Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 53 of 56
*page 91*
Bayan sati d'aya da yin biki Ryynt ce zaune a d'akinta tana shayar da Razeenah sae ga saliha ta shigo d'akin da sallamar ta,Ryynt ta amsa mata sallamar d'auke da murmushi a fuskarta,saliha ta zauna tana fad'in"maman yara kina nn sae shayarwa kike tayi ina Ammar da Anwar?
Ryynt tace"Ammar na gun Baaba hurera ta goya min shi hakama Anwar na a bayan alawiyya ta goya shi"
Saliha tace"ok dana shigo gidan sae naji tsit kamar ba kowa"
Suna baya suna shan iska ni kuma muna nn muna bacci nida Razeenah shine ta farka nake bata mamma.
Saliha tace"zakiyi fama kam idan kuka koma sauqin ki d'aya yaran basa da rigima"
Ryynt tace"wlh kuwa kuma naji ma mk yace idan mun koma en reno zae samar musu had'i da alawiyya"
Saliha tace"da yafi kam nama ji umma na fad'in wnn kàron mami bazata koma ba"
Ryynt tace"ae banji dad'i ba umma ce wae d'awainiyar zata yi yawa"
Saliha tace"ai kam abun zae yi yawa wlh"
Ryynt tace" haka dae kuke gani ya ita umma da mami suna lafiya?
Lafiya qalau suke umma ta ma ce in gaida ki keda yaranki ga ma wnn tace na baki sae ta kiraki a waya zata miki bayani.
Rryynt ta kar6i ledar da saliha ta bata tayi godiya had'e da jawo bedside drawer ta saka a ciki.
Saliha tace"tun yanzu an fara yiwa yaya gyara"
Hm saliha knn bafa kayan da kike nufi bane.
Ba wani nn kan me to za'a ce sae an kiraki a waya snn za'a miki bayani ni ba amin bayanin ba na miki.
Ryynt tayi murmushi
tace"ina jin kunyarki saliha a daina zancen nn kuma in banda abinki idan ba'a fara gyaran tun yanzu ba yaushe za'ayi?
To Ryynt ina na sani na d'auka wani abun sae kana tare da miji kake sha.
Eh akwai abinda dole sae kana tare da miji amma wnn basu bane na gyaran jiki ne tukun dan kinga tun rnr da na haifu na soma tsalki da ruwan bagaruwa sbd tana saurin warke miki ,
take kuma take matse mutum,sae dae kinyi aure zaki fi fahimta dan wani abun ma in kika sha shi sae kin qwaci kanki wlh.
Saliha tace"cabd'i da wahala knn?
Uhm kedai sae kinyi auren koma mene ne kyaji da kanki ba sae kin sami labari a bakin kowa ba.
Saliha tace"wlh Allah Ryynt ni har ko yaushe mamakin aure nakeji da bana ganin mata da miji na jin kunyar junan su wae ace rnr da aka kae amarya ko sakewa basu fara yi da junan su ba sae kiga abu ya shiga tsakanin su inyi mamakin ta yaya ma zan barka nikam.
Ryynt tace"hm saliha knn duk da dae ba haka nawa yazo ba amma wlh mazan ne da shegen wayo sae kiga suna miki laf laf sae lalla6aki suke suna kashe ki da dad'in baki har su kae ga cimma burin su kawae da safe ke ya bari da jin kunya dan dae shi ba jin kunyar zae yi ba.
Saliha tace"kae bazae ji kunya ba fa kika ce"
Ryynt tace"inafa namiji kuma ae sae dae ma yayi ta sa ki qara jin kunya dan wani ma sae ya tsinto abubuwan da kikayi fad'a a cikin faruwar abun yana fad'a miki kin jima baki nutse a cikin qasa ba shi ina ruwan sa.
Dan haka wata da muka had'u a chat da aka mata aure a kwanaki take gaya min wae ashe haka maza suke basu da kunya rnr da aka kaita ya neme ta taci kuka tana kiran umma da Abba da gari ya waye sunyi wanka sunci kwalliya suna zaune a d'aki suna breakfast kanta qasa ko kallon sa bata iya yi daga rad'a ya mata a kunne yace ni'ima mene ne ko zamu je gun umma da Abba ne naga daren jiya sae kuka kike kina kiran su,nayi dariya nace to ke me kika ce masa tace"inafa ji tayi kmr ta nutse anyi sa'a baqi sunyi sallama tayi saurin fita ta bashi guri,kuma kiji fa ni'iman ba sunan ta bane Aysha ne sunanta kawae dan yaji ta yanda yake so shike nn ya maida ta ni'ima kuma a gaban kowa kiranta yake da sunan da duk lokacin da ya fad'a sae taji kunya tunda tasan dalilin da yasa yake kira mata sunan tayi tayi ya daina yaqi ta gaji ta barshi.
Saliha tace"hm lallai maza ba kunya"
Ryynt tace"uhm kedai bari kawae"
Nan suka bar zancen saliha ta kar6i Razeenah da ta gama shan mamma sae kallonta take cike da sha'awa tace"gaskiya Ryynt mamman ki yana da kyau ji yanda yaran nn suka qara yin 6ul 6ul kamar ba en sati biyu ba wlh"
Ryynt tayi d'an guntun murmushi tace"ae dole wnn kunun hakukuwa na gyaran nono da inna keta d'ura min wani lokacin ma idan suka jima suna bacci mamman har zuba yake.
Saliha tace"to kuma shine ake had'a musu da madara"
Ryynt tace"eh mana nonon baya fa isar su har su uku dole sae an had'a musu da madara"
Saliha tace"kina ma qoqari wlh, ko d'aya ya aka qarasa dashi bare uku"
Ryynt tace"ae bari rnr da akayi suna da dare bayan isha'i ina cikin baccin gajiya da ya d'auko dad'i kawae naji Mk na tashi na wae in tashi in ba yaransa mamma sun tashi ae bansan lokacinda na fashe masa da kuka ba a take ya shiga rarrashina yana bani haquri,snn ya had'awa yaransa madara ya basu ni kuma tuni na koma bacci ban san ma lokacin da ya tafi ba.
Saliha tayi murmushi dan rayuwar mohd da Ryynt na matuqar birge ta bata dae ce komai ba sae tashi tayi tare da d'aura Razeenah a kafad'ar ta ta kwantar tana fad'in "bari naje na gaida su inna na dawo"
Ryynt tace"to"
Kafin saliha ke fita daga d'akin.
Da dare Ryynt ta fito daga gurin wanka ta sami mk kwance akan gadon ta idanuwan sa a lumshe kamar mae bacci sae shafa bayan Ammar yake dake kwance kan qirjinsa yana bacci,
Ryynt tazo ta zauna kan gadon tana kallon Mk da ya bud'e idon sa yana kallonta tace"Anwar fa da Razeenah ko sunyi bacci ne?
Yace"Eh suna can d'akin inna sunyi bacci amma shi ammar ya kasa baccin sae kuka da yake da alama yunwa yake ji shine nazo ina ta jiran fitowar ki amma naji shiru hkn yasa na had'a masa madara na bashi yasha yayi baccin"
Ryynt ta kae hannun ta a hankali ta shafo kan Ammar tace"Allah sarki na manta d'azun yana bacci koda aka basu madara da kuma ya tashi ba'a bashi ba shiyasa"
Mohd bae ce komai ba sae kallon jikin Ryynt yake wacce ke d'aure da towel iya guiwa tayi haske sosai ta qara kyau ga cikinta da ya koma tsaf kamar ba itace tayi kayan cikin en uku ba.
Yace"my ryynt kinyi kyau kuma jikin ki ya qara fresh me inna ke baki haka dani ta barni duk na rame"
Ryynt ta kalli jikinta d'auke da murmushi snn ta kalli nasa jikin lumui lumui kmr jikin zomo sbd laushin fata irin nasa da baka babance shida Ryynt wa yafi wani laushin jiki.
Tace"ni kuwa Mk banga wata rama da kayi ba"
Yace"Allah koh ni kuma ji nake kamar na rame"
Tace"um um gaskiya baka rame ba kana nn yanda kake,me ma zai sa ka rame to"
Yace"kewarki mana kwata kwata wlh tunda kika bar gidan baya min dad'i so lonely gashi nasan inna bazata barki ki koma ba sae kunyi arba'in"
Yana maganar ne kmr wani qaramin yaron da ke cikin damuwa.
Ryynt tace"kana fad'in arba'in nifa sae munyi wata ko uku ne"
Mohd yayi murmushi yace"ae ke nasan idan aka barki ko shekara d'aya zaki iya yi babu ruwanki da damuwar da zan shiga"
Tace"uhm Mk knn idan ban damu da damuwarka ba damuwar wa kake so na damu da ita?
Yace"to gashi kina fad'in sae kunyi wata uku bayan yanzu yanzun nn na gama gaya miki irin damuwar da nake ciki"
Tace"ka fahimce ni mana ba wae ban damu da damuwar ka bane"
Yace"ba wani nn ae na gano ki"
Ya fad'i hakane yayinda ya tashi zaune sannu a hankali rungume da Ammar a jikin sa ya tafi dashi zuwa kafad'ar sa snn ya tashi yaje ya kae shi d'akin inna ya dawo.
Ryynt na jikin wardrobe tana ciro kayan bacci yaje sukayi sae da safe kmr yanda suka saba snn ya wuce.
Sannu sannu lokaci keta tafiya wanda tuni su saliha hutun su ya qare sun koma school Ryynt kuwa har tayi arba'in.
Su Ammar sun qara yin 6ul 6ul da kyau abin sha'awa don duk wanda ya gansu sae yaji yana son d'aukar su har dae yanda sukayi saurin wayo dan idan ba'a gaya maka arba'in kawae akayi ba zaka d'auka ko en wata uku ne.
Da dare guraren bayan isha'i mohd ne tafe cikin mota shida Ryynt yaransu na baya tare da allawiya.
Mohd dake driven bae zarce koina ba sae gidan sa wanda tun lokacin da ya shigo gate d'in gidan Ryynt ke kallon sa da mamaki har ya parker mota kafin tace komai wayar sa tayi qara ya d'aga wayar ya fito mota ya zagaya ta gefenta ya bud'e mata yaja hannun ta suka shiga ciki suka tsaya a falo sae kallon sa take yana waya.
Yana gama wayar tace"Mk kai da kace min family house zamu je ya kuma kazo damu nn"
Yayi murmushi yace"wayon manya na miki ba wani family house da zamu je nn nake nufin zamu zo"
Tace"to meyasa?
Yace"har kya tambaya ko kin manta na gaya miki cewa da kinyi arba'in zaki dawo ne"
Tace"uhm kaima dae da wasa kake Mk abu sae kace tulin wanki haka kawae ba shiri ka kwaso mu kace mun dawo knn,da akwai dae abinda ka shigo d'auka je ka d'auko mu tafi kasan mun bar alawiyya da yara a mota"
Yace"Allah da gaske nake miki mun dawo knn ba wani abunda nazo d'auka"
Tace"Mk bana son irin wasar nn dan Allah ka maida mu gida dan wlh ni ban shiryi dawowa ba"
Yace"Ryynt wane irin shiri kuma idan kayane gobe zanje da kaina gidan inna na kwaso maku komai"
Haba mk haka kawai zan dawo banje nayiwa kowa sallama ba nida nake son har qauyen mu sae naje.
Gaskiya Ryynt ni bazan iya harakar al'ada d'in nn ba wae ace don mutum yayi arba'in sae yaje yawo gidajen mutane kiyi haquri bana so ba kuma zakiyi ba amma zuwa qauyen ku bazan hanaki ba ko gobe kike so zan kaiki.
Ryynt ta girgiza kanta tace"gaskiya ni kawae ka maida ni bazan iya wnn abin kunyar ba ae sae ace da had'in bakina tunda ko inna bata sani ba"
Da mamaki yace"abin kunya kuma Ryynt kina mata ta dan na maida ki shine ya zamo abun kunya"
Tace"eh mana yau yau fa da yin arba'in se aji kawae na dawo haba gaskiya ni ka maidani"
Yace"wlh bari kiji ba inda zan maida ki kin dawo knn"
Cikin muryar kuka tace"wlh ni kuma bazan zauna ba sae na koma"
Rae 6ace mohd yace"shike nn gaki ga hanya jeki bazan hanà ki ba amma wlh kar ki kuskura kice zaki je min da yara ,kiga idan baza mu rayu ba dan ba ke"
A fusace ta fita tana fad'in ae dama bance da yaran naka zan tafi ba.
Cikin 6acin randa tafito d'auke dashi taje taja alawiyya zasu bar gidan ,
Alawiyya tace"Anti ina zamuje munbar su Ammar a mota?
Ryynt tace"ki barsu ubansu zae ji dasu"
Daga haka alawiyya bata sake cewa komai ba har suka fita suka tari napep suka wuce sae gidan inna.
Billy giro😊
[10:07PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA🔮```
🔮🔮🔮
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.