Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 31 of 56
*page* *```49```*
Ana sauke Rynt a school sae kawai taji ihun mami tazo aguje ta rungumeta.
cike da murmushi Rynt ke kallonta tace"mami kece waya ya kawo ki?
Washe da baki tace"Abbana ne yanzu ya wuce"
Sae kuma tasha toka tare da fad'in"Anti wae meyasa kika koma gidan inna da zama?
Rynt tayi shiru tana kallonta can tace"to ai dama can gidan inna nake zama ko kin manta"
Tace"Aa ni nafi son ki koma gidan yaya sbd na fi son a riqa kawo mu school tare"
Rynt tace"ai ko ba'a kawo mu tare ba, ba gashi muna had'uwa ba"
Turo baki tayi tace"um um anti hk ba dad'i"
Rynt tace"kinga jeki 6angaren ku za'a fara assembly kar kiyi letti kinji"
Mami tace"to Anti gsky ni sae kin gaya min yaushe zamu koma gidan yaya"
Rynt tace"to kisa ido duk rnr da kika ga raqumi ya shiga akurki kizo da gudu ki gaya min sae mu koma ko"
Da murna mami tace"dgske anti!
Rynt tace"eh"
Mami tace"meye ma raqumi wnn abun mae girma kmr doki ko"
Rynt tace"eh"
Mami ta daka tsalle tace"Allah kuwa da jimawa na ta6a ganin shi hnyar kasuwa,gobe ma zan cewa umma muje kasuwa da na ganshi zanyi ta kallon shi har sae naga ya shiga akurki sae nazo har gidan inna na gaya miki,sae mu koma abin mu gobe gidan yaya ko.
Rynt tayi murmushi had'e da girgiza kanta ta tafi tana fad'in"to naji zan neme ki a break"
Tace"ok anti bye"
5:00pm
Rynt ce ta dawo daga mkrnta ta sami inna a falo duk ta raja'a gun kallo har sallama tayi kusan sau biyu amma bata ji ba, tayi tsaye d'auke da murmushi tana kallon inna snn taje a hnkli kan jikin inna ta rungumeta,
a tsorace inna ta juyo ganin Rynt ce ta sauke numfashi tace"yo Rynh kece aini har kinsa na tashi guduwa ,
Rynt tace"haba dae inna da tsufanki kk shirin guduwa?inna tace"yo ai shi tsoro ba ruwan shi da tsufa "
Dariya Rynt tayi tace"hln ma meya tsorota ki ne inna?
Tace"yo Rynh ina zaune qalau kawae naji an hau kan jikina bayan nsn ni kad'ai ce a falon ban kuma ji shigowarki ba
Tace"to inna ai nayi sallama har sau biyu kece dae bakiji ba sae kallo kike tayi abinki"
Inna tace"ayyo inafa zanji na maida hnkli gun shiriritar banzar nn da ba zata fisshe ni ba"
Murmushi kawae Rynt tayi ta tashi tare da fad'in "inna ni zanje na d'an watsa ruwa"
Tace"to er Albarka sae kin fito"
Nan Rynt ta wuce inna kuwa taci gaba da kallo.
Tana gama wanka ta shirya ta ciro wata baqar leda a cikin jakarta ta mkrnta ta fito ta tafi kitchen sae gata ta dawo d'auke da agwalima cikin bowl.
Taje ta zauna qasa kusa da kujerar da inna ke zaune akai ta d'auki d'aya zata fara sha tare da fad'in" inna ga agwalima"
Inna tace"yo Rnynh ni na d'auka ko abinci ne kika d'ebo"
Tace"Uhm agwalima ce na wanko na d'an sha ko d'aya ce sae naci abinci "
Inna tace"lallai kam ki hanzarta kici abinci kafin mai miki dasarin yazo"
Tace"inna ni idan ma da fura ita kawae zansha ba sae naci abinci ba dan bana jin yunwa"
Tace"to tashi kije ki d'ebo furar tana can a cikin firijin tayi sanyi kuwa.
Ba musu Rynt ta tashi ta d'ebo furar tazo tayi zaune ta shanye agwalimar hannunta snn tasha fura tana gamawa taje ta had'o komai nata na lesson ta fito ta samu inna na kar6a sallama inna na ganinta tace yauwa je d'auko tabarma don inaga mae miki dasarin ne yazo,nn Rynt ta koma d'aki ta d'auko tabarma ta fita.
6angaren mohd kuwa kwance yake a falo shi kad'ai kan 3 seater ya lumshe ido kmr mae bacci.
Da damuwa ya bud'e idonsa had'e da guntun tsaki sbd door bell d'inda yaji ana fmn dannawa kan dole ya tashi yaje ya bud'e qofa, ganin wanda ke tsaye yasa ya d'an saki fuskar shi ya bashi hannu suka gaisa har yana masa ya hanya.
Wanda ba kowa bane face lesson teacher d'in su Rynt wanda tun lokacinda yayi tafiya sae yau ne ya dawo.
Man bai iya bashi hanya ba sae nazarin abinda zai ce masa yake can ya kallesa yace"kayi hqr fa yaran basa nn sunyi tafiya"
Lesson teacher yace"to shikenn amma yaushe ne zasu dawo?
Shiru man yayi can yace"ka tafi kawae dae"
Ba musu lesson teacher d'in yayi sallama dashi ya wuce.
Man ya rufe qofar ya juya ya sami malika a tsaye tace"my man waye ne?
Yace" Lesson teacher ne
Tace"au shi baisan matsiyaciyar tayiwa kanta tsiya ba"
Komai bai ce da ita ba sae zama yayi ya jingina bayansa tare da lumshe idonsa .
Nn taje ta zauna kusa dashi tare da kwanciya kan qirjinsa yace "pls malika im nt in mood n i just wnt me alone ki tafi d'akin ki kinji "
Zata ce wani abu knn yace"pls just go"
Jiki sanyaye ta tashi ta tafi zuwa d'akinta,haka shima ya tashi ya bar falon ya tafi d'akin shi.
2 dayz later
haka mohd ya cigaba da rashin son damuwa komai qanqantar ta kuwa shiyasa ko yaushe yafi son ya kasance shi kad'ai wanda ko asibiti yaje baya wani jimawa yake dawowa.
Rynt kuwa sae karatun ta tasa ma gaba wacce ko yanzu zaune take a d'akinta ta tasa agwalima gaba tana sha yayinda take duba littafan mkrntar ta na boko dana islamiyya ,
kasancewar yanzu ta gyara d'akinta ta dawo ciki da zama sae bacci ke kaita d'akin inna.
Tana cikin duba littanfanta ne taji inna na qwala mata kira taje ta sami inna a falo inna taba ta waya tace"nasiru ne wae ki gaya mae abubuwanda aka ce ku siyo a makrnta.
Nan ta kar6i wyr ta snr dashi snn taba inna wayarta ta koma d'aki taci gaba da duba littafanta.
Ba ita ta tattara littafan ta ajiye ba sae da ta soma jin bacci duk da cewa dare bai wani yi sosai ba don qarfe tara ne a lokacin.
Bathroom ta shiga tayi wanka ta fito tayi shirin bacci cikin riga da wando ta zuba qaton hijabinta ta fito riqe da agwalimar ta guda biyu a hannu.
Nan ta had'u da Nasir ya fito d'akin inna zaije d'akinta hannun sa riqe da farar leda mai hoton littafai da kuma al'amin bookshop a rubuce ta gaida shi ya amsa tare da miqa mata ledar yace "duba kiga littafan ne "
Ta duba tace "eh sune nagode"
Har ya juya zai fita sae kuma ya juyo ya kalleta tayi saurin sadda kanta qasa yace"ki qara hqr kwana biyu kinji ni shiru har yanzu ban sami kaina bane"
Tace"ba komai yaya ai ka barshi kawae sae ka sami lokaci"
Yace"to sae da safe"
Snn ya fita ita kuma taje ta ajiye littafan a d'akinta taje d'akin inna.
Da shigarta ta bud'e fridge ta saka agwalimar ta a ciki.
Washe gari an sauke Rynt a makaranta sae dube dube take ta inda zata hango mami sbd kwana biyun nn duk suna had'uwa da safe idan an sauke su.
Tana cikin dube dube ne sae ga mami ta shigo gate d'in mkrntar da gudu Rynt ta saki murmushi taje ta tarbota tana mae fad'in"wnn gudu haka mami ba kya tsoron kije ki fad'i"
Tace"Anti sauri nake kar baki ganni ba ki tafi don na hango lokacinda aka sauke ki mu kuma muna baya da nisa har ma nayi ta kiranki baki ji ba,
to kince da nisa ya zan jiki mami,
Mami bata ce komai ba sae lunch box d'inta ta ajiye qasa snn ta ciro school bag d'inta dake bayanta ta bud'e ta ciro er wata container rubber mai marfi taba Rynt tace"umma tace na kawo maki"
Rynt ta kar6a takai hannu a hnkli ta bud'e.
Wacce tana bud'ewa qamshi mai dad'i ya daki hancinta nn taga
awara ce wacce taji cabbage da albasa bayan sauce d'in hantar rago da aka zuba akai mai had'e da kayan lambunda aka yanka su slice by slice ta yanda kallo d'aya zakayiwa awarar ka sami kanka da tsinkewar yawu.
Cikin nuna jin dad'i ta rufe snn ta kalli mami tace "kice ma mama nagode sosai kinji"
Mami tace"yauwa anti nifa har yanzu bamu je kasuwa ba bare naga raqumi ya shiga akurki,idan ma nayiwa umma magana se dariya kawae take min,ta qarashe mgnr ne shaye da toka.
Rynt tayi murmushi tace"umma da kanta take miki dariya"
Tace"eh mana"
To yi hqr jeki kar a fara maku assembly"
Daga hk kuwa sukayi wa juna bye bye suka wuce.
10:00pm
Man ne zaune kan bed ya rufe laptop d'inshi ya d'aura kan bedside drawer ya kwanta sae ga malika ta shigo d'akin taje ta kwanta kusa dashi had'e da kai hannu tana shafa sajen fuskar shi har izuwa qirjin shi,
kallonta yayi tare da janye hannunta daga kan jikinshi ya kashe wuta had'e da juya bayan shi,nn yaji ta matso gab dashi ta rungume shi ta baya
yace"pls malika bana son damuwa kin sani,ki matsa kusa dani bana son jinki a bayana.
Kmr kazar da qwai ya fashewa ta jaye jikinta daga nashi.
Billy Giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```
🔮🔮🔮🔮
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.