Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 3 of 56
_*page*_ ```20```
Zumbur umma ta miqe tace"haba Alhj! ni na d'auka ko zancen arziqi ne zanji ashe na tsiya ne.... Kina da hnkli shi zancen aure ne na tsiya...yo zancen tsiya man idan ba haka ba meye had'in mohd da wnn yrnyr er matsiyata er qauye ga 'ya'yan manya a gari,haba dan Allah! ,dan Allah Alhj ni ka ma daina wnn zancen.
Baxan daina sa ba kuma aure tsakanin mohd da Rynt kmr anyi an gama ne, ai bake keda iko dani ba haka shima ba ajiye ni yayi ba da ko yaushe na masa zancen aure se yace tukuna sbd ya maida mutane en iska shasha.... Amma alhj tsakani fa da wnn cutar dashi kake sonyi ai gwanda ya zauna ba aure da ace wnn yrnyr ce matar sa sae kace bakin uwa a rasa wacce za'a ce ya aura sae ita haba dan Allah!
Mtsw sae yau na fhmci rashin hnklinki ne kika yarfawa 'ya'yanki da kaf famlyn nn ba wanda yayi rashin mutuncin su ,na dai ji amma nikam sam bazan yarda da wnn zancen ba don wlh bazata sa6u ba wai bindiga a ruwa.
Fuuu!Abba ya fita yana mai fad'in"tsakanin ni da ke sae aga wanda keda iko akan wani .
Bai zarce koina ba sae downstairs ya samu still mohd na kan cin abinci
yace da mohd idan ka kammala cin abincin ka same ni a d'aki.
Nn take mohd ya kammala cin abincinsa yaje ga kiran Abba.
Abba ya kalli mohd da ya nemi guri ya zauna a qasa yace"mohd ina son ka saurare ni da kyau kaji,kuma bana son kazo min da wani shashanci, zancen auren ka shin har yanzu baka sami wacce ta maka bane ko yaya? Aa Abba dama malika nake jira ta kammala karatun ta kuma ta kammala yanzu ni a shirye nake inshaAllh, Abba yayi shiru na tsawon lokaci can yace"er gidan wacece ita malika? ba wani bane Abba sananen mutum ne wato Alhj ilyas na Allah..... Alhj ilyas na Allah ,yace"eh Abba da wata matsala ne? Abba da yayi shiru yana mai nazari yace"Aa ba komai jeka"
Cikin farin ciki mohd ya fito ya sami Rynt ta fito kenan tana neman shi.
Yayi tsaye daga inda yake har ta qaraso gurin shi ,ba yabo ba fallasa ta miqa masa wyr tare da fad'in"ngde" snn ta juyo tayi ficewarta.
Bayan kwana biyu da faruwar haka ne Abba ya sake kiran mohd.
Yace"mohd a gsky zancen aurenka da wnn yrnyr malika sae dai nace kayi haquri sbd ba er mutunci bace kwata kwata shiyasa tun lokacin da ka snr dani waye mahaifinta na shiga nazari dmn nasha jin cewa baya ganin kowa da mutunci,sae gashi kuwa da mukaje hakane ta faru damu,dmn wasu banzan sharudda ya shiga snr damu kan auren ka da er sa wad'anda sam hnkli ba zai d'auka ba,don haka tunda ersa ba er gwal bace ka haqura da ita.
Mohd da tun lokacin da Abba ya fara zancen sa yaji zufa na karyo masa.
cikin rawar muryar yace"Abba malika yarinya ce mai mutunci kayi haquri kabar ni na aureta tunda ba cewa yayi bazai bada aurenta ba"Abba ya kalle sa kafin yake cewa
"wae mohd ka koji irin maganganun da yake fad'a ne da kowanen mu sae da ya fito cikin 6acin rai wai ace hatta mahaifinku sa'eed da Allah yayi masa sanyin hali matuqa sae da yayi magana kan rashin mutuncin Alhj ilyas na Allah,
gaskiya da sake don nikam baza ka kwaso min er gidan Alhj Ilyas na Allah ba ,koda kuwà ace ita kad'aice 'ya a duniya tofa sae dai ka hqr don baza ka aureta ba.
Komai mohd bai iya cewa da mahaifinsa ba sbd gabad'aya lissafi ya kunce masa .
Abba yace"gaka mohd ina wnn yrnyr Rynt er gidan inna? eh Abba ,to na yanke hukunci zan aura maka ita don wlh ta kwanta min arai kuma inaji a jikina ita alhairi ce a gare mu, cikin tsananin mamaki ya kalli Abbanshi yace"Abba wnn yrnyr fa kace"
eh wnn d'in nn itafa Rynt ba.....ina Abba wlh ni bazan iya aurenta ba kawai dai ka bani dama wlh zan saisaita tsakanin ku da Abban malika, hm mohd kenan kaje dai kayi nazari akan aurenka da Rynt amma malika kam sae dai ka haqura da ita.
Tashi ka bani guri!
Da qyar mohd ya iya tashi ya bar gurin don gabad'aya jikin sa ya mace.
Ya tafi 6angaren sa cike da tunani kala kala a ransa ya zauna kan sofa tare da dafe kansa ,can kmr wanda aka tsakura ya zari makullin motar sa ya fita.
Wani katafaren gida ya nufa yayinda anguwar ta kasance very cylent ,ya parkar a bakin gate d'in gidan snn ya d'auko waya ya kira malika ,yana gama wyr ya d'aura kansa kan sitari ba jimawa sae gata ta fito cikin wani banzan dressing awa arniya ,kyau kam ba laifi akwaishi haka ma qirar jiki Alhmdlh kamar ita tayo kanta.
Cikin isa da yanga ta shiga motar tare da fad'in "my man ya baka shiga ciki ba ka tsaya a nn kmr wani baqo?
Mohd ya d'ago yana kallonta da idanuwansa da suka rine zuwa ja,yace cikin harsh voice"malika meyasa mahaifinki zai mana haka!"ta kauda fuskar ta gefe inda cikin sanyin murya tace"kayi hqr my man wlh nima banji dad'in abinda Abbana yayi ba,kasan hlin Abba sae a hnkli ,ba kace ga wanda yake mutunci dashi ba kowa ciwa mutunci yake..... Gud! ai gashi yanxu ya jamana baza mu auri juna ba ....ta zaro ido tare da fad'in "haba my man me yayi zafi haka? Sae da ya watsa mata mugun kallo kafin yake cewa"hln su iyayena duwtsu ne ko kuma basada zcy a qirji da Abbanki zai gaggaya musu maganganu ransu bai 6aci ba!,calm down my man sharudda ne fa ya kafa musu ba maganganu ya gaggaya musu ba,wane sharudda ne wai?tayi shiru tana kallon shi ,yace cikin d'aga murya "ki gaya min mana!kukan shagwa6a ta fashe masa dashi tace"nidai kayi haquri ba sae kaji ba wlh ba dad'in ji kuma don Allah ka ajiye zancen ba aure tsakanin mu wlh i cnt be wit a u,
yace"malika ke da sauqi ma shin kinsan chakwakiyar da nake ciki ma ta had'ani aure da ake shirin yi da wata banza can er qauye !
A rikice tace"bangane ba"baza ki gane ba kam tunda mahafinki ya 6arar mana da lissafi.
Ta wani marairai ce fuska tace"don Allah kamin bayani wlh ban fhmta ba"yace"malika Abbana ya hana min aurenki sbd zafin abinda Abbanki ya musu shine har yake qoqarin had'ani aure da wata kucaka,Komai kasa ce masa tayi sae kallon sa take hawaye na fmn zarya kan kumatun ta yace"take it easy don ko mutuwa nake bazan auri wnn yrnyr ba,abu d'aya nake so dake yanzu shine kisan yanda zakiyi Abbanki ya bawa iyayena haquri ya kuma janye banzayen sharuddansa to idan kika yi haka inshaAllah Abbana zai haqura.
Share hawayenta tayi tare da fad'in"shikenan my man inshaAllah i will try my best"
Kusan kwana hud'u amma malika ta rasa ta yanda zatayi ta shayo kan mahaifinta don ta sanshi kaifi d'aya ne in ya fad'i abu tofa shikenan.
Mohd kuwa kullum bayada aiki sae na roqon Abbansa kan yayi haquri ya janye aurensa da Rynt amma sam yaqi .
Rynt kuwa kwata kwata bata ma san da zancen ba ga soyayyar ta da munir sae abinda ya qaru wanda yanzu munir jiran dawowar inna kawai yake dmn ya snr da ita abinda ke tsakanin sa da Rynt ya kuma snr da ita yana so zai aure ta.
Mohd ne durqushe a gaban iyayen shi kmr kullum yazo bada haquri a janye zancen aurensa da Rynt Abba yace"bafa zan janye ba idan har kaga na janye tofa lallai inna ce ta buqaci haka"haba Alhj gaskiyar magana kana son takura yaron nn ai kasan halin inna zama d'aya take amincewa da duk wani zancenka,kawai kar ma ka snr da ita zancen nn dan Allah ka bar yaron nn ya auri wacce yake so...na barshi ya auri wacce ya keso ai inace kinji abinda uban nata ya mana wae har mu yake cewa yaji ya amince zai bada er shi ga d'anmu amma fa mu sani shi er shi ba tunkiya bace ko akuya da zata je tana haifawa d'anmu 'ya'ya barkatai kmr yanda yake ganin a familyn mu ana haifo mana 'ya'ya hkn nn ba tsari,shi a tsarin sa bazai wuce ace ersa ta haifawa mohd 'ya'ya biyu ba idan ba haka ba tofa sae dai d'anmu ya haqura da ersa,wnn wace irin magana ce babu dad'in ji snn har kike tunanin zan amince na had'a surukuta dashi.
To Alhj sae akace don ya fad'i tsarin sa shi zai sa dole abi ,muradi kawai ersa ta shigo hannun mu ,mu kuwa sae yanda mukayi da ita tunda ta rigada ta dawo a qarqashin ikon mu..... Sam bazan yarda da auren da za'ayi ana dinga ci min mutunci ba, dmn nida shi ba wanda zai nunawa wani kud'i ba kuwa zai zo yana dinga nuna min iko ba don kawai d'ana yana auren ersa!
Cikin damuwa sosai mohd yace"don Allah Abba kayi haquri wlh a guna ba matsala ai yara biyun ma sun ishe mu jin dad'in rayuwa.....kul!na qara jin zancen nn ya fito a bakin ka!kuma maganata ta qarshe shine ba zan janye aurenka da Rynt ba wlh,sae idan ita Rynt d'ince ta furta da kanta cewa bata sonka, kuma ko bayan raina ban yafe maka ba idan ka auri malika!
Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:43PM, 5/2/2017] Billy giro😊: 🔮```BAZAN BARSHI BA! ```🔮
🔮🔮🔮
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.