Complete Hausa Novels

Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel

Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt

Chapter 4 of 86

Ta kalli y'ar uwar ta "muje ciki Aunty ai munsha iska sosai ga boy na yayi bacci, baza mai duwai wukan ta tayi da gangan saida ta saka kafar ta cikin falon ta juyo tareda jefa mai blow kiss har da kashe mai ido daya cike da salon daukar magana

Ta fada cikin falon, kusan sumewa yayi a tsaye yakai hannun shi saitin wandon shi ya dafe saida ya dauki lokaci kafin ya daure fuska tamau ya shige cikin gidan nashi shima dauke da kudurin samun wannan Aljanar Yarinyar daga gani yar hannu ce,

Ita kuwa tana shiga ta kyal kyale da dariyar mugunta " ai zaki ga BARIKI maman Amla,

"Dariyar me kikeyi Yasmin? Ina fatan ba wani mugun Abin zaki kulla ba domin nasan halinki sarai dariyar ki ba Alkhairi bace,

" kai Aunty na ba komai kawai inajin nishad'i ne' "Hmmm Allah yasa, ta wuce masaukin ta wato dakin y'ar uwarta domin bin lafiyar gado saidai kwanciyar ta keda wuya ba Abinda ya fado mata sai fuskar wannan gayen,

" me yasa kake neman mata? Shine kawai ta samu bakin ta da furtawa tarasa dalilin da yasa taji kawai tsanar shi ta ragu a cikin ranta tunda ta ga fuskar shi a karon farko,

Kirar jikin shi domin ta hango irin muscles din da ya Ajiye na karfi w'anda tasan ba shakka idan ya riki namiji zai ji jiki bare mace,

His face look innocent he look pure but why is he like that? Saurin runtse idanun ta tayi tareda yin Addu'a har barawon ya dauke ta,

*"farkon farawa kenan my fans ina fatan wannan labari nawa da na faro ya baku ni shadin da kuke bukatar samu ya kuma ilmantar daku ya fadakar*

*"ku ci gaba da biyoni nidin ce dai "UMMU AMMAR Aunty Fener ku kuma Matar soja*
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
_*BARIKI*_
_Auren soja_
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

_written by fenerh_
Maman Ammar

*Dedicated to*
Fiddousi mainasara

3&4

Kasan cewar ta saba tashi da wuri, yasa ko a gidan y'ar uwar tata ta tashi tun karfe shida tafara gyara musu gidan,

Ita ta shirya breakfast na gargajiya koko da kosai domin basa rabo da ni kak'ken wake a firij domin k'arin safe,

Saida ta kammala da wannan ta kwashi kayan su ta fita domin d'aurayewa, tana fitowa taci karo da maman Amla na tsaye tana kallon gidan nasu,

Daga murya tayi tareda cewa "ina kwana maman Amla mun sameku lafiya? Wata irin muguwar harara ta zabga mata tareda maka mata mugun tsaki ta shige tareda cewa " karuwan banza masu kwace mazan mutane kawai,

Dariya Yasmin tayi ta girgiza kai "zakiga karuwa ganin idon ki karamar y'ar bariki sai na koya miki darasi,

Tafada can kasan zuciyar ta domin batason tayi wata hayaniya da Matar Aure Ace tayi rashin kunya Amma sai ta gasa ta a ruwan sanyi zata koya mata hankali,

Wankin ta tayi ta shanya kasan cewar ba yawa ta koma ciki lokacin har Ahmed ya shirya cikin kakin shi ya fito fes Maryam na rike da hannun shi tana cewa,

....yanzu dear Bazaka sha ko tea ba? " Nop nayi latti kuma kinga mun makara yau, Shigowar ta yasa suka kalleta ganin ta rike da bocket "Yasmin har kintashi?

" ina kwanan ku ta fada tareda kallon mijin yayar ta "ni ai tun karfe shida Natashi da yake ku yan gayu ne kalli karfe takwas fa yanzu,

" eh bakyason matata ta huta ne ? "Inaso y'ar uwata ta huta don haka nayi mata Aikin komai har breakfast nayi muku yau,

" wow kanwata godiya nake bari ingani yafada yana matsawa wurin d'an karamin table dinsu ya bude flask yaga koko da kosai,

"Gaskiya kin burgeni kanwata a zuba min idan naje office zansha Acan nayi latti oga na jira na yanzu,.

Juyawa kawai tayi ta nemi flask me kyau ta zuba mai koko da kosan yayar ta karba ta rakashi har waje kafin ta dawo cikin gidan,

Kukan yaron Yane yasa ta nufi cikin dakin ta dakko shi dakan ta tayi mai wanka ta shirya shi kafin yasha nonon shi,

Shirya wa tayi cikin kwalliyar ta mai matukar kyau da daukar hankalin duk wani namiji, riga da wandone tasaka sunfito da surar ta mai kyau duk da rigar takai har guiwar ta,

Ta yafa d'an karamin mayafi ta fito tana zuba kamshi da kuma kyalli,
Taku take kamar wata Sarauniyar kyau tsabar jin kanta datakeyi,

Y'ar uwar ta ma saida tace " yayi Autar Mama wannan irin kyau haka saikace suruki na zai zo? Murmushi tayi kafin tace "kin manta kinada suruki a kusa Baban Amla,

" aa Yasmin kirufa min Asiri k'arki tafi kibarni da rigimar Matar nan don y'ar bala'i ce ta karshe wallahi, "takai karshen ta kuwa Aunty watch and see,

...nidai aa ki fita hanyar ta kawai, " hmm kawai tace tayi waje' "ina zakije? " shan iska zanfita "ki rufa min Asiri ki sanya hijabi Yasmin kinsan halin sojoji kuwa?

" wanda duk ya sa rai yasha wuya domin gani nan bari nan wallahi bani ba soja, shiru kawai tayi ta bita da kallo har ta fice,

Tana fitowa Emanuel na fitowa daga cikin gidan ya washe baki tareda nufota jikin shi na rawa"my friend '

"Yes wo good morning EMA, ya zauna gab da ita tareda zuba mata idanu domin tayi mugun yimai kyau, " chiii friend this kind fine no be small ting wo if my oga saw you Ahh,,,

Ya fada yana cizon yatsa basar da shirmen shi tayi tareda kawo wata hirar "why are you not going to office? " na because I dey cook for oga so I no dey go office,

"Friend oga bring one Celine Dione yerstaday no shape no boobs noting I don no wetin he go enjoy there wo?

Wani irin kallo ta watsa mai domin ya fara bata haushi da mu gayen hirar shin nan da baya gajiya kowa ya tanbaye shi oho?

Ta manta ita ke tanbayar shi a da can saboda gulma, kuma ita yau bata bukata impact zaman jiran Baban Amla takeyi Alakar sa idon can ta juya bata ta oga MA yanzu,

Ganin taki bashi fuska ya canja magana " I beg friend help me na oga say ma I cook kuka soup for him before he come back,

Kallon shi kawai tayi domin ya ishe ta da magana gashi da mugun nacin tsiya bata taba dana sanin sake mai fuska ba irin yau,

Cewa tayi ya tafi kawai zatazo ta nuna mai da fatan ogan shi Bazai dawo ya sameta ba yayi saurin girgiza kai "no oga no go comeback now till one O'Clock,

Saida ta fadawa Aunty Maryam ta fito suka wuce tare yana ta faman zabga mata magana,

Tundaga harabar gidan ta fara baza idanu fulawoyin da aka zagaye gidan sunyi matukar burgeta bata taba sanin haka wurin yakeba don bata taba matsawa ko jikin gate din dake zagaye da Bob ware ba ginin na tsakiyar shi,

Wani irin ni ima ke kadawa da ita ga kamshin furanni kala kala ga kayan mar mari zagaye da gidan irin su lemo gwanda mangwaro ayba har ma dasu gwaba,

Tsarin wurin ya matukar burgeta " hmm gidan mutum daya d'an iska yafi kuma kowa tsula iskan ci ogan y'an iska, ta fada aranta,

Falon gidan kuwa ai sai shuru kawai domin tsarin gidan gaba daya kamar Akwai mace saboda kyale kyale ga shi kalar komai favourite dinta purple and white,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.