Complete Hausa Novels

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 1 of 56

[2:38PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BAR SHI BA!🔮```

_[9/25/2016]_

*Na Billy giro😊*

🔮🔮🔮🔮񛠊

_*page 1*_

Rayyanat! Rayyanat!! Rayyanat!!!

Er 16 yrs ce ta fito da gudu tana fad'in "Na'am Baffanah"

Shiru baffan nata yayi yana mai kallon Rayyanat wacce ta kasance chocolate ba qiba ba rama tana da kyau daidai gwargwado tana sanye da riga da zane bara da bana sae dankwalin kanta da shima ba kalarkayan jikin ta bane ga zanen jikinta duk gabad'ayan sa dashi ne ba masoka tsintsinya gashi ta riqe wani gurin da ya yage bata son aga jikin ta yace"Rayyanat baki sami allura da zare bane wannan karon? Abba ban samu ba naje suka ce baza su ara min ba sun gaji da siya ina qare musu zaren"cikin muryar kuka ta qarasa maganar ,Baffan ta yace"kar kiyi kuka Rayyant inshaAllah yau idan mai gari ya biyani kud'in noman da nake masa zan saya miki allura da zare domin ki huta da aro maqota kinji"to Baffanah na gode Allah yasa ayi nasara fiye da kullum"

yace "Amin Rayyant, zan tafi ki kula da kanki banda yawon maqota"inshaAllah amma Abba yau baka so na raka ne?Rayyanat ta yaya zaki fita bayan zanin ki ya yage ga samarin da ke dandali a tsakiyar gari"Haka ne Baffa Allah kiyaye hanya"Amin Amin.

Daga haka ya fita rataye da fartanya kan kafad'ar shi inda Rayyant tabi mahaifin nata da kallo wanda shima tufafin jikin sa duk sun tsufa sun tamure.

sae da ta daina hango shi sannan ta koma d'aki tayi zaune

tana qarewa d'an akurkin d'akin ta kallo wanda ba wasu kayan kirki a ciki face d'an kunshin tufafin ta da baza su wuce kala biyu zuwa uku ba sae tsofuwar tabamar da take kwanciya da wani pillow akai mai kama latsatstsen biredi sae gidan sauro da aka dunqule shi aka soka jikin taga sae wasu kwallaye guda biyu da ke cikin d'akin da bansan meye a cikin su ba.

Tana cikin qarewa d'akin kallo cikin ta ya shiga qugi sbd yunwar da ke addabar ta wacce tun safiyar jiya da suka ci abinci ita da Baffan ta har yau washe gari basu sake samun abinda suka ci ba.

Kwanciya tayi ko zata samu bacci ya d'auke ta kafin Baffan ta ya dawo amma yunwa ta hana ta bacci kamar yanda tayi fama a daren jiya wanda sae da ta cika cikin ta da ruwa ta samu tayi bacci haka ko yanxu tashi tayi taje waje gurin randar ruwa ta cika cikin ta tap ta koma ta kwanta .

Har bacci ya soma d'aukar ta ne taji sallamar wata qawar ta mai suna "Sarat"

Sae da Rayyanat ta amsa mata sallama sannan ta shigo .

Yarinya ce doguwa er sililiya baka wacce ita ma tana da kyaun ta dai dai gwargwado zama tayi tace"Rayyanat kiyi haquri fa tun jiya naso ace nazo amma shiryen shiryen tafiyar da muke yi na komawa Birni bai barni ba "

D'an guntun murmushi Rayyanat tayi taji kamar ita ce zasu je Birni ita da Baffan ta sbd ta kasance tana mugun son zuwa Birni amma ko sau d'aya bata ta6a samun zuwa ba.

Sarat ta miqa mata wata er baqar leda wacce ake kira cefanen mutum d'aya tace"dan Allah kar ki ce baza ki kar6a ba sbd nasan halin ki kuma ban saya miki don wata manufa ba sae don nasan kina bala'in son rogo inda har ka kasuwa naje na saya miki amma kiyi haquri nasan ba kya son haka "

ba komai Sarat a yau zan kar6i kyautar ki sbd zaki tafi ki barni ban kuma san yaushe zamu sake had'uwa ba nagode amma yaushe ne zakuyi tafiyar ?a yau d'in nan kuma a yanzu shiyasa na baki haquri kan rashin zuwa na tun jiya nima ban so haka ba wlh...kar ki damu domin nafi kowa sanin yanda kika damu dani shiyasa a kullum bani da wata qawar da ta fiki...Uhm na gode Rayyanat ni zan tafi su Abba na a bakin qofar gida da mota suna jiran fitowa ta .

Nan Rayyanat ta tashi suka fito inda Rayyanat ta russuna cikin ladabi ta gaida iyayen Sarat kafin wani d'an matashin saurayi ya fito a cikin motar wanda sak Sarat ce da alama yayanta ne.

Da sauri Rayyanat ta duqar da kanta qasa cikin jin kunya tana d'an kame kame gayen yayi murmushi yace"ako yaushe ina sonki Rayyanat ba kuma zan daina ba duk rintsi duk wuya ina tare da sonki a cikin zuciya ta koda kuwa bana raye.

Ga wannan na roqe ki ki kar6i kyauta ta ta farko da na ta6a baki wanda a duk lokacin da ki ka sanya abinda ke ciki zaki kasance cikin farin ciki sbd tamkar kina tare da nine,

ina fatar masoyiya ta zata kar6i kyautar da na mata ko don tsalkakekken son da take min,,,cikin tausassar muryar ta mai sa shi natsuwa tace "yaya Anwar ban ta6a kar6ar kyautar ko wane d'a namiji ba face ta mahaifina amma yau zan fara a kanka kuma nayi maka alqawari kai kad'ai ne d'a namijin da zan ci gaba da kar6ar kyautar sa har abada kuwa bazan ta6a sa6a alqawarin da na maka ba, ka riqa tuna hakan ako yaushe domin nima na riqa kiyaye wa"

A hankali ya lumshe kyawawan idanun sa yace"InshaAllah Rayyanat bye mu zamu tafi dan Allah ki kula min da kanki "

Daga haka ya shiga mota ya zauna seat d'in driver ya tashi mota yana danne hawayen da ke qoqarin zubo mishi yayinda yake kallon fuskar Rayyanat ta jikin mirror.

Sarat kuwa bye bye take yiwa Rayyanat yayinda kowannen su ke fitar da hawaye a idon shi .

Tsaye take har suka 6ace ma ganin ta nan ta kalli Viva ledar da ke hanun ta ta rungume ta tsam a qirjin ta wasu zafafan hawaye suka gangaro kan kumatun ta inda a hankali ta furta cewa"ina sonka yaya Anwar ba kuma zan daina sonka ba har abada duk rintsi duk wuya ina tare da kai koda kuwa bana raye to kuwa ruhi na zai kasance tare da kai"

🔮🔮🔮🔮🔮

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.