Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 23 of 56
*page* *```41```*
Ta rufe qofa tare da zamewa jikin qofar ta had'e kai da guiwa tana ci gaba da kukanta.
Mohd kuwa juyawar sa yayi zai fita d'akin sae ga mami ta shigo riqe da hijab, school bag, da takalmi da socks ta jefarda su kan sofa ta riqo hannun sa tare da kallon fuskar sa snn tace"yaya anti ta gaya maka me take ma kuka?
Yace"bata gaya min ba ko kinsan me take ma kukan ne"
um um nima ban sani ba kawai na ganta tana kuka"
Bai sake cewa komai ba sai hannunta yaja suka tafi downstairs ya kira kuku ya kawo abinci plate biyu mohd ya kar6a yaba mami d'aya ya tashi ya nufi d'akin Rynt da d'aya.
Wanda yana shiga d'akin yaga giftawar Rynt ta koma bathroom, ya ajiye abincin yabi bayanta .
Yana tsaye ta cire hijb da riga takai hannu zata cire vest kenan ta hango shi ta jikin mirror ai kuwa ta buga ihu had'e da kare qirjinta ta duqe qasa tana fad'in ya fita! bai fita ba sae bayan banta yake kallo da duk ya kasance d'auke da shatar bulala,rai 6ace ya tayar da da ita tsaye ya juyota yana kallon fuskarta snn yace "wane d'an iskan malami ne ya dake ki haka!
Shaye da toka ta sake juya mai baya tace"to ni ka fita ai zan zo na maka bayani ne"
Fixgota yayi ya sake juyo da ita yace"bana son raini wlh gaya min wa ya dake ki nace!ko kuma iskancin da kike min ne suma malamman kika je kina musu,kut!zaki daina bokon nn ne wlh tunda ba kya ji,tayi saurin kallon shi le6ace da baki zuwa kuka tace"wlh Aa shine yake takurani kullum wae shi a dole sae naje office d'insa..... What! kije office d'insa fa!
tace"eh wlh hk kullum yake aikowa ni kuma bana zuwa shine yau yaje har class d'in mu ya same ni yana gaya min wae shi sona yake shine na mai tsawa nace ya fita haraka ta ni ba irin en matan nn bace shine kawai ya sami bulala ya daken"
Cikin mugun 6acin rai ya damqota kafad'unta yana kallon fuskarta yace"kinga bana son qarya fa!meye abin so a tare dake da zai wani nace miki!
kawai dai kin mae iskanci kmr yanda kike min ko!
Tace"wlh gobe ma kaje ka tambayi en class d'inmu kaji"
Ya nunata da yatsa snn yace"idan na samu laifin ki ne fa"
Tace"kawai ka cire ni daga bokon"
yace"yayi kyau Allah kaimu goben"
Nn ya tafi awa zai tashi sama ita kuma ta rufe bathroom d'in ta watsa ruwa ta fito tayi sallar zuhur.
Washe gari Friday tun safe yazo d'akin Rynt yace da ita"mami kad'ai zaki yi ma shirin school bada ke ba"kmr zatayi kuka tace"meyasa? yace"sae na gama bincikena tukun"
Ajiyar zuciya ta sauke tace"to"
Har zai fita sae kuma ya juyo yace"ya sunan malamin?
Tace" malam a shaqata....
bana son raini sunan sa na qwarai zaki gaya min,to ni ban sani ba ai da haka kawai nake jin ana kiranshi,
Tsaki kawai yayi tare da fita d'akin yana fad'in"zai shaqata a cell don ubanshi"
4:05pm
Rynt ce zaune ta gama sallah wacce tun sha biyu da mami ta dawo school take jiran shigowar man amma taji shiru sae roqon Allah take kar malamin ya lauye ta bokon ta ko ya sami matsala tana cikin hakane sae ga man ya fad'o d'akin yaje kan bed ya zauna ya tasa ta gaba yana kallo sae can ya girgiza kai yace"kin rainani ko?a rikice tace"me yace maka ne wlh ko mene ne qarya ya maka"
Yace"kinga yi min shiru! Dan ubanki ashe ba kya saka niqabi cirewa kike idan kinje school!
A d'an daburce tace"ni kuma"
Yace"akwai wata ne banda ke to bari kiji bake ba bokon nn kuma wlh ba inna ba ko Abba zaki kai qarata agunshi baza kiyi nasara ba kuma ki gwada ki gani shege ka fasa!
Nn ya tashi zai fita ta tashi da hanzari tasha gaban shi inda cikin marairaicewa tace"kayi hqr dan Allah"
Tsaki yayi ya tureta ya wuce wanda har yakai bakin qofa ya mird'a handle tasha gaban shi tare da riqe handle d'in tace"kar ka fita dan Allah kabari nama bayani"
Yace"wane bayani kin tallata fuskar ki kuma kin samu an yaba sae kuma me!
Tace"bafa haka bane wlh en makarantar ne suka takurani suna ta magana akai shine na cire"
Gud idea kin kyauta ma kanki.
Oya!bani hanya na wuce!
Tace"nidai don Allah kayi haquri ka barni na ci gaba da boko na"
Yace"kije su da suka saki daina sa niqab d'in su maida ke makarantar very stupid!
Nn ya mird'a handle zai fita tasa hannunta duka biyu ta riqe tana roqon yayi haquri,
A fusace ya d'aga hannu zai mareta tayi saurin sake handle d'in ta kare fuskarta cike da tsoro had'e da fashewa da kuka tana bashi hqr,bai marenta ba sae ture ta yayi daga jikin qofa ya bud'e qofar ya fita.
Haka Rynt tayi weekend cike da damuwa ganin bakin rai bata zuwa school mami kad'ai ake kaiwa haka ma lesson ana gama ma mami lesson teacher ke tafiya .
Rnr lahadi da qarfe hud'u tana jin mae lesson yazo ta had"a komai nata na lesson taje tayi zaune falo ta fake yana gama ma mami tazo zata zauna ya kwashi kayansa yace"kiyi hqr yace qaramar nn kawai za'a ci gaba da yi ma lesson "
gyad'a mae kai tayi tana mai danne hawayenda ke qoqorin zo mata.
Zata haura sama kenan taji fitowar man yana magana a waya taje gurin sa ta tsaya tare da sadda kanta qasa yana gama wyr yace lafiyar kin wani zo kimmin tsaye ,hawayen idonta kmr zasu zubo take kallon shi tace"don Allah kayi haquri ka barni naci gaba da karatuna kaji"
Kallon ta kawai yayi yace"naji amma je ki gyara min d'akina"
Da sauri ta fiddo ido waje tace"cab! Allah sauwaqe wlh bazan sake gyara ma d'aki ba"
Ya kalleta da kyau yace"ke me kike nufi ne to idan har ma wnn abun kike tunani ki cire dmn sanin kanki ne qaddara ce ta afka min a wnn rnr ina kuma roqon Allah da kar ya sake had'a ni da irin wnn qaddarar,cikin 6acin rai mai had'e da muryar kuka tace"ai dole kace haka tunda ka gama cutar dani,mugu kawai wlh bazan barka ba!
Nn ta fashe da kuka ta tafi da gudu tabar shi nn tsaye cike da mamakin yanda renin wayonta ke qaruwa a kanshi,sae jin yayi malika ta rungume shi ta baya tare da fad'in "my man albishirinka" ya kalleta d'ai ,ita kuma ta rad'a mai magana a kunne da tasa shi wani irin matsanancin farin ciki kai tsaye ,
ya ta6o cikinta yace"dagske malika! tace"wlh kuwa my man muje ma ka duba a PT strip"
Nn yaja hannunta cike da farin ciki suka tafi d'akin shi.
Bayan sllr isha'i Rynt ta gama sallah d'auke da hawaye a fuskarta tana tunanin hanyar da zata bi ta samu taci gaba da bokon nn don dai kam koda kuskure bata son ta sake zuwa d'akin man bare har yayi galabar sake cutar da ita.
Tana cikin hkne taji qarar bud'e gate ta tashi a hnkli ta yaye labulen windonta ta hango motar man ce ta fita ta saki labulen tana mae tunanin idan har zai barta ta koma school in ta gyara mae d'aki ,gwanda kawai tayi sauri taje ta gyra mae kafin ya dawo nn ta kalli mami dake kallon tom and jerry tace"mami muje ki rakani a d'akin yayanki sae ki kunna kallon ki a can kinji"
Ba musu mami ta tashi suka je Rynt ta gyare koina tsaf cikin en mintinan da basu fi 30 ba wacce har ta gama gyara d'akin gabanta na dukan uku uku.
Tana gamawa taja mami suka koma d'aki.
Sae bayan awa 1 da komawar su d'aki ne taji qarar bud'e gate ta tashi ta duba taga motar man ce ta kunno kai.
Byn an parker motar driver ya fito da sauri yaje ganbun baya ya bud'e ya kuma zagaya da sauri ya bud'e d'ayan,nn man da malika suka fito kowannen su d'auke da fara'a a fuskar shi man ya riqa hannun malika suka shiga gida yayinda driver ya bisu da kaya niqi niqi.
Rynt ta saki labulen ta koma ta zauna.
Har sha d'aya na dare Rynt batayi bacci ba sbd jiran ko man zai shigo idan yaga ta gyara mae d'aki amma shiru kmr shirwa ta cinye d'an tsako.
Gashi sosai take jin bacci amma tasan ko ta kwanta bazata iya yinsa ba idan ba taji, ko zai barta ta koma school ba.
Har sha biyu shiru bai zo ba, gata kwance amma fir bacci yaqi d'aukarta sae juyi take, ta kalli gefen mami da tuni tayi bacci abinta ,ta tashi zaune tare da had'e kai da guiwa sae jin tayi an bud'e qofa tayi saurin d'ago kanta yayinda hawaye ke silalowa a hnkli kan kumatun ta.
Man ne ya shigo yayi tsaye a bakin qofa yana kallonta ita kuwa sau d'aya ta kalle shi ta kauda fuska tare da share hawayenda suka zubo mata ya qarasa cikin d'akin yaje kan bedside drawern da ke kusa da Rynt ya zauna snn ya kalleta ba yabo ba fallasa yace"lafiyarki kike kuka da daren nn"
Tace"kace idan na gyara ma d'aki zaka barni na koma school ko"yace"yaushe nayi dake haka? kmr zata yi kuka tace "d'azun kmr hk fa ka nuna min"
A tunanin ki kenan amma ni ba hk bane,ya fad'i hkne tare da kallon fuskarta sae yaga nn take hawaye sun zubo mata nn yaji ta burge shi sosai sbd yanda take son karatu.
ya sauke numfashi snn yace"zan barki ki koma d'in amma fa da sharad'i"da sauri ta kalle shi tace"ina jinka gaya min"
Yace"Duk kika bar wani malami ya sake fad'awa sonki ko wlh bake ba makarantar koma nace gabad'aya bokon don ba kud'in banza nake dashi da zan kai ki karatu kije kina soyayya ba idan kuma har kince soyayya zakiyi ni kinma hutar dani kuma kin hutar da kud'ina don sallamar ki zanyi ki koma can gidan inna da taji zata iya.
Rynt ta sauke ajiyar zuciya tace" naji zan kiyaye,yace"idan ma kin kasa kiyayewa wa kanki,
Nn ya fita tayi hamdala wa ubangiji ta kashe wutar d'akin ta kwanta.
Washe gari da taje school wata qawar ta da suke shiri sosai take ce mata
"bari Rynt yanyanki yayi wlh don naji dad'in da yasa aka kori malam a shaqata daga mkrntr nn shikenan yanzu mun huta da muguntar shi"
Rynt tace"hm korar sa yasa akayi?au bai gaya miki bane? tace"um um"
Hm bari kedai naso ace rnr Friday d'in nn kinzo wlh don qaramin yaqi aka tashi yi a makarantar nn dmn en sanda fa yayanki ya kiro mishi yace a tafi dashi sae da qyar principal ta shawo kan yayanki a cewar yayi hqr kar yasa a kama shi zata sa ayi mai transfer zuwa mkrntr maza don dama ta jima da jin wasu halayen shi maras kyau da ake fad'i.
Rynt ta kalli qawar ta tace"to a bakin wa yaji cewa bana sa niqab hln?tace"gsky ban sani ba kawai dai munji hayaniyar fad'an su ne"
Qawar tace"amma yayanki yayi aure ko? Rynt tace"eh"
tace"kai amma fa ko waye matarsa tayi sa'ar miji kuma kema kinyi sa'ar yaya"
Ta6e baki kawai Rynt tayi ta jawo littafinta tana dubawa sbd haka take ko yaushe ko ba test idan dai basa komai a aji ,bazatyi strn banza ba sae dai ta jawo littanfanta tana karatu.
5:00pm
Rynt ce da mami sun dawo daga school suka sami malika da mohd zaune a falo ,malika nata zubawa man kukan shwaga6a wae ita yunwa takeje bata iya cin abincin kuku don ko warinsa bata son ji.
Tana ganin su Rynt sun shigo tace"yauwa my man kasa wnn abar ta dafa min abinci wata qil ko zan iya cin nata.
Rynt na jinta taji sa6o ma take bata dai kula su ba tayi ficewar ta ita da mami.
Shi kuwa mohd kmr ma ince tare suka shigo d'akin shida su Rynt ,
Ya kalli rynt dake qoqarin ajiye school bag yace "ke yi sauri ki cire uniform kije ki d'aurawa malika abinci"
Rynt ta ta6e baki tace"hm wae sa6o idan bazata d'aurawa kanta ba ai sae ta zauna da yunwar"
Yace"bana son raini wlh maxa ki cire uniform kije ki d'aura mata girki "
Tace"wae ya zaka ce na d'aura mata girki wane irin ma rashin tausayine ynx daga dawowata daga mkrnta"
Yace"haka zaki ce to bari kiji idan har kina son ci gaban karatunki to fa lallai sae kinyi abinda nake so wlh"
Tace"naji amma bafa zan d'aurawa qatuwar banza girki ba"
Yace"well ya rage naki idan kina son ci gaban karatun ki kije ki d'aura mata girkin idan kuma ba kya so ba dole sae kiyi zamanki.
Billy Giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [2/2/2017]
```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```
🔮🔮🔮🔮
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.