Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 24 of 56
*page* *```42```*
Yana gama fad'ar hk ya fita.
Wani irin baqin ciki ne ya tokare Rynt a wuya da har ta sami kanta dajin qwalla sun cika mata ida bata dae bar sun zubo ba ta ajiye school bag ta cire takalmi da socks takai su inda ya dace snn ta fito downstairs ta wuce su man zaune a falo ta tafi kitchen ba tare da tako kalli gefen su ba.
Malika tace"matsiyaciya ai da na d'auka ko bazata fito ba"
Man yace"dolenta mana tunda tana son ci gaban karatun ta.
malika ta tashi tare da fad'in "bari ma naje naga wane d'an iskan abinci ne take da niyyar dafa min.
Rynt kuwa tana shiga kitchen ba abinda tayi niyyar dafawa sae indomie har ta d'aura c pot ta zuba ruwa sae ga malika ta shigo ta kalli Rynt a yatsine tace"ke matsiyaciya me kike shirin dafa min ne "Rynt tayi banza da ita ,malika tace"idan kin iya kar ki bani amsa amma wlh ina mae gaya miki kar ki kuskura ki dafa taliya ko indomie,sakwara zaki min da miyar agusi"
Still dae Rynt bata tanka ta ba har ta fita taje gurin man cikin masifa tace"wae da yrnyr indomie na samu zata dafa min don ta rainani"
Yace"wae da to me kike son ta dafa miki? Sakwara mana da miyar agusi,ya kalleta yace"amma kinsan tana da lesson 5:30 to six har yaushe ta gama,da dai kin barta kawai ta dafa miki indomie d'in, kallon sa tayi tace"ban gane ba tausayinta kake ji ne ko yaya?
Yace"ko d'aya mae lesson d'in ne bana son ta 6atawa lokaci"
Tace"to ai sae a farawa mami idan ta gama min girkina sae a mata"
Yace"ok"
Suna nn zaune cikin en mintina sae ga Rynt ta fito riqe da plate d'in indomie takai kan center table d'inda ke kusa da su ta ajiye ta kuma yi ficewarta.
malika ta bita da ido sake da baki snn ta kalli man da ya gama waya knn
tace"kaga er iska indomie d'in fa ta dafa min"
Ya tashi tare da fad'in "bari ina zuwa"
Yaje ya sami Rynt tana shirin shiga bathroom tayiwa mami wanka ,
ya dakatar da ita cikin cewa"ke zo nn "bata je ba sae kallon sa da tayi yace"me malikà tace miki ki dafa mata? tace"sanin kanka ne ban iya wnn abincin ba don ni abu biyu kawai na iya dafawa daga taliya sae iñdomie....bana son raini da kike dafawa a gidà n inna fa?
Tace"Bani ba kam sae dai ko baba hurera"
kallonta yayi kmr zai ce wani abu sae kuma ya fasa ya fita, Rynt ta ta6e baki ta bishi da ido wacce ba klr abincinda bata iya ba a gidan inna qin yine kawai tayi.
Taja hannun mami dake fad'in"wae anti meyasa anti amarya yau tace bata cin abincin kuku? Rynt tace" oho mata kedai muje ayi wanka muci abinci kafin mae lesson yazo ko"
Mami tayi murmushi dan da murmushi Rynt tayi mata mgnr,
wa enda tuni sun shigo bathroom sae ruwa Rynt ta had'a tayiwa mami wanka byn ta gama mata mami ta fita ita kuma tayi nata.
Mohd kuwa koda yaje ya snr da malika cewa Rynt bata iya wnn abincin da tasa ta ba sae masifa take ita lallai sae Rynt tazo kuku ya nuna mata yanda ake don ita kam baza taci indomie ba da qyar man ya samu ya lalla6ata har ta yarda taci indomie a cewar gobe sae Rynt ta dafa mata duk abinda take so.
Rynt tana fitowa wanka sharp sharp ta shirya suka ci abinci sae dai koda suka gama har sun shigo cikin lokacin lesson d'inta tayi saurin kwasar littafanta ta tafi ta samu kuwa har mai lesson d'in yazo yana jiranta.
Wnn karon man baizo ya fake kmr ko yaushe ba don yana can shida malikarsa a d'aki.
6:00 ake gama mata lesson d'in sae ya farawa mami ana yin magrib ake gama mata ita kuma.
But rnr Thursday ,Friday Saturday and Sunday suna samun enuf time da ake yi musu lesson bcs thursday 2:00 ake tashi friday 12:00 then asabar da lahadi islamiya ce 8am suke zuwa su dawo after 2 yayinda duk ranakun nn hud'u da qarfe hud'u lesson tearcher d'in ke zowa bashi yake barin gidan ba sae anyi magrib.
Bayan 2 dayz duk kwanan nn biyu Rynt ke dafawa malika abinci idan sun dawo daga school amma ba wani abinci bane face indomie wacce take silalawa sama sama takai ba tare da ta damu da ta nina ko bata nina ba.
Gashi kullum malika sae masifa take yiwa man ita tgji da cin indomie a kira kuku ya nunawa Rynt kallolin abinci ta riqa dafa mata,Man kuwa sae rarrashinta yake yana lala6ata sbd hk kawai yaji baya son kuku ya koyawa Rynt abinci inda dae mace ce.
Rnr dai ta matsa mai kan dole ya kira kuku suka sami Rynt a kitchen ,man ya dakatar da Rynt dake shirin d'aura indomie snn yace da malika"me kike son ta dafa miki ?
Nn ta shiga shafa cikinta a yangace snn tace"inaga yau jellop rice muke ra'ayi nida babynka amma taji busasshen kifi da manja a kuma zuba ganyen alanyafu snn ayita da yaji sosai"
Yace"shikenan abinda kk so? Tace"eh ni zanje na kwanta na huta nagaji da tsayuwar nn yace"ok"snn ta fita nn ya maida dubansa gun Rynt yace"oya ga kuku nn zai nuna miki komai yanda zakiyi".
Kallon sa kawai tayi snn ta kalli kuku shi kuma man ya nemi kujera ya zauna yana duba jarida.
Kuku yazo gaban Rynt ya had'a komai da za'a sa a jellof d'in snn ya d'ura c pot ya zuba manja a cewar idan ya d'auko zafi sae ta saka niqaqqin tattasai da albasa da tarugunda aka niqa sama sama bayan en yankakkin da ke ajiye gefe da sae jellop d'in ta d'auko dafuwa xa'a saka su.
Hanklin kuku nakan busasshen kifin da yake d'an qara gyrawa yayinda Rynt ke kallon manja har yayi mugun zafi ,ta d'auko kofin ruwa kai tsaye ta kwara cikin manjan,
baaa! belar wuta ta fito tayi sama! ai kuwa Rynt ta buga ihu da ita har kuku ba mae kama wani sae qoqarin 6ira suke su fad'i wanda tsirif ya rage Rynt ta fad'a kan jikin kuku man yayi saurin tashi ya fizgota zuwa jikin shi,
Yayinda cikin mugun 6acin rae man ya kalli rynt yace"u are very stupid! ke ba kya ganin inda zaki fad'a ne!
Ta rufe ido gam had'e da fashe mai da kuka wacce da gayya ta zuba ruwan amma tayi mugun tsorata da ganin yanda wutar ta fito a manja, dan ynz hk jikinta sae qyarma yake.
Man kuwa ganin yanda Rynt ta rufe idanunta sosai tana kuka ,ya d'auka ko manja ya shiga mata a ido nn yakai hannu zai bud'e ya hura mata idon amma taqi yarda sae tsalle take tana kuka bayan ba abinda ya shiga mata a idon pretending ne kawai don ta samu ta zillewa girkin.
Da hk ta qirqiro tari tana tayi se duk Man ya damu ya rasa yanda zai mata ya kalli kuku cikin daka mae tsawa yace"dan Allah qaton banza tashi kaje ka kashe wancan abun duk yabi ya damu mutane!
Da hnzari kuku ya tashi yaje ya kashe gas cooker,
man kuwa yaja Rynt har zuwa d'akinta wacce sae tari take ga kuma idanuwanta dake rufe still .
Bathroom ya nufa da ita ya wanke mata fuska ya ciro farin handkerchief d'insa ya share mata fuska snn ya fito da ita ya zaunar kan bed tana d'an ci gaba da tari kad'an kad'an nn yaje ya tsiyayo ruwa a glass cup ya zauna snn yace"bud'e idonki ga ruwa kisha "
Qin bud'e idon tayi sae hannu takai tana lalube sae jin tayi yakai cup d'in ruwa a bakinta tasha ruwan kad'an ta kwanta shi kuma yasa blanket ya rufa mata jikinta ya fita sae a snn Rynt ta bud'e idonta a hnkli tare da saurin yaye blanket ta tashi ta watsa da gudu bathroom sbd fitsarin da yayi mugun matsar ta.
Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [2/4/2017]
```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```
🔮🔮🔮🔮
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.