Complete Hausa Novels

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 9 of 56

_*page*_ *```26```*

Kauda kansa yayi gefe dan shi sam tunanin hkn bai fad'o masa ba shidai kawai dukan ta yaso yi har sae jikinta ya gaya mata.

Ya kalle ta ta6e da baki yace"badai akwai fata a jikin ki ba wacce zata aika miki da saqona har ixuwa daqiqiyar qwaqwalwarki"

Rynt ta wani qara bud'e manyan idanuwanta ganin yana zare belt d'in wandonsa ,

ta fizgi jikinta da qarfi tace"wae dukana zakayi, don Allah kayi baquri wlh duka fa da zafi"

Yace"da zafi?eh wlh don Allah kayi haquri bazan sake fita ba sae da izinin ka na rantse!bai kula ta ba yayi cikinta ya fara dukanta kan qafafunta gunda hijab bai qarasa kai ba ,

ihu take sosai tana bashi haquri amma fafau yaqi haqura sae da ya zane mata qafafu tas snn ya dakata tare da nuna ta da yatsa yace"idan har tunanin kike kinzo nn gidan don jin dad'i shine har kike fita anguwanni to ki cire kisa a ranki nn tmkr kurkuku kika shigo don haka daga yau ko qafar ki kar na qara ganin ta fito daga d'akin,nn ya kama kunnen sa yace"kinji me na gaya miki? da sauri ta gyad'a masa kai cikin kuka,nn wyr sa tayi qara ya d'aga had'e da fita d'akin Rynt kuwa ta had'e kanta da guiwa tana ci gaba da kuka ,takai hannunta cikin hijab tana shafa qafafuwanta da duk sukayi shatar belt.

Tana jin za'a shigo d'akin tayi saurin d'aukar zanin ta ta d'aura ,mohd ne riqe da hannun mami ta tafi da gudu ta rungume Rynh wacce tayi saurin share hawayenta kar mami ta gani ,

mami tace"Anti na dawo ne sbd inajin dad'in zama gurinki sbd kullum kina koya min karatun islamiyya ko yau zaki koya min kafin muyi bacci ko? Dan guntun murmushi Rynt ta qirqiro ta gyad'a mata kai kawai don har lokacin man na tsaye yana kallon su, mami ta maida dubanta gare shi tace"yauwa yaya d'azun da mukaje gida nida anti har nake gaya ma Abba cewa kullum kullum mu kad'ai ne a cikin gida ba mai kawo mana fira daga ni sae anti har kai bama gani sae yau kad'ai muka ganka kaida anti amarya zaku tafi anguwa sae naji Abba yace wae zaka zo ka same shi ne ai,to yaya kaje ka same shi d'in don wata qil aiken ka zai yi ko?kallon su yayi da ita har Rnyh d'in kafin yace komai mami tace"yaya wai anti d'azun da mukaje gida har na gaya ma Abba haka tace min wae kar na qara gayawa kowa haka kuma wae na rage yawan srt ba kyau wae hakane yaya?hakane mami,yayi mgnr ne a takaice ya kuma juya zai bar d'akin ,

mami taje da gudu ta riqo hannun shi tare da d'aga kanta tana kallon shi tace"yaya yau ma baza ka taya mu fira ba tafiyar ka zakayi?eh zan tafi ne naci abinci,nima yaya zan bika muci abinci,yace"to muje"Rynh na kallo suka fita taje ta kwanta ruf da ciki tana ci gaba da kukanta .

Sae goma da rabi mohd ya dawo d'auke da mami wacce tayi bacci ya samu ita ma Rynt tayi bacci sae dai kallo d'aya xakayi mata kasan da tsoro baccin ya d'auketa don duk ta cusa fuskarta cikin pillow ta kuma damke pillow kmr wacce za'a qwacewa shi ,

yaje a hnkli ya kwantar da mami snn ya kalli Rynt wacce cikin qaton hijabinta tayi baccinta nn idonsa ya fad'a kan santala santalan qafafuwanta da hijab bai ida rufewa ba da har yanzun suna d'auke da shatar dukan da ya mata,ya kauda idonsa snn ya fita yaja musu qofa ya rufe.

Washe gari Rynt ta tashi cike da jin yunwa sbd jiya da dare bata ci abinci ba tayi bacci.

Tana gama yi ma mami wanka ta shiryata,mami tace zata je gun yayanta nn mami ta fita ita kuma Rynt taje kan bed ta zauna cike da tunanin inda zata sami abinci tunda yanzu kam inna bazata qara aiko mata ba.

Tana nn zaune yunwa ta cita har ta gode Allah sae duk rayuwarta ta baya ta dawo mata nn ta had'e kai da guiwa ta fara kukan tuna baffanta, sae jin tayi an turo qofa ta d'ago fuskarta a hnkli don ganin wanda ya shigo.

Mohd ne yaja ya tsaya a nn bakin qofar ya jingina tare da sanya hannuwansa a aljihun wadonsa yana kallonta ita ma tana kallon shi da idanuwanta da suke cike tap da qwallah ta taso cikin tafiya kmr bata so har ta qaraso gurin shi tayi tsaye tare da sadda kanta qasa tana kallon farin tiles d'in d'akin,mohd ya fiddo d'ayan hannunsa a aljihu ya d'ago fuskarta dashi yayinda hawayen idonta ke silalowa a hnkli kan kumatunta sae dai still idonta na qasa sae da yace"mene ne"snn ta kalle shi tare da fad'in yunwa nakeji tun jiya banci komai ba"

To shine zaki wani ajiyewa ma mutane kuka !ni ba yunwa nake ma kuka ba ai,to me kike ma kuka? tace"nidai ka taimaka min da abinda zanci.... idan anqi fa, Allah zai taimake ni,au kinsan da Allah kuma kika ce ni na taimaka miki,shiru ta mishi ta komawarta kan gado tayi kwancinta ya saki guntun tsaki ya fita daga d'akin.

Ba jimawa sae ga kukun gidan ya kawo mata abinci tayi mamaki don ita kanta roqonsa kawai tayi bata d'auka zatayi nasara ba ,

don a nn kwancen da take har ta fara tunanin tashi ta sami ruwa tasha kmr yanda ta saba yi a qauye.

Sama Sama taci abincin sbd abincin duk rabinsa ganye ne ita kuwa ba son ganyen take ba tunda ba'a saba ba, don ko yanzu ture ganye tayi gefe taci abinda take iya ci tabar saura, bayan d'ayan plate d'inda ta ajiyewa mami.

Bayan kwana d'aya da faruwar haka Rynt na zaune a tsakiyar gado ta lanqwashe qafafu tana karatun qur'ani cikin muryar ta mai dad'in sauraro ga duk wanda yaji,mohd ya shigo d'akin yayi tsaye tsawon lokaci bata sani ba sae karatu take abinta, sae da yayi gyaran murya snn tasan da shigowar shi ,kallon sa take ba yabo ba fallasa haka shima sae dai kuma zama d'aya ya sha mata toka ya juya tare da fad'in "biyoni muje ki gyara min d'akina"

Ba musu ta ajiye qur'aninta ta bishi.

Tsarin gidan tsari ne da d'akunan matan shi suka saka shi tsaka wanda dole duk wacce zata je d'akin shi sae tazo ta main falo take zuwa kuma in an shiga qofar da zata sada ka da 6angaren shi sae an hau upstairs kafin ka kai ga d'akinshi.

Rynt sae rarraba ido take tana kallon koina don dai gurin ya zamar mata kmr aljannar duniya,suna shiga d'akin mohd ya juyo gareta yace"kinga d'akin sae kiyi ki gyara min kan lokaci"

Gyad'a masa kai kawai tayi,shi kuma ya fita yaje 6angaren malika,ya sami malika jikin wardrobe yaje ya rungumo ta ta baya tare da fad'in"malika had'a min kayana dake d'akin nn zan koma d'akina ne yau"ta juyo tare da qara rungume shi snn tace"gsky ba inda zaka je muyi zaman mu guri d'aya yafi don ni bazan iya whlr jeka ka dawo ba"

yace"hqr dai zakiyi malika sbd komawata d'akina shine saiti "ta d'ago a fusace tace"ok kana nufin zaka raba mana duty tsakani na da wnn abar! girgixa kansa yayi yace"ko d'aya kuma kwata kwata ki cire wnn tunani a ranki kawai dai ina buqatar komawa ne"to gsky ni bana buqatar ka koma can! yace"A'a fah!cikin masifa tace"to wlh duk ka koma sae na bika!ya gyad'a kafad'a tare da fad'in "no vex yanzu sae ki had'a mana kayan ko? murmushi tayi snn tace"yanzun naji bayani don wlh ban yarda da zamanka kai kad'ai ba"yace"to da sharad'i ba gabad'aya fa xaki tare guna ba...kmr ya?kawai bacci zaki riqa kai min sbd bana son kowa na shigar min 6angare,sbd frnds d'inki sun fiye zowa kin sani ba kuwa zai yiyu kina zuwar min dasu 6angarena ba,ta wani 6ata fuska tana kallon shi tace"to meye a ciki don naje dasu kawai kai dai na fhmce ka so kake da rana ka riqa zuwa kana holewa da wnn yrnyr,cikin daka mata tsawa yace"wlh kar na koma jin kin ambata min wnn yrnyr idan muna zancen mu!bcs i am absolutely hate her!don haka yawan yimin zancenta kan iya sa qiyayyar da nake mata ta dawo gare ki be careful!daga haka ya juya zai fita daga d'akin ,

malika tayi saurin rungumoshi ta baya, tare da fad'in "my man yi hqr zan kiyaye kaji"sae da ya sauke ajiyar zuciya snn ya juyo tare da riqo kumatunta yace"malika ina mata d'aukar baiwa ne ba mata ba amma ke kinxo kina alaqantani da ita a matsayin matata wlh malika da kinsan baqin cikin da nake ji da hkn da ko da kuskure baza ki ambata min ita ba,kayi hqr my man bazan sake ba,fuskarta ya shafo tare da fad'in "shi kenan ya wuce muje mu had'a kayan ko?murmushi ta sakar mai taja hannun shi suka nufi wardrobe.

Rynt kuwa nn take ta gyara d'akin tsaf don dama ba wani datti ne dashi ba ,zata fita kenan idonta ya hango mata wani photo na mohd su uku wato shida abokan haifuwar shi, ta d'auko d'an frame d'in tana kallo nn ta fhmci akwai rubutun da akayi kmr fulawa dan sae ka kula da kyau kake fhmtar rubutu ne akayi ,

Aamil,Amir &Aminullah shine a rubuce ta qasan kowanensu.

Shafa rubutun ta shigayi sbd ba qaramin kyau ya mata ba yayinda ta shiga kallon fuskokin su cike da son gano meye banbancin su,sae ga mohd rungume da malika sun shigo d'akin,malika na ganin abinda Rynt keyi tayi saurin d'agowa daga jikin man tace"kaga er iska photonka fa take kallo shine har da wani shafawa!

taje fuuu!ta fizgi photon tare da kife Rynt da mari tace"keda aka sa gyaran d'aki me kuma ya kaiki ga photon mijina er iska ,tambadaddiya dake nake! ki gaya min ko wlh na qara miki wani marin ynx!nn mohd yazo gun Rynt wacce ta dafe kuncenta yace cikin kakkausar murya"dan ubanki aikin da na saki kenan ko kuma ni sa'anki ne da zaki d'auko photon mu kina kallo!bari kiji wlh daga yau duk nasaki aiki naga sa6anin haka ubanki na lafira ma sae yafi ki jin dad'i!da sauri Rnyt ta d'ago idanuwanta da sukayi jajir suka ciko da qwallah tana kallon shi.

Billy giro😊

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

[2:48PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [1/13/2017]

🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

🔮🔮🔮

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.