Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 27 of 56
*page* *```45```*
Man kuwa yana fita d'akinsa ya tafi ya sami malika zaune kan sofa tana shan 'ya'yan fruits yaje kusa da ita ya zauna ta kaimai slice d'in kankana a baki tare da fad'in"ya baka fita ba ko kun fasa ne? Eh an d'aga meeting d'in sae zuwa 12,tace"OK" daga hk suka ci gaba da shan fruits suna er firar su a cikin firar ne man ya d'auko laptop d'inshi yana nuna mata wasu kayan jarirai da ya gani masu kyau yace"duk a England ake samun su,tace "wow yaushe zamu je siyo kyn? Yace"na fison sae cikinki ya farà qwari muje har sae idan kin haifu snn ko zamu dawo amma zan riqa yi ina dawowa sbd aiki na,kiss ta d'aura mai tace"wnn ba matsala bane"
Yayi d'an guntun murmushi yana ci gaba da nuna mata wasu kyn jarirai.
Rynt kuwa ta jima kwance abinta tana baccinda ya mata dad'i fiye da kowanne.
11:30
Man ya shigo d'akin still sae bacci take,dube dube ya shiga yi ta inda zai ga suit jacket d'insa wanda har bathroom ya duba amma bae ganta ba.
Hkn yasa yazo ya durqusa gab da ita yakai hannu ya d'an yaye mata blanket kad'an, nn yaga jacket d'in na jikinta hannuwanta na jikin qirjinta da ta kama magamar jacket d'in ta riqe gam.
Ganin hkne yasa ya janye hannuwanta a hnkli ya rufe mata buttons wanda garin hkne ya hango d'an bum short d'inda ke jikinta kauda idonsa kawae yayi ya rufa mata blanket ya fita .
Ba ita ta tashi ba sae qarfe d'aya.
Ta tashi zaune tana mai kama mgmr jacket d'in,ga mamakinta taga an sanya mata buttons d'in rgr,ai kuwa taji fad'uwar gaba don tasan mohd ne ya shigo qila ma ya ganan mata jiki nn taji wani irin haushinsa ya kamata meye ruwansa da ita da har zai zo ya samu tana bacci ya yaye mata blanket har yakai ga sa mata buttons, ta buga tsaki tare da mamakin wane irin ma bacci ne tayi da har hkn ta faru bata jiba ita da sam bata da nauyin bacci .
Rae 6ace ta d'auko towel ta cire jacket d'in ta jefar kan sofa snn ta nufi bathroom ta watsa ruwa sbd ta samu jikinta ya sake mata kan baccin da tayi.
Koda ta gama shiri duk yunwa ta cika ta sae a lokacin ta tuna ko break fast ma batayi ba a nn ta kula da plate d'inta na break fast ,ta d'auki plate d'in ta fita ta kar6o wani abinci gun kuku.
Sama sama ta samu taci abincin sbd tana jin jikin nata ba dad'i shiyasa ko cinye abincin ma ta kasa yi taje takai ragowar ta dawo har zata kwanta taji kiraye kirayen sllr zhr sae a lokacin ta kalli agogo taga biyu saura dama tayi arwala da taje wanka kuskure bakinta kawae taje tayi tazo tayi sallah.
Tana idar da addu'a ta jawo pillow ta kwanta nn kan sallaya wacce sae son take ta tashi ta d'an dudduba littafanta amma tana jin kmr jikin bazai barta ba.
Haka ta yini bata jin dad'i sae da tasha magani ne ta samu jin sauqi.
Wacce har washe gari bata sake jin komai ba.
Sae dai koda suka dawo school gabad'aya zazza6in ya dawo mata don ko uniform bata iya cirewa ba ta kwanta sae bacci.
Mami kuwa ta cire uniform taje ta watsa ruwa ta saka er doguwar rgrta ta kanti da iyakarta guiwa taje d'akin yayanta ya bata abinci taci byn ta gama ya sama ta kallo nn malika taxo ta same su tace"my man wnn abar fa banga ta fito ba bare zancen d'aura min girki kuma kaga dae ba yanzun ne dawowar su ba zamanta ne kawae tayi "Yace"jeki zanje na taso ta "
Nifa i cnt wait any more don yunwa nakeji sosai kuma kar ma mai lesson d'insu yazo ta wani ce zata zauna ma lesson ,hannun ta yaja suka fito yana mai fad'in "ai mae lesson d'in nasu bazai sami zuwa ba yau yayi tafiya"
Ta6e baki tayi tace"hm lesson d'in ma nsn ba komai take ganewa ba don da gani kwañyar kifi ce da ita....wyr tace tayi qara tana ganin qawar ta faiza ce mae kiran ta nufi d'akinta shi kuma man ya wuce zuwa d'akin Rynt.
Tsaki yayi ganin ko uniform bata cire ba amma tayi kwance tana bacci yace"lallai yrynr nn kinji dad'inki"
Nn yaje yana tashinta da doka mata jiki ta tashi cikin mugun 6acin rae tana kallon shi tace"wae meye!?
Yace"tambayata ma kike oya tashi kije ki d'aurawa malika girki"
Tace"cab ni wlh bazan iya ba don bana jin dad'i"
Yace"bana son raini maza tashi kije ki d'aura mata girki ko kuma wlh nayi maganin ki"
Cikin marairaicewa tace"wlh bana jin dad'i ko tsayuwa ma fa da qyar nake yi"
Yace"Bari kiji ko a kwance ne sae kin d'aura mata girkin stupid girl!
Cikin muryar kuka tace"wae kai meyasa baka da tausayi ne,na gaya maka bazan iya ba bana jin dad'i wlh.
Zowa yayi gab da ita yakai hannu ya d'ago fuskarta da kyau yana kallon ta yace"shin kin manta abinda na gaya miki ne na dole kibi abinda nace idan ba haka ba karatunki"
Da mugun tsana take kallon shi tace a ranta
_"mugu kayi abinka lokacinka ne nawa na nn zowa da zan rabaka da farin cikin ka gabad'aya don wlh bazan barka ba"_
Daga hk tafita ta bar shi tana saukowa downstairs ta had'u da malika wacce ta sha gabanta tana gaya mata maganganun banza.
Tsaki kawai Rynt tayi ta ra6a ta gefenta ta wuce.
Cike da azama malika tayi niyyar fizgo Rynt sae kawae ta hango man tafe nn tayi saurin sakin glass cup d'inda ke hannunta ya fad'i qasa ya tarwatse ta duqa kmr zata tsince glasses d'in dae dae man ya iso ya tada ta tsaye yana fad'in"ya akayi cup d'in ya fashe kuma har kk qoqarin saka hannun ki,da mamaki
tace"hm wnn abar ce fa hk kawae ta biyo tamin muguwar bangaza ta wuce har ma tana fad'in wae zan gani"
Yace"what!
Tace"hm wlh"
A fusace ya kama hanya zai tafi kitchen tayi saurin shan gabanshi tace"no my man kayi hqr ka barta kawae ni yanxu bana son wani tashin hnkli"
Yace"da zanso naji me take nufi da zaki gani"
common my man wnn abar me ta isa tamin ne shirme ne kawae take fad'i kaima ka sani,yi hqr kaji barta.
Tsaki yayi yace "ya zama dole nayi maganin yrnyr nn sbd rainin nata ya fara isata"
Tace"da Allah shareta ta zo muje"
Nan taja shi suka je suka zauna kan two seater malika ta kira cleaners aka kwashe glasses d'in,snn ta kalli man tare da jawo hannunsa ta d'aura kan cikinta tace"my man wae nikam yaushe babyn mu zai fara motsi duk na qagu wlh"
Wani murmushi yayi mae nuna jin dad'i har ransa yace"3 to 4 month ne yake farawa"
Ta kalle shi zata ce wani abu knn wyrta tayi qara tana ganin qawar ta faiza ce tace da mohd "ina zuwa umma ce mae kiran"
Bata jira me zai ce ba ta tafi.
Tana shiga d'aki ta d'aga wyr .
faiza"tace ya ake ciki ne kinsha maganin?
Tace "Aa ynz nake shirin sha dae sbd so nake dai dai wnn abar ta gama min abinci maganin ya fara min aiki sbd zan fi son ina saka loma d'aya ta biyu sae kawae na fasa ihu kan aje asibiti na tabbatar cikin ya gama lallacewa,amma kuma wlh ina tsoron azabar da zanji kafin cikin ya zube
Faiza"ta kwashe da dariya tace"kin fiye tsoro azabar da kwata kwata ta minti nawa ce yayinda ita waccan matsiciyar kin rabata da mijinki har abada"
Tace"wlh kam yau dolenta ta rabu dashi,bari kedai nayi sauri nasha maganin kar taje ta gama abincin bansha ba,tace"ok bye sae mun had'u asibiti knn.
Nan suka katse wyr malika ta ciro tablet a jakarta tasha snn ta fito ta sami man zaune inda ta barshi sae waya yake.
Taje ta zauna kusa dashi tare da jinginwa a jikinsa wanda bae wani jima sosai ba ya gama wayar.
Rynt kuwa da qyar taga ta kammala dafa indomie sbd wani irin bacci da takeji.
Tana gamawa ta zuba indomie a plate ta fito wacce tun lokacinda ta fito kitchen man ke mata mugun kallo har ta qaraso gurin su,shi ya kar6i plate d'in indomie da taikaci yayinda Rynt bata damu da ganin yanda ya kar6i plate d'in ba tayi ficewarta ita dae ta samu ta ganta kan bed.
Rynt na wucewa malika takai hannu zata kar6i plate d'in don har ta fara jin maganin ya fara mata aiki.
Man yace"da zafi malika bari ta d'an sha iska tukun"
Tace"my man yunwa fa nakeji sosai"
Yace"Baza kici da zafi haka ba kam"
nn gabanta ya shiga fad'uwa don in har yace sae abincin ya rage zafi asirinta zai iya tonuwa don gadan gadan ta fara jin maganin na mata aiki.
Nan ta shagwa6e mae tace"pls my man kawae barni naci don zan ma fi jin dad'inta"
Ba musu kuwa ya bata plate d'in ta kar6a ta fara ci tayi loma d'aya biyu a ta ukun ta ajiye plate ta fara riqe ciki man yayi saurin kallonta ya kuma kalli plate d'in indomie yace"lafiya?
Tace"nima dae haka kawae ina fara cin indomie na fara jin cikina yana 6ird'a min"
Yace"what!me tasa miki a indomien ne to?
Bata iya bashi amsa ba sae zamewa tayi daga kan seater tana yarfi da hannu yayinda ta matse cikinta sosai da d'ayan hannunta.
A take man ya rud'e ya jawota jikinsa ita kuwa sae ihu ta fara tana fad'in"wayyo my man cikina zan mutu na shiga uku ka taimaka min da magani nasha"
Da sauri man ya tashi yaje d'akinshi yana shiga ya sami mami kwance kan sofa tayi bacci tana qoqarin fad'owa da saurin sa ya d'auketa ya maida kan bed snn ya d'auko magani da ruwa ya fito yana isowa ya saki magani har cup d'in ruwa sbd ganin yanda malika ta fara bleeding ba wata wata ya d'auke ta ya fita da ita yana qwalawa driver kira,driver yazo suka shiga mota aguje sae asibiti.
Duk wani qoqari na ganin jinin ya daina zuba man yayi amma bai yi nasarar ceto cikin ba ya riga da ya zube,baqin ciki bai bar ya qarasa kula da malika ba sae wata docta yasa ,ya baro asibitin yayo gida a fusace wanda bai zarce koina ba sae d'akin Rynt riqe da belt a hannun shi.
Rynt dake bacci sae saukar duka ta fara ji ta koina.
Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 2/7/2017]
```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```
🔮🔮🔮🔮
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.