Complete Hausa Novels

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 11 of 56

_*page*_ *```28&29```*

Tsaki mohd yaja tare da ture ta daga jikin shi, kan ta kai qasa yayi saurin tarbota dan sae a lokacin ya fhmci suma tayi,ya kwantar da ita nan qasan tiles ,mami kuwa ta jefar da teddy tazo da gudu gun Rynt ta saki ido tana kallon Rynt dake kwance,

mohd yace"je 6oye teddy ki d'ebo min ruwa"

Mami taje ta maida teddy snn ta kawo masa ruwa ya kar6i ruwan ya shiga yayyafa ma Rynt a fuska,firgigit ta tashi tana ihu tana fad'in"mami ki daina liqa min wnn abun bana so dan Allah"ta qarashe mgnr kmr qaramar yarinyar da zatayi kuka,wacce sae a lokacin ta kula da mohd da ko lokacinda taci karo dashi ta d'auka ko teddy ce,shiyasa ta qara firgicewa har ta kaita ga suma .

Mami tazo gab da ita tana kallon Rynt wacce tayi zaune ta had'e kai da guiwa yayinda jikinta ke ta rawar tsoro ta dafa ta snn tace"anti kiyi haquri kinji bazan sake ba"kafin Rynt tace komai mohd yace da mami,"d'auko min teddyn naje dashi d'akina idan kin buqata sae kije d'akina kiyi wasa a can ko? Mami ta gyad'a kanta tare da tashi ta d'auko mai teddyn ta bashi ya kar6a tare da duqawa zai d'auki agogon sa da ya fad'i kusa da Rynt,dai dai Rynt ta d'ago fuskarta da idanunta ke cike tap da qwallah,ganin teddy a hannun shi yasa tayi saurin matsawa tare da tura masa agogon sa da ta fhmci zai d'auka, sae da ya kalleta snn ya d'auki agogon ya fita.

Mami tazo jiki sanyaye gun Rynt tace"Anti kin haqura ko?Rynt ta gyad'a mata kai tare da share hawayenda suka zubo mata,snn tayi d'an murmushi tace"ba komai ya wuce"

Daga haka ta tashi sukayi shirin bacci suka kwanta.

Mohd kuwa 6angarensa ya nufa yana shiga ya jefar da teddy kan sofa snn yaje ya kwanta kan bed tare da ciro wyrsa a aljihu ya fara latse latse.

Malika ce ta shigo d'akin cikin rgrta ta bacci dani da babu taje kusa dashi ta kwanta tana kallon abinda yake yi a waya, ta kalli fuskar shi snn tace"my man ashe kana game"yace"in tamin dad'i ba"ta mirgino kan jikin sa tare da kai hannu tana shafa sajen fuskar shi tace"my man nifa ban gane ba har mun shigo cikin sati na biyu da aure amma banji kana zancen zamuje honeymoon ba"

yace "malika nida ke son komawa bakin aiki ina kuma zancen wani honeymoon"

ta 6ata fuska tana kallon shi tace"ba wani nn gsky ni sae munje honeymoon tunda ba fina akayi ba"to shikenan zamu je d'in"

kiss ta bashi tare da fad'in "tank u"yayi murmushi yaci gaba da aikin sa kawai,nn malika ta shiga qoqarin hana mishi game d'in don sae wasu abubuwa take mishi a jiki har ta kai ga ta qwace wyr tana qoqarin had'e bakin su, ya kauda bakinsa gefe snn ya koma kallonta sbd buttons d'in rgr sa da ta shiga 6allewa ya riqo hannunta yace"malika wae ke ba kya gajiya ne,naga yaushe yaushe ne muka rabu"

to my man kai d'in na daban ne kasani shiyasa bana gajiyawa da kai"ta qarashe mgnr tare da kashe mai ido d'aya ,yace"to muyi bacci har gobe don yanzu kam ngji"ta wani 6ata fuska tace"gsky nifa ina buqata"

ya salam shine abinda ya fad'a a ransa har ga Allah baya son yawan laluboshi da take wace irin mace ce da tun auransu bata ta6a bashi rana d'aya ya huta ba har yau,nn yace"ok ina zuwa"ya tashi ya fita sae gashi ya dawo d'auke da fresh milk da cups ya kalleta d'auke da murmushi yace"bari musha tukun ko" bai jira amsarta ba ya tsiyaya mata fresh milk ya bata,

har ta shanye cup d'in tas shi bai ko fara shan wacce ya zuba ma kanshi ba,ya kar6i nata cup yace"na qara miki ne? Ta girgiza kanta tare da matsowa kusa dashi ta kwantar da kanta a qirjin sa, daga nn tayi bacci don dama maganin bacci ya zuba mata don kawai ya huta da jarabarta.

Bayan kwana uku da faruwar hakane zuwa honeymoon d'insu ya tashi dan har ma ga gobe zasu tafi shiyasa tun safe yakai malika gidan iyayenta don ta musu ban kwana, Rynt kam bata san abinda ake ciki ba kawai dai kullum da safe mohd na shigowa 6angarenta yaja mami suyi breakfast ita kuma kuku ake aikowa ya kawo mata nata,kuma in banda gaisuwa ba abinda ke had'a ta da mohd.

Zaune suke ita da mami a d'aki kan bed tana koyadda mami karatun qur'ani, ya shigo ya same su ,

Rynt na had'a ido dashi ta kauda kai amma shi still kallonta yake sae ma cewa yayi ki taso keda mami zamu fita, daga haka ya juyawar sa ya fita mami ta bishi da gudu tana jin dad'i.

Koda Rynt ta fito harabar gidan ta samu har sun shiga mota ita kad'ai suke jira,taje ta shiga motar itama.

Basu zarce koina ba sae family house,mami ta tafi da gudu zuwa 6angaren su,mohd kuwa ya nufi nasu 6angare shida Rynt ,

suna shiga falo suka sami Abba zaune ta durqusa ta gaidashi cike da ladabi ,ya amsa mata cikin sakin fuska.

Byn sun zauna da ita har mohd d'in snn Abba yace" nine nace yazo min dake kan wani rashin adalci da naji yana shirin yi da na masa magana se yace kece baki buqaci hkn ba,Rynt ta kalli Abba don ita bata gane inda zancen nasa ya dosa ba, Abba yace"batun zuwan su honeymoon ne shida malika shin kinsan da batun zuwan?

Rynt da batasan meye honeymoon ba illa kawai abinda ta fhmta wani guri zasu, zuwansu da rashin zuwansu kuwa duk d'aya ne a gurinta se tace"eh"

to meyasa baza ki bisu bane ko kuma shi ya hana miki? Aa Abba kawai dai ina son zan koma islamiyya ne, Abba ya kalli mohd yace"to kaji idan ita waccan d'in honeymoon ta buqaci zuwa kaji wnn islamiyya take buqatar komawa don haka sae kayi adalci a tsakanin su"yace"inshaAllah Abba, nn mohd ya tashi ya fita Rynt kuwa ta tashi zata haura sama dmn gaida hjyr su mohd Abba yace"Ai bata nn ta fita,

tafi kawai abinki ku koma gida, tace"to snn ta fita"

Koda ta fito mohd na jingine jikin mota yana jiran fitowar ta,bata nufi gunshi ba sae 6angaren su saliha ta nufa yace"ke ina kuma zuwa?tace " Zanje gaida mama ne daga haka bata jira amsar shi ba ta shige abinta.

Bata wani jima ba ta fito ita kad'ai ba tare da mami ba don dama tun cikin mota da suna kan hnyr zowa tace in sunxo sae dare zata koma.

Tafe suke kan hanya ba mai ce ma wani can Rynt tace"gidan inna fa"kallon ta kawai yayi ba tare da yace komai ba yaci gaba da tuqin sa har suka isa gida.

Da dare ta fito daga wanka mohd ya shigo d'akin riqe da hannun mami ya same ta sanye da qaton hijab d'inta as usual ,ta d'auko Vaseline zata je kan bed ta shafa,ya tsaya bakin qofa mami kuwa taje da gudu gun Rynt snn ya juya ya bar d'akin yana mai jiyo yanda mami ta fara cika Rynt da srt.

Washe gari tunda ya dawo daga masallaci sllr asuba ya tafi d'akin ya samu duk bacci suke da ita har mami kasancewar fashin sll Rynt keyi shiyasa bata tashi sllr asuba ba.

Rynt bata da nauyin bacci ko kad'an shiyasa taji lokacin da mohd ya shigo,yana jin yanda sautin addu'ar tashi daga bacci ke fita a hnkli daga bknta snn ta tashi zaune had'e da blanket d'in jikinta wacce still tana sanye da hijabinta.

Ta amsa masa sallama tare da had'e kanta da guiwa tana mishi ina kwana,ya amsa ba yabo ba fallasa sae kuma ya fita bai ce mata komai ba hkn yasa ta komawarta ta kwanta.

Koda ya koma d'akin shi ,malika na kwance bata tashi ba sae sharar bacci take bayan ba irin tashin da bai mata ba kafin ya tafi masallaci, ya kalli yanda take kwance bata da maraba da tsiraici sbd gabad'aya abin rufan ta kad'an ya saura ya sauka kan jikinta,guntun tsaki yayi snn ya fara tashin ta da qyar ya samu ta motsa sbd baqin bacci ne da ita ,a maimakon ta tashi sae ma gyra kwanciya tayi,cike da takaici yace"wlh duk kika koma wani bacci za'a fasa tfyr nn ne!firgigit ta tashi tana miqa had'e da hamma tace"wayyo my man bacci bai ishe ni ba fa"komai kasa ce mata yayi don duk ta cika shi da takaici ganin ba komai a jikinta amma ko kunya babu sae wani miqa take a gabanshi, haka ta tashi ta nufi bathroom ba tare da ta yafa komai a jikinta ba.

Guraren qarfe tara mohd ya koma d'akin Rynt cikin shirin sa tsaf sae qamshi yake zubawa ,ya same ta zaune da breakfast a gabanta yace"mami fa ?tace"tana bayi"

yace "ok mu zamu tafi" tayi saurin kallon shi tace"to mufa zamu koma gidan inna ne, snn zancen komawata islamiyya fa ?yace"zancen islamiyyar ki babu"kmr zatayi kuka tace"amma ba haka mukayi da kai ba gurin Abba,,wani mugun kallo ya watsa mata yasa kai zai fita tayi saurin tashi ta bishi hkn yasa ya dakata tace"bafa zan iya kwana daga ni sae mami a gidan nn ba,yace "wnn kuma ya rage naki"

Ya fita hk ta koma binshi ya daka mata tsawa yace"kikayi gigin na sake taka qafa ki tako taki ko wlh sae na mare ki"kuka ta fashe mai dashi tace"nidai kayi haquri dan Allah mu tafi gidan inna kuma na koma islamiyya wlh na sa raina a islamiyyan nn"

A sae ki cire tunda ba gidnku bane da zakiyi abinda kika ga dama!

Sautin kukanta ne ya soma fitowa ta hana faruwar hkn ta komawarta ta zauna tana jin mami zata fito bathroom tayi saurin share hawayenta yayinda mami ta fito tana fad'in " gufranaka ya Allah"

ta washe baki tare da fad'in"hkne ko Anti?Rynt ta qirqiro murmushi tare da gyad'a mata kai"snn takai dubanta gun mohd da har lokacin yana tsaye bai fita ba mami taje gurin shi da gudu yaja hannunta suka fita.

Tayi awa d'aya kafin taga dawowar mami.

Wacce ta dawo d'auke da kayan wasa kala kala sae murna take taje kan bed tana fad'in"Anti yaya ne ya sayamin kayan wasa yace in ta wasa har su dawo wai baza su jima ba"Rynt tace"to zo kici abinci?ai anti sae da nayi breakfast kafin naje raka su yaya a airpot ,Rynt da ba tasan meye haka ba ta basar da zancen. can mami tace"lah anti na manta yaya nasir fa yana falo wae kije.

Koda Rynt taje kuwa ta same shi zaune a falo cikin ladabi ta gaida shi ya amsa ba yabo ba fallasa snn yace"ko da akwai wani abunda kike buqata?ta gyad'a masa kai tare da fad'in "eh"yace"me kenan"

tace"ina son na koma gidan inna da zama ne har idan sun dawo snn kuma ina son na koma islamiyya"yace"meyasa kike son komawa gidan inna? Sbd bana jin zan iya bacci daga ni sae mami a gidan, gidan nn ya mana girma sosai"indai wnn ne ai mai sauqi ne Rynh don da sannu zaki saba kuma idan wani abu kike tunanin zai faru ai akwai masu tsaro sosai a gidan kuma da yardar Allah ba abinda zai faru kinji? ta gyad'a masa kai snn yace"zancen islamiyya kuma gobe inshaAllah nn cikin anguwar zan nema miki wata islamiyya ta matan aure "tace"to nagode yaya nasir"

yace"sae kuma me kike buqata? Shike nn komai bana buqata, to ga wnn ki riqa a hannun ki, tace"Aa wlh ka barsu kawai nagode inada kud'i a hannu na da inna ta ban"murmurshi kawai yayi ya ajiye kud'in kan center table ya tafi tace"masa nagode snn ta d'auki kud'in ta juya cike da jin dad'in zata koma islamiyya,yayinda nasir ya fita cike da mamakin mohd ace zai yi tafiya bai bawa mtrsa komai ba.

Da dare kuwa duk ta cire wani tsoro a ranta sukayi baccin su ita da mami.

Washe gari da kanta taje kitchen tayi musu break fast sbd yinin jiya duk bata ga kuku ba bai kuma kawo musu abinci ba.

8:pm nn falo suke zaune su biyu abinsu suna kallon tom and jerry.

Sae ga nasir ya shigo da sallamar sa.

Bayan sun gaisa ya bata leda yace" hijabin makarantar ne a ciki kuma da qarfe biyu ake zuwa a dawo qarfe hud'u .

makarantar tana a nn bayan gidan ba nisa amma gobe zan zo na kaiki don kiga makarantar.

Sosai tayi mai godiya snn ya tafi.

Haka ko akayi washe gari nasir yazo ya kaita islamiyya mami kuwa ya kaita gida.

To tun daga rnr ita ke kai kanta ta kuma maida kanta amma sae da qarfe biyar ake maida mata mami.

Su mohd kuwa kusan sati uku sukayi a yawon honeymoon d'insu.

Rynt kuwa sosai ta maida hnklinta zuwa islamiyya kuma rashin kuku bai kawo mata wata matsala ba don koda 1:30 keyi har ta gama musu abincin su na rana sunci ita da mami bcs kafin qarfe biyu nasir ke zowa yakai mami gida,sbd Rynt ta samu taje islamiyya kan lokaci,idan kuma ta dawo qarfe hudu sae tayi sll snn take d'aura musu girkin dare,kuma duk abinda tayi ra'ayin dafawa akwai shi a gidan matsalar ta d'aya itace kewar inna da take sosai.

Rnr wata assabar ne Rynt ta dawo daga islamiyya ita da wata qawar ta suka shigo gidan kowanen su cikin niqabi,da kuma hijab d'insu har qasa da socks .

A nn harabar gidan ta had'u da malika da mohd wa'anda saukar su kenan, gaban Rnynt yayi mugun fad'uwa sbd tunanin abinda zai biyo baya ita da mohd idan yaga ta koma islamiyya bada sanin sa ba, hkn yasa ko gaida shi taqi tayi dan kar ya balbaleta gaban qawar ta.

Dashi har malika kallonta suke har suka shige, malika ta kalli mohd ta6e da baki tace"my man lokaci fa yayi da zaka gargad'a mana yrnyr nn, jifa har da wani kwashe kwashe take maka ,mohd yace"zanyi maganin ta ne ai ,in ni sa'anta ne ko kuma gidan nawa an gaya mata qwai da dunge duk shigowa suke suyi abinda suka ga dama"hm rainaka tayi wlh ita d'in kanta wace ce da har zata yo maka wani jajube jajube.

Su Rynt kuwa har suka shiga d'aki gabanta na dukan uku uku .

Byn ta nunawa wacce suka shigo tare bathroom tayo fitsari ta fito take ce ma Rynt "nikuwa Rynt

ba mai gidan ki bane ya dawo?Rynt tace"shine"

tace"ikon Allah sae kikayi kmr baki sanshi ba,"uhm"cewar Rynt yayinda er makarantar tasu bata sake cewa komai ba ta fita had'e da yiwa Rynt godiya.

Nn kan saukowa upstairs ta had'u da mohd ta gaida shi ya amsa ba yabo ba fallasa snn ya wuce sae d'akin Rynt wacce ya samu ta cire niqab d'inta kenan ,tana had'a ido dashi tasha mai toka, shima fuskar sa tamau yake cewa "wace ce kika shigo min da ita a gida?tace"qawata ce"

da wane dalilin ta shigo min gida? Lalura, shine kad'ai abinda tace ta kuma kama hanya zuwa bathroom haka shima bai sake cewa komai ba ya fitawar sa, fasa shiga batroom d'in tayi don dama tsoron kar ya dake ta yasa tayi niyar shiga bathroom,shiyasa ma tayi mamakin ganin ya fita bai yi mata fad'an ftr ta ba da kuma inda ta fito,ko meyasa,oho.

Da dare mohd ya dawo daga masallaci sllr isha'i ya tafi d'akin malika ya sameta kwance tana waya tayi saurin katse wyr ta tashi ta tarbo shi cike da kisisina tace"ya akayi my man ko wnn abar ce takai ma koina don naga fuskar ka kmr ba annuri ,yace"yunwa ce wlh na rasa ina d'an iskan kukun nn ya shiga ace tun d'azu da muka dawo bai kawo mana abinci ba kuma har yanzu ba alamar za'a kawo,,tace"oh no am sorry my man ai baya nn, ina yaje? Wlh nice na sallame shi da zamu tafi honeymoon ,da sauri ya kalleta snn yace "meyasa?

tace"me zai xauna yi to tunda bama nn"

yace"haba malika mami fa?

tace "naga fa a gabana ka damqa kulawar mami a gun yayanta nasir kuma kasan komai mami ke buqata nasir ba baqonta bane zata gaya mai kuma zai mata tunda ko baka bashi kulawarta ba ai dole ya kula da ita tunda qanwar sa ce,,kuma ai tun lokacinda mukayi tafiyar nn kullum a gida mami ke yini ko ba haka naji kana waya da shi nasir d'in ba?naji hkne ,kira shi kukun yazo ya dafa mana abinda zamu ci da daren nn don nikam ina buqatar naci abinci kafin na kwanta, to my man amma don Allah zanso na roqeka wani abu, fad'i inajinki,dama ina son naje gida ynz zuwa qarfe goma sae na dawo kaji, ya shafo cikinta tare da fad'in"to ki bari idan kinci abinci ko"um um lokaci zai tafi kuma idan naje gida ai zanci,to shike nn kira min kukun ni yazo ya dafa min nawa, tace"ok"snn ya fita.

Yana nn kwance a d'aki ta shigo cikin shiri na qananan kaya amma ta d'aura after dress akai sae zuba qamshi take kallon ta yake har ta qaraso inda yake kwance kan sofa ,ta duqa gab dashi d'auke da murmushi a fuskarta takai bakinta kan nashi ta had'e,inda cikin minti 1 ta zare bakinta

tana mai fad'in"ur food is ready sae kaje kaci then ni zan tafi "yayi murmushi yace"ok ki gaida su mama"tace"zasuji" snn ta fita.

Shi kuma mohd ya fito ya nufi gun dining ya zauna har zai fara cin abinci sae kuma ya tashi ya nufi d'akin Rynt,

Kai tsaye Rynt ta ganshi amma hkn bai hana tayi saurin 6oye littafanta na islamiya ba da ta ftr tana d'an dubawa,snn ta kalle shi kmr marar gsky ga hannyenta takai baya tana qara 6oye littafan a bayanta.

shaye da toka yace"lafiyar ki? tayi saurin cewa"lafiya ba komai"

ya qara shan mur snn yace"da bama nn a ina kuke samun abinda kuke ci keda mami? Tace"ina dafa mana ne kullum"

to ina mami take ne yanzu?tana gida har yanzu bata dawo ba"yace"shike nn amma ki sani daga yau kar na qara ganin kucakar qafar ki a kitchen"ta gyad'a masa kai kawai shi kuma ya fita

sae kawai ya had'u da mami ta wani maqalqaleshi tana mai murnar ganin shi.

Washe gari da qarfe biyu Rynt tayi shirin ta tsaf na islamiyya ta fito cike da tunanin yanda zata kaya da mohd idan ya ganta.

koda ta fito gate d'in gidan sae ko tayi kici6is dashi zai kunna hancin motar sa a cikin gidan.

Yana ganin ta ya fasa shiga gidan sae ma tsaida motar sa da yayi ya fito,a lokacin Rynt jin tayi kmr ta kwasa aguje kafin ya qaraso gareta amma hkn ta dake tayi tsayinta har ya qaraso gab da ita har ma tana jiyo qamshin turaren shi.

Billy giro😊

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

[2:48PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [1/18/2017]

🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

🔮🔮🔮

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.