsa waya,

" wai me ka aikeshi ne ? "Forget that mad man, saida ya matso kusa da Yasmin ya d'an tsaya tareda sauke glass kadan,

Kanwata zan shiga gari me kike so?
Kawar da kanta tayi domin batason kallon fuskar wannan gayen ko kadan mai kama da Aljani,

" bakomai yaya na sai kadawo' "yau baza Asha ice cream din ba da two one two bread ? Dariya kawai tayi har hakoran ta suka bayyana tace bye tareda nufar gidan na y'ar uwar ta,

Domin Sam bata son ko minti daya tayi da wannan mutumin, saida sukayi nisa yace " kanwar kace wannan? "Eh sistan maman Auwal ce,

" Amma dai kamar itama kalar Emanuel din ce ko ? Dariya yayi tareda cewa "kawai tana son mutane ne kuma sun dade da sabawa dashi tun farkon zuwanta,

" Hmm kawai yace tareda ci gaba da d'anna wayar shi har suka isa lafiyayyar unguwar ta malali dake cikin garin na Kaduna

Bakin wani tafkeken gate ya yi horn mai gadi ya wangale mishi ya kutsa hancin katuwar jeep din, tasowa sojojin sukayi tareda Sara mai domin har mai gadin gidan soja ne,

Da kanshi ya bude motar ya fito tareda nufar cikin gidan da tundaga bakin kofa yake jiyo hayaniya, yana bude falon gaba daya suka koma wacce ta natsu kamar ruwa ya cinyesu,

Y'an matane guda uku a cikin falon sau wata dattijuwa bai cikar haiba da kamala faratas da ita tana Jan carbi sanye take da less lafiyayye dinkin buba,

Sallamar shi yasa Matar ta dago kanta domin ita Sam hankalin ta baya kan yaran zuciyar ta tay nisa sosai,

Washe bakin ta tayi wanda ya bayyanar da hakorin makkan dake gaban hakoranta guda biyu na gold suna sheki,

Saida ya zauna kusa da ita akasa kafin yace "ina wuni momy na? " lafiya lau yanzu nake son insa Fatima ta kiramin kai a waya danaji shiru,

"Gani nazo momy kema kinsan dole inzo inganki kullum sai dai idan da Akwai matsala ko aiki ya rikeni kuma ai Zanfada miki,

" ina wuni ya Muhammad, yan matan suka hada baki wurin fada ya waiga tareda zabga musu harara "dama zaman da kukeyi kenan saboda kusa jinin uwata ya hau sai haushi kukeyi kamar karnuka a cikin gida kowacce fuska kamar tayi dambe da toka kun tasa min ita a gaba kuna ta iface iface,

." banson dibar Albarka Muhammadu kai Bakayi Aure naga Matar ka ba bare insa ran jikoki ya'yan ka ba kila sai na mutu sannan yaran dake debe min kewa ka sasu agaba da kyara,

Dukan su wani irin bakin cikine ya rufesu wai duk kwalliyar da suka caba shine zai ce kamar sunyi danbe da toka lallai wannan gayen zasuga Matar Auren shi,

Tashi sukayi sum sum suka shige kafin ya kara labto musu wata bakar maganar, Shigowar Ahmed ne yasa momy tasaki fara'a "Amadu dama tare kuke?

" eh mama ina wuni? "Lafiya lau d'an Albarka ya iyali, ? Ina labarin y'ar Albarka Yasmin? " ai momy dazu kuwa tazo bariki tazo mana hutu,

"Ai yar nan nada hankali sai daya kawai da kukazo tayi mugun shiga zuciya ta, kallon Momyn nashi yayi kafin ya kalli Ahmed yace " who is Yasmin?

"Oga that my sister, tabe baki yayi kafin yace yaushe kukazo nan har momy ta ganta? Last time datazo ka aikoni lokacin zata tafi muka biyo nan kafin in sauke ta gida,

Shiru kawai yayi domin yasan halin Momyn shi idan taso mutum, " Muhammadu yaushe zanga Auren ka ? Idan Bakada zabine ni inmaka zabi kuma nasan zakayi farin ciki,

.

"Momy Muyi magana mai ma ana don Allah Mubar wannan, " oh wannan batada ma'sna kenan ? "Muhammadu idan lafiya ce Bakada ka fada min anemi magani shekarar ka talatin da bakwai yanzu kakusa arbain kullum ba wai yarinta kake karawa ba shekarun ka natafiya ne fa, Amadu ka fadawa Abokin ka ko mai gidanka zance ne oho domin nasan baida wani Abokin da zai iya fadawa matsalar shi sama dakai,

"In Akwai matsala kufada min, ta fada cike da damuwa aranta, saurin riko hannun ta yayi tareda rage murya a hankali,

" momy na kiyimin hakuri zanyi kok'arin yin hakan idan na shirya banason inyi Auren da zan shiga damuwa insa Kaina a matsala momy kitayani Addu'a kawai,

Tashi yayi tareda kallon Ahmed da idanun shi da sukayi ja saboda tausayin mahaifiyar tashi "muje ko dafatan bakwa bukatar komai?

Ya tanbaye ta Amma ido kawai ta zuba mai domin babbar bukatar ta itace Auren tilon d'an nata ta kuma ga jinin shi a duniya,

Yana fadawa motar ya jefar da wayar shi ya dafe goshin shi da yafara Sara mai Ahmed ya tayar da ita sai da suka tsaya bakin unguwar shanu sannan yace " oga Gasu nan fa sai ka zaba,

Daga jajayen idanun shi yayi ya zuba wurin matan dake Jere akan titi da shiga kamar Tsirara

Fita Ahmed yayi saida yayi ma wata magana tareda Ciro bandir din kudi ya bata ya dawo cikin motar "oga na yi making Arrangement din,

" ok muje mess ", ya fada kai tsaye suka wuce batareda sun tafi da ita ba,

Karfe kusan tara nadare suka dawo, kasan cewar lokacin zafine kusan mafi. Yawancin mutane kan fito waje domin shan iska duk da kuwa Akwai wutar lantarki ta ko ina ga A.c

Amma sanin kowane iskar ubangiji tafi kowace iskar bature ni ima tareda Amfani a jikin dan Adam,

Hirar su sukeyi irin ta y'an Uwa gefe data bowl ne dauke da chips Yasmin ta Ajiye agefen ta wandone ajikinta dogo mai fadi sosai da wata tea shirt mai guntun hannu ta kamata tsam kanta sanye da hular net kafar ta kuwa silipas ne sabo tayi matukar yin kyau sosai duk da bawai kwalliya tayi ba,

Amma she look very Adorable kamar ka sace ta ka gudu Babyn ta hadu sosai kamar y'ar Aljana ga kirjin nan cike tab da dukiyar Fulani daga kasa kuwa zakasan Allah yayi halitta a wurin nan mai daukar hankali,

Maryam ta kalle ta " Yasmin kije ki saka hijabi kinga yadda mijin maman Amla ya kasa shiga cikin gida tun dazu saboda ganin ki a nan kuma ga shigar dake jikin ki,

"Kyale tsinan ne Matar shi naciki tana jiran shi Amma ya tsaya kallo na Ayya kuwa sai na haukata shi,

" nidai ki rufamin Asiri kina ganin Matar nida ita saidai gaisuwa daga nesa saboda tsabar kishi tun zuwan ki na farko tazo nan tayi min magana "wai me yasa mukeson kawo kannin mu mata bariki neman maza?

" Kwal uba kika ce mata mene? "Hakuri na bata nace nidai ba neman miji kika zoyi ba zumunci ya kawoki tayi hakuri,

" ai wallahi sai nayi maganin ta Allah ya kai mu gobe bari ma kigani tun yanzu in dana tarko,

Mikewa tayi cikin salon daukar hankali har tana girgiza kirjin ta wanda suka yi d'an rawa kadan da saida numfashin shi yayi skipped sannan ta duk'a ta dauki bowl din chips din da takeci,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.