Complete Hausa Novels

Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel

Reading file: Bariki Auren Soja Complete Hausa Novel.txt

Chapter 1 of 86

(¯`*•.¸,¤°´✿.。.:*քʀօʄɨƈɨɛռȶ աʀɨȶɛʀֆ*.:。.✿`°¤,¸.•*´¯)

тнε αвιℓιтү тσ gυι∂ε ιs тнε мσsт ιмρσятαηт qυαℓιтү α ωяιтεя cαη нαvε, ωε *_ρяσғιcιεηт ωяιтεя's αssσcιαтιση_* ωιℓℓ sнαяε тнεsε qυαℓιтιεs.

INSTAGRAM: https://www.instagram.com/proficient_writers/

FACEBOOK: https://mobile.facebook.com/groups/2455147078097572/

TWITTER: https://twitter.com/pro__writers?s=09

🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻
_*BARIKI*_
👨‍✈ _Auren soja_👨‍✈
🌻🌻🌻🌻🌻🌻🌻

_written by fenerh_
Maman Ammar

*Dedicated to*
Fiddousi mainasara

*Allahamdulilahi Ala kulli halem ina godiya ga Allah mai kowa mai komai da ya bani ikon dawowa a cikin sabon labari na wato BARIKI Auren soja duk kan yabo da godiya su tabbata ga Allah madaukakin sarki wanda ya bani ikon rubuta wannan labari Alkhairin dake cikin shi Allah yasa Alumma su Amfana dashi kuskuren dake ciki Allah ka gafarta min Ameen*

*KADUNA*

N.D.A BARRACK convoy ne na sojoji a Jere na hilux sai wata jeep katuwa guda daya a tsakiyar su,

Katon gate d'in suka shiga na w'anda gaba daya sojojin dake wurin suka kame Alamar girmama wa ga wanda ke cikin jeep din mai ruwan kalar sojoji,

Jiniya kawai ke tashi Alamar koma waye a ciki babba ne a Aikin, jerin manyan gidajen suka nufa w'anda daga gani na manyan sojoji ne dake cikin barikin wanda sune farkon shigowa,

Gidan da yafi kowanne girma suka tsayar da motocin, kuratan sojojin suka fito dauke da bindigogin su tareda kamewa domin jiran Fitowar ogan nasu,

Gaban motar aka bude gefen mai zaman banza wani soja ya fito rike da brief case da kuma manyan wayoyi har ma da jakar laptop duka a hannun shi,

Shi ya bude kofar bayan tare da sarawa da hannun shi daya Alamar girma mawa, w'anda ni a zatona shine ogan saidai ganin wanda yasako kafar shi a waje ai tuni na yi saurin boyewa bayan manyan itacen fulawoyin dake harabar gidan,

Wani kyakkyawa kuma kakkarfan matashi ne fari tas dashi ya fito daga bayan motar sanye cikin kakin green na soja,

Wanda da Alama da wuya ya kai shekara Arba'in a duniya, ga kakin ya mugun fitoda kwarjinin shi har ma da kara bayyanar da kyanshi a zahiri,

Cikin takun shi mai cike da kasaita da kuzari irin nasu na sojoji jarumai, ya fara takawa domin shiga cikin gidan nashi,

Nayi matukar jin mamakin ganin wannan karamin matashin ana bashi girma duk inda ya wuce,

General Muhammad Abdullah kenan G.O.C I DIV Nigerian Army Kaduna

Mutum mai matukar kwarjini da cikar haiba kana ganin shi kasan yana gina jikin shi ta hanyar training da kuma Abinci mai lafiya,

Yakai namiji ta ko ina domin samun kyakkyawan namiji sosai wanda ko wacce mace zataso ta mallaki irin shi,

Kofar gidan nashi ma sojoji ne masu tsaron lafiyar shi, ciki suka shiga shida PA dinshi wanda daga gani Akwai y'ar da mai karfi a tsakanin su da kuma Aminci,

Juyowa yayi cike da bada umarni ya kalle shi "Ahmed take care of them am going to take a bath and rest u can go to your house and rest too,

" tank you sir ya fada tareda mikamai kayan shi ya juya domin isa nashi gidan,

Motar ogan nasu ya bude ya Ciro bandir din kudi ya mika wa sojojin da suka rako ogan,

Sunyi matukar farin ciki shiyasa suke matukar kaunar megidan nasu domin Akwai kyauta kusan kullum sai ya basu kudi su raba,

Kafin su wuce,
Shima PA din da aka kira da Ahmed ya wuce gidan shi wanda yake gaba kadan da gidan ogan nashi wanda kana gani kasan boys quarters ne duk da suma ba laifi sun tsaru Amma ba kamar gidajen manyan ba,

Wata kyakkyawar mace ce ta fito da gudu tareda dan karamin yaronta ta tareshi da murna fal fuskar ta,

Da sauri ya riketa da hannu daya shima fuskar shi cike da fara a dajin dad'in ganin farin ciki a fuskar Matar tashi,

"Madam dina ya Akayi kike irin wannan gudu haka kin manta da Ajiya ta ne kikeso kimun Asara?

Kankame shi tayi gam tareda fara hawaye w'anda kana gani kasan na farin ciki ne. Da kuma jin dadi,

Dagowa tayi tareda Jan hannun shi suka shiga cikin falon su tana cewa " Dadyn Auwal ka tayani murna yau munyi waya da baba harda Mama yau da kanshi zai kawomin Yasmin Ahmed baba ya daina fushi dani,

Ta karasa tana fashe wa da kuka, kan kujerun dake falon ya jata tareda rungume su gam ita da yaron shi yana mai lallashin ta daga gani kasan Akwai wata akasa da har yakesa shi jin tausayin Matar tashi,

"Am sory Maryam nasan nine sanadin komai Amma ki daina damun kanki bazan taba juya miki bayaba kuma gashi kinga su baba sun hakura har zai kawo mana uwar rigima da kanshi,

To kija mata kunne karta zo tana leka min gidan oga don nasan tasa mai ido, ya furta cike da dariya domin kawar mata da damuwar ta,

Dariya tasa itama tareda goge fuskar ta " ai Yasmin Akwai tsiwa ita wai y'anda mata ke shiga da fitane yasa ta tsane shi kuma ko ganin shi bata taba yiba Amma ta mugun sashi gaba da Zagi,

"Hmm pray for him ni kaina ina son oga yayi Aure ko zai rage kwaso mata gidan shi, duk da nasan wasu suke kawo Kansu Amma inaso Allah ya bashi ikon daina wa,

Ameen tace tareda zamewa ta fara kwance mai boot din kafar shi ya rungume yaron shi dakyau a kirjin shi,

" mama tace kar inyaye Auwal inbari har inhaihu tunda bai kaiba, "haka nafada miki tun farko ai kika kiji yanzu tunda mama ta fada zakiji ai,

Dariya tayi tareda mikewa rikeda takalmin domin fita dasu susha iska, bin bayan ta yayi da kallo yana maijin son Matar tashi har cikin b'argon shi,

Muhammad na shiga falon shi yaci karo da takalmin mace, ya kwalawa kukun shi kira tareda ajiye kayan dake hannun shi akan kujerar dake lafiyayyan falon nashi da ya mugun kaya tuwa da kayan Alatu,

Da gudu ya fito yana " yes sir "Emanuel who came? " oga na da madam way day give me money come,

Wani irin mugun kallo ya watsa mai tareda cewa "you are very stupid didn't I warn you ?

" sory sir ya fada yana kamewa kafin yace wani Abu yaji tace "hy M.A ta fada cikeda yanga da kara'i raya gaba daya surar jikinta a bayyane yake don kusan rabin kirjinta da sukayi ruku'u a bayyane suke,

Matsowa tayi tareda rungume shitsam wanda yayi sanadiyyar watsawa Emanuel mugun kallon da ya kwasa a guje yayi kitchen din gidan,

Saurin janyeta yayi tareda daure fuskar shida Sam dama ba Alamar fara'a atare da ita,

" why the you come? Marai raicewa tayi tareda cewa "come on baby I miss you so much that's is why I came,

Kafin ya bude baki yayi magana wata budurwa ta fito daga cikin dakin baccin shi sanye da T-shirt dinshi na Como flag rigar ko cinyar ta bata rufe ba domin idan tayi kyakkyawan motsi za a iya ganin pant dinta,

Wani irin kallo ya bita dashi tareda kwalawa Emanuel kira cike da bakin ciki,

Da gudu ya fito rike da cooking spoon yana sarawa " yes sir, wani irin disgusting look yake aika mai kafin ya ce,

"Are you stupid,? " no sir Am sory "na she tell me say..... " come on keep quite, ya fada yana mai ture su duka cike da fada "now All of you out of my house, you All no my rules no one comes to my house without my permission,

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.