Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 10 of 56
_*page*_ *```27```*
Tsawa mohd ya daka mata mai firgitarwa tare da fad'in"get out!da sauri Rynt ta tafi har tana had'awa da gudu taje d'aki ta fad'a ruf da ciki kan bed tare da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi.
_Ta yaya zan barshi! bayan shine silar rabani da farin cikina kuma shine silar zuwana birni har na had'u da qaddararren aurenda nake ganin wlqnci haka, lallai idan mohd ya kasance shine wanda ya kashe min mahaifi a cikin su ukun nn fansar da zan d'auka akanshi mai munin gske ce._
_Allah sarki yaya anwar nsn da kana raye haka ta faru dani da ka bimin haqqina ba tare da na aiwatar da abinda bai dace dani ba._
Tana magana ne a cikin zuciyarta yayinda take ci gaba da kuka mai cin rai.
Tana cikin hakane mami ta shigo d'akin, Rynt tayi saurin share hawayenta wasu suka sake zubowa dai dai mami ta hau gadon d'auke da ledodi a hannunta ta kalli Rynt tace"anti wa ya dake ki kike yin kuka?share hawayen tayi tace"ba wanda ya dake ni"amma kuma kikeyin kuka ko wani ne ba lfy don naga yau da mukaje asibiti nida yaya Nasir duba wani yaya munir abokin yaya man ummansa sae kuka take tayi sbd ko magana baya yi ance ma sae an fita waje dashi ko zai sami lafiya,wasu hawaye ne suka sake zubowa Rynt tace"yaya munir yayan su safiyya? Eh anti shi ashe kin sanshi,kuka ta shiga yi mara sauti ,mami tace"anti umma fa tace min ba kuka ake yiwa mara lafiya ba addu'a, kinji anti ki daina kuka ki masa addu'a, had'e kai da guiwa Rynt tayi tana ci gaba da kuka ,mami ta dafa ta tana fad'in"anti addu'a fa zaki masa ba kuka ba,nima da nake er qararrama ban masa kuka ba sae cewa nayi Allah ya bashi lfy,naji mami zan masa addu'a nima, ta fad'i hkne yayinda ta d'ago tana share hawayenta, mami ta jawo ledodin da ta shigo dasu guda biyu tace"Anti yaya nasir ne ya saya mana chocolate nida ke ga ledar ki kar6i,Rynt ta kar6i d'ayar leda ta d'aura kan bedside drawer,mami kuwa sae kallon idanun Rynt take da sukayi jajir tace"Anti hln yaji ya shiga miki ido da na samu kina kuka"girgiza kanta kawai tayi,snn tace"tashi muyi sllr zhr sae mu yiwa yaya munir addu'a ko?to anti daga nn ma mu roqi Allah yasa mu anjannah muci kayan dad'i ko?Rynt tayi d'an murmushi snn taja hannun mami suka nufi bathroom tare sbd haka suke kullum in zasuyi arwala tare suke shiga dmn arwala Rynt ke koyawa mami amma wani lokacin sae ta fara shiga in ta kama ruwa snn ta kira mami ta shigo.
Bayan sun gama sallah mami ta d'auko ledar chocolate d'inta tace"Anti zanje na kaiwa anti amarya chocolate taci"
Rynt tace"to sae kin dawo"
ba jimawa sae gata ta dawo tana cin chocolate tace"Anti qofar anti Amarya a rufe take inaga ta fita,na bari gobe na sake kaimata ko? "eh"shine kad'ai abinda Rynt tace don sae tunanin rashin lfyr munir take.
Washe gari da safe ko break fast basuyi ba mami ta jawo ledar chocolate ta fita wae zata kaiwa anti amarya ta d'iba.
Fitar ta keda wuya ta jiyo kukan mami ta fito da sauri har tana had'awa da gudu tana isowa main falo ta had'u da mohd shima ya fito sbd jin kukan mami da yayi ,mami taje da gudu jikin Rynt inda cikin kuka sosai take nuna malika ,mohd yace da malika me kika mata ne! shaye da toka tace"sanin kanka ne qanwar nn taka baqin srt tsiya ne da ita ,tazo ta sameni ina bacci daga kawo min ledar chocolate tayi wae na d'iba nace mata bana so bai isheta ba sae da ta wani cika ni da srt shine ni kuma na mareta,
jiki sanyaye ya kalli mami wacce bakinta ke fitar da jini ya jawo hannunta yasa tissue ya goge mata jinin yace"ki daina takura anti amarya idan tana bacci kinji, cikin muryar kuka tace"Allah yaya qarya take ba bacci take ba "malika ta dallah mata harara tace"dan ubanki ni ke qarya "a fusace ya d'ago yace"malika mind ur tongue qanwata ce fa kike zagin ubanta"to kai baka ji me tace min bane!kuma indai zagin ubana ne ai akanka na koya ,tsaki yayi ya kalli Rynt wacce yake ganin kmr duk laifin ta ne yace"da Allah malama jata ku tafi!
Rynt ta kalle shi snn ta d'auki mami tana share mata hawaye tace"yi hqr Allah zai isar miki"
Malika tace"jar uba! ke ni kike gaya ma magana!
ta tafi fuuu!zata kaiwa Rynt duka ,mohd ya jawota yace"barta kawai zanyi maganin ta ne,nn ya tafi da ita sae masifa take tana sirfà wa Rynt zagi har suka shige 6angaren mohd.
ta6e baki Rynt tayi snn ta wuce d'auke da mami.
Da dare mohd ya shigo d'akin Rynt ya sami Rynt da mami suna pillow fight sae dariya suke suna dukan pillown juna har Rynt tayi nasarar da pillown mami ya qwace ya fad'i qasa nn Rynt ta tashi cikin dariya tana mata gwalo tana fad'in "ko yanzu na cinye ki"cikin shagw6a mami ta turo baki,sae kuma ta washe baki ta tashi da sauri ta bud'e wardrobe ta d'auko qatuwar teddyn ta da tasan Rynt na mugun jin tsoro tayo kan Rynh aguje zata liqa mata,Rynt da ko ganin ta bata son yi ta rufe ido ta kuma kwasa da gudu zata bar d'akin,sae jin tayi ta fad'a jikin mutum nn ta fasa wani irin ihu ta zube gabad'aya a jikin man.
Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:48PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 1/16/2017]
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮
🔮🔮🔮
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.