Complete Hausa Novels

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 20 of 56

*page* *38*

Yace"wae kukan name to! Tace"na gaya maka test mukeda kuma malamin idan akayi letti duka yake kuma baya bari a shiga aji har sae ya fita"

tana maganar ne cikin muryar kuka .

Yace"oya shiga bathroom zaki samu na had'a ruwan zafi ki shiga ciki ki gasa jikin ki"

Tace"Dan Allah kabari idan na dawo wlh bana son ayi test bana nn"

Bai kula ta ba sae kan sofa yaje ya kwanta snn yace "idan kinga dama kije ki gasa jikin naki idan kuma tsayuwar zakiyi tayi to.

Daga nn ya rufe idanuwan sa Rynt kuwa wani takaici ne ya kawo mata iya wuya,ita ba don tana son bokon nn ba da ba abinda zaisa ya kama yi mata abubuwa hk ta barshi.

Haka ta nufi toilet tare da fashewa da wani irin kuka na takaici tana maganganun da ba'a jin me take fad'i,wacce tana shiga bayi ta rufo qofa da qarfi kuma sae jin abubuwa kake suna ta 6irari ga dukkan jefar dasu ne take.

Sae a snn mohd ya bud'e idonsa ya koma rufewa,jin ihunta yasa shi saurin tashi yaje bakin bathroom d'in yace"lafiya"tace"to ai ruwan ne da mugun zafi baka gaya min ba"

Yace"sae na gaya miki ke bazaki ta6a ruwan ba kafin ki shiga"

Uhm Uhm wlh Allah kayi min mugunta.

Tsaki kawai yayi yace "kinga kiyi sauri ki sirka ki fara abinda nasaki ,ni ina da abin yi idan ba hk ba zaki fito ki samu bana nn"

Daga haka ya koma yayi kwanciyar sa.

Bata wani jima sosai ba ta fito gudun kar ta samu baya nn ,

ba tare da ya bud'e idon sa ba yace"har kinyi me? Har na gama mana,to koma ki sake zama,tace"haba dan Allah kaifa kace nayi sauri"

Yace ke kika sani jikin ki ko nawa.

Daga haka ya tashi ya fita tabi bayan shi wacce yanzu har sauri take had'awa dashi sbd jikinta duk taji ya sake mata ba wani ciwo sosai d'in nn.

Bayan en wasu kwanaki da faruwar haka.

gabad'aya Rynt ko gaida man ta daina yi asali ma in ya shiga d'akinta kmr ma bata ganshi ba takeyi haka shima mami kawai yake kulawa.

Karatun ta kawai ta sa ma gaba sae dai a duk lokacin da ta tuna cewa wani abu ya shiga tsakanin ta da man sae ta zubar da qwallar baqin ciki,taji inama rayuwa zata koma baya da rnr bata je gyra mai d'aki ba.

D'aki take ta dawo daga mkrnta kenan ta ajiye jaka snn ta cire hijab,d'ankwali da takalmi da kuma socks ta kalli mirror taga gashin kanta duk ya taso ta cire ribbon sae ga mami ta shigo da gudu tare da cire school bag d'inta ta jefar haka hijabinta da takalma sae kuma ta fita da gudu abinta Rynt ta d'auke kayan ta kaisu duk inda ya dace snn ta taje kanta ta shiga bud'e buttons d'in rgrta ,ta bud'e na farko da na biyu sae kawai taji ihun mami.

Ba shiri ta fito da gudu don ta d'auka ko wani abu ne ya same ta sae taga ashe pretty ce tazo shine take ihun tarbonta.

Rynt ta d'an saki fuskarta ta gaida pretty wacce tayi kunnen uwar shegu da ita,Rynt ta qara gaida ta indà cikin daka tsawa pretty tace"da Allah ni kin cika min kunne bana buqatar gaisuwar ki dole ne!

Rynt ta kauda kanta zata juya ta bar gurin sae ga man ya fito shida malika,pretty ta gaida man yayinda malika taje da murna gun pretty tana fad'in"oyoyo mamn twins ya tsufa, pretty ta ta6o tulun cikinta tace"wlh gashi nn muna fama dashi ita kuma er iskar yrnr nn ta wani zo tana cika ni da gaisuwa sae kace don ta nazo"

Malika ta ta6e baki tare da kallon Rynt tace"kinsan matsiyata sun fi kowa baqin shisshigi da cusa kae ba farin jini"

Wlh kuwa kmr kin sani cewar pretty wacce malika taja ta zuwa 6angarenta yayinda mami ke biye dasu.

Rynt kuwa bata bar zuciyar ta taji zafin mgnr su ba sae juyawarta tayi zata koma d'aki tare da jin hausin kallonta da taga man nayi,wanda ba don komai yake kallonta ba sae don ganin yanda yalwataccen gashin ta ya sauka har kafad'unta, ba kmr na malika ba dako kan wuyanta bai kawowa shiyasa kullum take fama da sa na kanti.

Har Rynt ta fara taka matattakala ne taji sallamar nasir tare da fad'in "ah Rynt"fuskarta wasae ta juyo tace"na'am yaya nasir ina yini yace"lfy lau ya mkrnta? bata riga ta amsa ba taga man ya dalla mata muguwar harara had'e da kallon qirjinta,

a kafaice ce ta kalli qirjin nata wacce sae a snn ta tuno yanda ta fito ba hijab ga buttons d'in rgrta da ta fara bud'ewa amma ba'a ganin komai sae white vest d'inta wacce ko ita kad'an ake hangowa.

Ai kuwa da sauri taba nasir amsa ta wuce.

Su Malika kuwa suna shiga d'aki pretty ta kalli mami tace"mami jeki ki cire uniform kici abinci sae kije gun yaya nasir ya siyo miki ice cream ko.

mami ta fita d'akin da murna yayinda

pretty tayi saurin bud'e jakarta ta ciro wani qullin magani ta bawa malika tace"umma ce tace na kawo maki kisa ma wnn matsiyaciyar yrny a abinci taci ta haukace tabi duniya.

Malika ta kar6a fuska a yatsine tace"nifa ba iya abubuwan nn nayi ba"pretty tace"ai kuwa shiyasa gata nn har yanzu kin kasa ftr da ita abin haushi har shi kanshi yaya dako yaushe yaso rabuwa da ita zai iya amma shiru kmr an shuka dusa"malika tace"hm ni kaina abin na ban mamaki da haushi wlh"

pretty tace"yo kina tunanin a banza tabarshi ne wae ace tun auren ku umma ke fushi dashi akanta amma still yaqi rabuwa da ita ai kinsan ba a banza ba wlh,dashi har Abba ni ban yarda cewa ba wani abu tayi musu ba.

Malika tace"that's y ba'a banza ba kenan shiyasa naga an sanyata a tsadaddiyar mkrnta har ma wae ana mata extra lesson a gida"

Pretty tace"to kin gani idan zaki tashi tsaye ki tashi tsaye don wata rana baki da kwanan ceto zata qwace miki miji kizo ki zama er kallo har dai idan ta fara hayayyafowa......tuf! bari zancen nn dan Allah da wane matsayin nata zai fara kula ta har takai ga fara haifo 'ya'ya.

Pretty tace"kina sake da baki kuwa duk hkn zata faru don gashi yanzu kece ke baki iya aiki da irin wnn maganin ba"

To gaya min yanda zanyi inji, pretty tace "kmr dai yanda na gaya miki a abinci zaki saka mata da zarar taci ko lomo d'aya ce tofa hauka tubran,few! kuda sake jin lbrnta sae dae ko a lafira, malika tace"aike matsalar kuku ke dafa mana abinci kuma har dakin ta yake kai mata nata abincin,

but zan san yanda zanyi bcs man zaiyi tafiya a kwanakin nn byn ya tafi zan sallami kuku ,

dolenta zata fito zuwa girka abinci da haka zan fake tana d'agawa zanje na zuba mata shi a abinci,idan man ya dawo bae sameta ba ce masa kawai zanyi tun rnr da kayi tfy itama ta sa qafa ta fita.

Pretty ta kwashe da dariya had'e da bata hannu suka tafa.

Bayan kwana d'aya da faruwar haka man ne zaune a tsakiyar gado ya lanqwashe qafafu yana aiki da laptop sae ga malika ta shigo d'akin riqe da kofin coffee a hannunta kan gadon ta hau taje close to man tayi irin zaman da yayi tana mai kallon aikin da yake a laptop ta miqa mishi coffee tare da fad'in gobe ne tafyrka ko?

Sae da ya kar6i coffee ya kuma yi kur6i d'aya snn yace"eh ko kina zuwa? Tace"Aa"

Yace"en son yawon basa kai kenan"tace"hakane kam sae dai idan zakayi wata tafiya xan bika"

Kallon ta kawai yayi yaci gaba da shan coffee d'insa.

Tace zakayi sammako ne? Yace"sosai kuwa da wani abu ne ?um um ba komai.

Sukayi shiru can malika ta kalle shi ganin yanda yake ta kallon fotunan yara kyawawa,

dama tasan aikinsa ne kullum sae yayita searching d'in pics d'in yara yana kallo"

Cikinta kawai taji ya shafo ya kalleta yace"malika ina son yara sosai amma naga kmr ba kya son haifo min"

Murmushi tayi tare da shafo gefen fuskar shi tace"zan haifa mana nawan kasan ina son abinda kake so"

yace"ina son yara da yawa amma Abbanki bazai bar mu ba,hancin sa taja tace"abu mai sauqi se na haifa maka en uku a lokaci d'aya kmr ku"yayi murmushi yace"da kinci babbar kyauta kuwa tace"Allah"yace"dgske"tace "kmr me kenan?yace"sae abinda kika ce kina so"tace"wow har na qagu naga na samu ciki"

yace"na fiki qaguwa da hk"tace"a daa kenan amma yanzu na fika"

Yace"dsgske to meyasa?ta bashi kiss snn tace"sbd ina sonka da yawa kuma xan so ko yaushe na ganka cikin farin ciki "

"Uhm"shine kawai abinda yace yaci gaba da shan coffee yana kuma ci gaba da kallon fotunan yara.

A sha biyu na daren rnr ne mohd yaje d'akin Rynt ya samu sae bacci suke ita da mami,

kowaccen su na sanye da riga da wando na bacci ga littafai watse akan gadon ga dukkan alama baccin kwasar su yayi basu kammala abinda suke ba dan har ma biro ya hango riqe a hannun Rynt,a hnkli ya zare biron yana mai kallon fuskarta snn ya tsince kaf littafan ya d'aura su akan bedside drawer yayi tsaye yanata kallon Rynt bako qyaftwa sae itace ta motsa tare da juya mai bayanta amma duk cikin bacci ne bawai don tasan yana tsaye ba.

Numfashi ya fitar a hnkli yaje yaja blanket ya rufe musu jikin su sbd yanda yaga yanayin kwanciyar Rynt da kmr sanyi take ji.

Sae da ya kashe musu wuta snn ya rufo musu qofa ya fito.

A washe gari tunda safe kuwa man ya tafi.

Ko breakfast malika bata bar kuku ya had'a ma mami ba ta sallame shi a gaban su Rynt don kawai Rynt tasan anjima dole zata fito d'aura girki.

Hkn yasa ta riqa kud'in breakfast har da mami.

Da yamma su Rynt sun dawo school a gjya amma hkn ta jure ta fad'a kitchen ta d'aura musu taliya snn ta koma d'aki dmn ta d'an watsa ruwa.

Dama malika na zaune a falo tana ganin wucewar Rynt ta nufi kitchen ta bud'e girkin ta zuba garin maganin kaf ta motse ta rufe snn ta fito.

Taje har d'akin Rynt ta jawo mami tace"muje kici abinci"tace"ai Anti ta d'aura mana abinci malika tace"wanda zan baki yafi wanda take dafa muku dad'i ko ba kya ci?tace"ina ci"

Bayan sun fito mami ke cewa "anti ina son zan d'auko teddy na a d'akin yaya "

tace"to muje ki d'auko"

Bayan sun fito ne suka tafi d'akin malika ,malika bata bata abincin ba sae waya ta shiga yi bayan ta gama ne ta d'aukowa mami ragin abincin ta da taci mami ta kalli abincin a yatsine tace"anti aini bana cin ragi tace"don ubanki da kike cin ragin yayanki fa!

To anti yaya kika ce...iyye lallai ma yrnyr nn oya ftr min a nn! daga ma naso taimakon ki!mami ta wani turo baki tana kallonta snn tabar d'akin,

malika ta buga tsaki tare da kwanciya kan sofa tana fad'in"Allah yasa har kema kici abincin duk ku haukace ni ba ruwana.

Mami kuwa d'aki taje bata sami Rynt ba ta fito sae wasa take da qatuwar teddyrta ta nufi kitchen ta samu dai dai Rynt ta gama zuba abinci a tray ta juyo riqe da trayn a hannun ta.

Billy giro😊

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 1/30/2017

```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.