Complete Hausa Novels

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 38 of 56

*page 76*

Malika ce ta kirashi wacce tana gama waya dashi ta kalli qawar ta faiza dake tsaye kusa da ita a bakin gate ta rakota, tace"kinji my man a cikin kwanakin nn zae dawo amma wae sae yaje Germany tukun"

Faiza tace"yin me kuma?

Malika tace"mtsw ni bansan uwar me zae je yi ba wlh yanda na matsun nn ya dawo har ji nake kmr nayi tsuntsuwa naje na same shi amma shi na fahimci kmr ma sam ba missing d'ina a tare dashi sae harakar gaban sa da yake"

Fa'iza tace" haba ae kinsan dole yana cikin missing d'inki tunda shi ba qarfe bane,amma keda kike tare da switat d'inki yana d'an d'ebe maki kewa meye na damuwa"

Malika ta dalla mata harara snn tace"kinji ki nifa manage kawae nake dashi wlh don baza a ko ta6a had'a my man da shi ba, dmn my man qarshe ne gurin iya sarrafa mace samun irinsa a cikin maza sae an tona, shiyasa ko a mafarki bana fatan ganin rabuwa ta dashi.

Faiza tace"hm ae kuwa tunda kika koma a ruwa kina cikin had'ari dan duk rnr da man yasan kina tare da wani d'a namiji bayan shi sunanki sorry"

Malika tace"hm fa'iza knn hkn ma ba zae ta6a faruwa ba,don bazan ta6a sakacin barin sa har ya gano ni ba,dan haka kima daina min baki"

Fa'iza tace"hm ni ba baki na miki ba idan dae zaki daina to walillahi hamdu ni kinga tafiya ta sae gobe idan kin shigo, kuma dan Allah karki 6ata mana lokaci don nasan halinki da baqin African time kmr akan ki aka fara.

Malika tace"to naji"

Daga haka ta juya ta koma daga ciki yayinda fa'iza taja motar mijinta da tazo da ita ta bar layin.

Man kuwa yana gama waya da malika ya koma daga ciki yayi tsaye yana kallon Rynt sae ci gaba take da baccin ta.

Guraren qarfe biyar tuni Ryynt ta tashi suna zaune gefen gado ita da man wanda ke rungume da ita yana ciyadda da gasasshiyar kaza da fresh milk.

Ryynt bata wani ci sosai ba tace ya isheta.

man yace"No Ryynt ki d'an qara ko kad'an ne kinji"

Tace"um um ya isheni sae anjima ko zan qara"

Bae ce mata komai ba sae sauran fresh milk d'inda ke cikin cup ya qarasa shinyewa ya ajiye cup yana mai kallon yanda ta d'aura hannunta kan cikin ta nn shima ya d'aura hannun sa akan cikin nata yana mae kallon fuskarta da kulawa yace"mene ne?

Murya can ciki tace"ba komai motsi kawae yake min"

Mohd ya shafi cikin yace"motsin ae ba zafi koh?

Tace"um um babu zafi akwae damuwa dae"

Yace"shi motsin?

Tace"eh mana ni ban so"

Mohd yayi d'an nurmushi yana kallon Ryynt wacce ta qarashe zancen ne cikin shagwa6a.

Bae ce mata komai ba sae shafa cikinta da ya ci gaba dayi ita kuma ta lafe kmr mae bacci tana shaqar daddad'an qamshin turaren sa.

Sukayi shiru tsawon lokaci abinsu d'akin yayi tsit kmr ba kowa sae can mohd yaje zuwa janye jikin sa a hnkli Ryynt ta d'ago ta kallesa tace"fita zakayi?

Yace"eh zan fita ne me kike so?

Tace"zan bika"

Yace" yi haquri bari idan jikin ki yayi sauqi sosai sae mu fita koh"

Ba musu ta gyad'a masa kai shi kuma ya d'aura mata kiss kan goshi ya tashi tare da fad'in sae na dawo"

Ryynt tace"Allah ya tsare min kai"

Mohd ya tsaya cak ya dawo ya zauna yana kallon ta d'auke da murmushi yace"dan Allah maimai ta min me kika ce"

Ryynt ta sadda kanta qasa d'auke da murmushin jin kunya tana wasa da zoben yatsar ta wacce cikin murya can ciki mae dad'in sauraro tace"nace Allah ya tsare min kae"

Mohd dake kallonta sae yaji ya qara sonta cikin jin dad'i ya d'ago fuskarta d'auke da murmushi ya d'aura mata kiss kan lips yace"Amin my Ryynt ina sonki Allah ya bar min ke"

D'auke da murmushi tace"Amin"

Ta bisa da ido har ya fita snn ta kwanta tare da janyo pillow ta rungume a hnkli had'e da lumshe ido tana murmushi.

Sae da ya d'an jima kafin yake dawowa ya sameta zaune falo ita da mtr Amir sae fira suke abin su suna kallo,

Ryynt ce ta fara ganin sa,

ya sakar mata murmushi ta mayar masa yayinda take kallon ledodin da ke hannun sa tana son tashi ta tarbo sa amma kuma tana jin kunyar matar Amir wacce ta shiga gaisawa dashi,suna gama gaisawa da ita ya shiga daga ciki ita kuma ta kalli Ryynt wacce ke zaune abinta ba alamar zata tashi,ta saki baki tace"Ryynt ya haka mijinki ya dawo ba sannu da zuwa kuma ba alamar zaki je ki tarbe sa kika bar sa da kaya a hannun sa har ya shige"

Ryynt tayi murmushi kawae ta sadda kanta qasa, mtr Amir ma tayi murmushi had'e da girgiza kanta ta miqe tsaye d'auke da Sadiq da yayi bacci tace"in dan nice nikam kinga ma tafiya ta"

Ryynt tace"Aa dan Allah yi zamanki"

Matar Amir tace"kinji ki da wani zancen kedai sae anjima Allah ya baki lafiya ya kuma tsare gaba"

Ryynt tace"Amin"

Matar Amir ta fita ita kuma ta shiga daga ciki.

Man dake tsaye jikin wardrobe sae jin yayi ta rungumo sa a hnkli ta baya tace"sannu da zuwa"

Ya juyo d'auke da murmushi ya shafo fuskarta yace" sannu my Ryynt ya jikin naki"

Tace"Alhmdlh bana jin komai sae zafin allurar da ka matse ni aka min"

Tayi mgnr ne tana kallon sa d'auke da yanayin shagwa6a a fuskarta.

shi kuma ya lakato hancin ta yace"to ai kece kika qi tsayi sae kuka da kike tayi kina qoqarin guduwa sae kace kinga mae d'aukar rae"

Ta turo baki a shagwa6e tace"to ai zafi ne da allura gashi har yanzu sae zafi take tamin"

Yace"to yi hqr bari na qara murza miki sae ta daina miki ciwo koh"

ya fad'i hkne yayinda ya qara janyo ta zuwa jikin snn yakai hannun sa a bayanta yana murza mata gurin ta yanda gurin zae yi saurin watsewa.

Ryynt tace"wash"tare da qara qanqame shi snn tace"uhm uhm ciwo kamin a hankali"

Ya qara rungume ta yace"sorry kar kiyi kuka kinji hkn zae fi saurin watsewa"

Nan yaci gaba da murza mata gurin ita kuma sae wash take fad'i tana qara shigewa jikin sa har ta fara masa kuka.

Kan dole mohd ya barta ya d'ago fuskar ta sae rarrashinta yake yana share mata hawaye yace"is ok kukan ya isa haka muje na nuna miki wani abu da na siyo miki.

Nan yaja hannun ta sae jin dad'i take taga mene ne.

Kan bed ya fara zaunar da ita snn ya jawo ledodin da ya shigo dasu ya ciro wata er qaramar leda mae d'an akwatiñ sarqa a ciki ya bud'e

ya ciro wata dakakkiyar sarqar diamond simple design mai matuqar kyau iri d'aya da zoben da ya saya mata.

Wani irin dad'i Ryynt taji har ranta ta qar6i sarqar tare da qanqame sa tana masa godiya yayinda man ke kallonta d'auke da murmushi

tace"ya naga iri d'aya da zobe na?

Yace"wlh nima haka kawai yau ina komawa shagon da muka siyo zoben nagan su wae ashe kowane zobe idan kana ra'ayi akwai sarqar su har ma da abun hannu, rigimar ki ce bata bar na fahimta ba"

Ya qarashe mgnr ne cikin zolaya tare da kai hannu a cikin aljihun wandon sa ya zaro bracelet yace"kinga abun hannun har dashi na siyo maki"

wani irin dad'i Ryynt taji fiye da na farko ta kar6i bracelet d'in tare da qara qanqame shi tana zuba mishi godiya man kuwa sae kallonta yake cike da so yana murmushi dmn yanzu bashi da wani burin da ya wuce yaga Ryynt cikin farin ciki ako yaushe.

Da kanshi ya saka mata sarqa da en kunne da kuma abun hanun ya jata sukaje gun mirror a nn fa ta kasa rufe bakinta dan sarqar ta mata kyau ba kad'an ba har ma ta rasa ta yanda xata qara gode mishi sae hugging d'in sa da ta qara yi tare da masa peck ,

shi kuma ya d'auke ta cak yana juyi da ita kmr wata er baby sae qyalqyatar dariya take har ya kaita kan bed ya sauke.

Washe gari da dare bayan sunyi shirin bacci suna zaune kan bed manne da juna suna cin popcorn suna kallo cike da nishad'i ,

man ya kalli Ryynt wacce ta kwantar da kanta a kafad'ar sa,yace"gobe kad'ai fa muke a garin nn inshaa Allah don haka gobe da safe sae ki shirya muje ki siyo en tsaraba"

Ryynt ta d'ago fuskarta tana kallon sa tace"to Allah kaimu goben,su maman Sadiq fa yaushe zasu koma ko a nn zamu bar su?

Yace"No ae Amir ya kammala abinda yazo yi tare zamu koma har ma Germany duk tare zamu je muyi kwana biyu sae mu wuce Nigeria.

Daga haka sukayi shiru Ryynt ta jawo wayarta ta soma chart man dake kallon ta ya kar6e wayar yace"baki san cewa idan ana tare da mai gida ba ba'a yin chat lokaci ne da zaki bashi kulawa"

Ya qarashe mgnr ne yana murmushi ita ma tayi murmushi tace"yi haquri ganin nayi wae ba ma yin komai sae kallo kuma ni na gaji da yin kallon"

Sae da ya kashe TV snn yaja hancinta yace" to ai nima na gaji da yin kallon sae kimin fira mae dad'i inji"

Tace"uhm sae dae idan kai zaka bani labari"

Yace"ke ba kiyi labari ba sae ni Ryynt"

Tace"To ni ina zan sami labari nida ba fita nake ba"

Yace"to ae ba dole sae labari zaki bani ba"

Nan takai hannu a hankali ta shafo cikin sa tace"ni kuwa me zan baka naga dae baka jin yunwa"

Yace"ae ba abinci kad'ai ne abinda mata zata bawa mijinta ba"

Tace"to ni kuwa me nake da shi da zan baka?

A hnkli ya shafo cikinta tare da fad'in"to tunda ba kya da abinda zaki bani ni inada abinda zan baki wanda zan qarawa babyna qwari"

Tace"uhm kmr y......bata qarasa fad'a ba kawae taji bakin sa a cikin nata yayinda yakai hannu ya kashe musu wutar d'akin.

Billy Giro😊

[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [3/25/2017]

```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.