Complete Hausa Novels

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 7 of 56

_*page*_ *```24```*

Bayan ankaita kowa ya watse ita kad'ai a d'aki sae autar su saliha da suke kira da mami.

Ambar mata ita ne sbd ita Rynh d'in ta nemi haka sbd mugun tsoron bacci ita kad'ai take ji.

6angaren su mohd kuwa bayan an kawo amarya suka tsiri wani party maxa da mata sae shagali suke duk Rynt ta kasa samun baccin kirki sbd hayaniyar su hkn yasa ta tashi ta d'auro arwala ta shiga yin nafilfili yayinda autar mama keta sharar baccinta.

Sae kusan qarfe d'aya da rabi en party suka watse amma hkn bai hana mohd da malika suka sha amarcin su ba.

Washe gari sae da Rynt tayiwa mami wanka snn ita ma tayi nata wnkn.

Ta gama shiri kenan taji an turo qofa saliha ta shigo mami taje da gudu ta rungumeta Rynt kuwa tazo cikin sakin fuska saliha tace "amarsu ta ango ya amarci?murmushi kawai Rnyt tayi snn tace"nidai yasu umma? Lafiyar su qalau tana ma gaida ke ,ta fad'i hkne tare da ajiye basket d'inda ke hannunta tace"ga break fast inji umma,Rynt tace"mun gode"

Byn sun zauna saliha

ke cewa yaya fa?Rynt tayi kmr ma bata ji ta ba tace"wai shin saliha yaushe ne kika ce zaku koma makaranta?

Saliha tace "kinsan na gaya miki cikin satin nn hutun mu ya qare sae aurenku yazo ya tsaida mu amma yanzu rnr lahadin nn zamu koma,Rynt tayi shiru can tace"to yaushe ne ake saka sabbin d'auka? Da zarar mun tafi yanzu munyi third term muka dawo gida mukayi hutu se mu koma first term to a lokacin ne ake kai sabbin d'auka sbd anyi canjin aji,yanzu za'ayi kmr wata nawa kafin haka don ni tunda inna tamin albishir d'in bokon nn na qagu naga na fara boko nn wlh,saliha tace"hm boko ko wahala ,komai wahalar sa zan so nayi saliha sbd a rayuwa ba abinda ke birge ni kmr ilimi, gskyr ki ne Rynt sbd ba abinda ya kai ilimi dad'i.....qofa suka ga an tura koda suka duba Ameera ce yamutse da fuska tace da saliha"wae ke a nn kika shigo, nikam ki sameni 6angaren anti malika, saliha tace"to sae idan zamu koma xaki ganni"

nn Ameera ta ka6a kai ta fita,Rynt tace"ai da kin bita kun tafi d'in"saliha ta ta6e baki tace"um um sae idan zamu koma"

Rynt bata sake cewa komai ba sae zama sukayi zasu ci abinci sae ga wani saqon abinci daga gurin inna, sosai Rynt taji dad'i sbd abincin da take mugun so ne inna ta aiko mata.

Ameera kuwa koda taje 6angaren su malika ko bud'e qofa basuyi ba sae da tayi ta fmn danna door bell snn sae can ta samu aka bud'e .

Man ne da malika rungume a jikinshi da gani yanzu ne tashin su don malika farin bedsheets ma ne a jikinta man kuwa yana sanye da white bathrobe yayinda fuskar sa take d'aure tamau yana kallon Ameera yace"lfy zaki mana wnn sammako hk?kafin Ameera tace"komai malika tace"haba my man ba qanwar ka bace? Ko qanwa tace sae tazo ta takura ni, kiss ta d'ora masa a gefen fuska tace"kuma fa tayi laifi amma ayi haquri ta shigo ta zauna sae muje muyi wanka ko,lumshe mata ido yayi alamar suje d'in ,ba tare da kowanen su yace da Ameera ta shiga ta zauna ba suka juya zasu tafi, malika ta kalli mohd tace"my man me xai hana ta d'aura mana break fast kafin mu fito don wlh yunwa nake ji"ba musu ya juyo ya kalli Ameera da bata riga ta shigo ba yace"ke shigo kije kitchen ki d'aura mana girki"

Ameera ta shigo tare da rufe qofa tana ji kmr ta fasa ihu don ta tsani aiki ba kad'an ba.

Mohd kuwa suna shiga d'aki malika ta jefar da bedsheets din jikinta ta dawo nakedness,hm mohd sae d'aukar ta yayi suka je toilet.

Bayan sati 1 da faruwar haka tuni su saliha sun koma school ,mohd da malika kuwa sae cin amarcin suke inda ko sau d'aya mohd bai ta6a leqa 6angaren Rynt ba.

Sam Rynt bata damu ba wacce har yanzu inna na aiko mata abinci,kuma bata da wani kad'ai ci sbd still mami na nn da kullum tare suke cin abincin su suna kallo.

Yau tun da safe da suka tashi mami keta kuka ita gida take son zuwa gun ummarta duk Rynt ta shiga damuwa tayi rarrashi har ta gaji amma fafau taqi shiru ita sae taje taga mamarta.

Ba yanda Rynt ta iya dole ta shirya dmn kaita gida tunda ba waya ne da ita ba bare ta kira azo a d'auke ta kuma ko banza tana son zuwa gida don zaman banzan nn ya isheta tana son komawa islamiyya.

Hijabinta har qasa ta zuba ta jawo hannun mami suka fito suna kawowa harabar gidan ta sami kanta da mamakin ganin mohd zaune kan resting chair shida wani mai kama dashi sak har ma baka babance su,sam mami bata kula dasu ba sae kuka ta ajiye wae Rynt ta d'auketa ita bacci take ji,nn Rynt ta d'auke ta tare da d'aura ta kan kafad'a sae jin tayi tace "lah anti ga yaya da anti amarya sun fito"a hnkali Rynt ta juya bayanta don ganin wad'anda mami ke nufi sae kawai taga mohd shida malika ta kalli gun resting chair taga still wad'an can su biyun suna nn zaune abinsu suna fira ga kuma mohd shida malika tsaye mutum uku kenan fa iri d'aya nn kan Rynt ya d'aure sosai tana tunanin shin dama su en uku ne.

Kuyi hqr da wnn.

Billy giro😊

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

[2:48PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 1/11/2017]

🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

🔮🔮🔮

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.