Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 5 of 56
_*page*_ *```22```*
Don tasan a rashin imaninsa zai iya aiwatar da abinda ma yafi haka in akwai, amma kuma bari taga shin me yake nufi da sae dai wata ba ita ba.
Abba kuwa da mohd har umma ba wanda ya kira cikin su bare ya snr dasu yanda sukayi shi da Rynt kawai ya yanke hukunci sae inna ta dawo su yanke shawara shi da ita asa rnr aure.
washe gari hnklinta a kwance tayi shirinta na islamiyya ta fita.
Ko minti 5 batayi da fita ba inna ta dawo daga qauye kuma a nn gidan ta sauka sae murna ake da dawowar ta yayinda ita kuma ta matsu taga Rynt nn Abba ke snr da ita ai ta tafi islamiyya.
Bayan inna taci abinci ta d'an huta Abba ya shiga snr da ita shawarar da ya yanke kan zancen had'a mohd aure da Rynt har yanda sukayi da Abban malika duk sae da ya snr da ita.
Sosai inna tayi murna ba kad'an ba haka kuma itama bata bada goyon bayan mohd ya auri malika ba wanda duk zancen nn da suke yana kunnen hjyrsu mohd wacce tana gama sauraren kaf abinda suka tsara ta koma d'aki cike da masifa ta kira mohd a waya ta snr dashi tace"ga irinta nn sae da nace kbr ni da yarinyar nn ni nasan yanda zanyi da ita wanda ko da kuskure baza ta yarda ta amince da zancen Abbanka ba wlh, amma kace a'a wae kar ta rainani ,raini duk ya wuce ace kmrta baqauya er matsiyata ta had'a surukuta dani,mohd yace"yanzu umma kina nufin duk yanda nayi da ita ta amince da buqatar Abba? Hm!na nawa kuma gashi har sun tsara anjima da dare iyayenka zasu tafi gidan inna asa ranar aurenku!ai wlh kayi wa kanka!don yanzu sae kasan yanda zakayi ka ftr da kanka ko kuma ka nemi wata uwar don muddin ka rasa mafita har takai ga an aura ma ita tofa bani ba kai tunda tun farko sae da nace kabarni da ita kaqi.
Daga haka ta katse wayar sae huci take
tace"in shi mai hnkli ne ko islamiyya baxata dawo ba sae dai wata ba ita ba amma bari nasa ido naga ko dabara ta tayi!in yaso ni kuma na tayasa da wani aikin ta yanda baza ace dasa hannun mu kan 6acewar ta ba.
Mohd kuwa hjyrsa na kashe waya ya rasa ta inda zai sa kansa kan baqin ciki da kuma tunanin hukuncin da zai yiwa Rynt.
Ya zama dole yaje ya jirata kan hnyrsu ta islamiya don yau sae ta fad'i wanda ya aiketa .
Yana fita da motar sa yayi kici6is da Malika ta parker motar ta ta fito, dole ya tsaida tasa motar ya fito yaje gab da ita ya tsaya yana mata wani irin kallo,ita kuwa ta wani langwa6ar da kanta snn tace"my man wai ya ake ciki ne tun jiya da mukayi waya naji shiru har yau "
yace"to shine zaki wani biyo ni har gida da kuma wnn banzan dressing d'inki salon Abbana ya ganki yace bakida kamun kai kuma,in yaso Komai ya qara cakud'e mana! Kayi haquri my man wlh banda wasu kaya sae ire iren su kuma ka sani,to me ya hana ki kirani a waya muyi magana? Ina mgnr zata yiyu a waya nida kwata kwata daren jiya ban samu nayi bacci ba,amma malika kinsan bana son damuwa koma mene ne ai zanje na sameki har gida,kayi haquri na damu ne sosai ,tayi mgnr cike da qwallah tap a idonta, yayi saurin cewa"shikenan kar kiyi kuka gaya min me kike so yanzu?so nake ka gaya min abinda ake ciki ,ajiyar zuciya ya sauke snn yace"wnn yrnyr ta lalata mana komai don ta amince da buqatar Abba snn kuma Abbana har yanzu dai yana kan bakarsa na bazan aureki ba,amma kar ki damu zan shawo kan matsalar komai inshaAllah ,matsalata d'aya yanzu shine anjima za'a sa rnr aurena da wnn yrnr shiyasa at all kaina ya kunce bansan ma wane hukunci zan yanke ba, ga umma ta sani cikin wata chakwakiyar wae bani ba ita idan ban nemo mafita ba har akayi aurena da wnn yrnyr.... Wae da kana nufin zaka yarda ayi auren ne to! Malika uba ba abin wasa bane idan kuma ya yanke hukunci ba yanda za'ayi kuma ya rantse cewa in ta amince tofa shikenan ba fashi aurena da ita, but my man be wise mana,idan ba yrnyr ai ba auren shike nn dole Abba ya haqura, aikin hnkli dai malika ina mai gaya miki 6atar wnn yrnyr tmkr tsinuwace na jawa kaina don dole Abba yasan nine, kawai dai zan aureta amma na d'an wani lokaci .....Wlh! my man bari kaji in gaya ma ba maccen da ta isa ta aure ka bayan ni don ka ma daina wnn sa6on!daga haka taja motar ta a tsiyace ta bar gurin.
Har zai shiga mota sae ga kiran Abba yana son ganin shi,dole ya juya ya tafi ga kiran Abba.
Yau Rynt ita kad'aice kan hnyr dawowa islamiya sbd da safe munir bai cika zowa ba sae da yamma.
Tana cikin tafiyar ta har takai titi zata tsaida napep sae ga wata tsaleliyar mota ta tsaya a gabanta.
Malika ce ta fito daga motar taje gab da Rynt tare da kai hannu ta yaye mata niqabi,nn malika ta yamutse fuska kmr wacce taga kashi tace"hm rainin wayo wai kece ke shirin shiga tsakani na da my man,ta nuna ta da yatsa snn taci gaba da cewa" lemmi tell u 1 thing ruwa ba sa'ar kwando bane haka kuma ramin kura ba gurin shigar akuya bane,a bisa yanda ma na fhmta kwata kwata tsabar talauci ne ke d'ibar ki da haka zan taimaka miki na baki check ki rubuta duk iya kud'in da kike so after that ki sani inda dare ya miki ma'ana kwata kwata ki 6acewa duniyar mu ki tafi can taku duniyar ta matsiyata wnn umarni ne dmn in kika sake kika dawo gare mu wlh sunanki gawa!
gama fad'ar haka ta zaro cheque da biro ta miqawa Rynt ,sae kuma tace "koda yake nasan duhun kai na tattare dake bare har ki iya rubuta wani abu nn ta rubuta million biyar snn ta ce ungo kud'i ne masu yawan gaske da nsn ko ubanki bai ta6a riqa irin su ba bare ke!
Kallonta kawai Rynt keyi wacce batada niyar kai hannu bare har ta kar6i cheque d'in .
Malika tace"gwanda ki kar6a don wlh kanki kika yiwa idan baki kar6a ba sbd ynzu hk ni a shirye nake da nasa a yanke miki hukuncin da yake dai dai a guna.
Komai Rynt bata ce mata ba sae ma ra6awa tayi ta gefenta zata wuce ,sae kawai ta sami kanta da ganin qarti zagaye da ita.
Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:43PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 1/9/2017]
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮
🔮🔮🔮
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.