Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 21 of 56
*page* *```39```*
Girshi Rynt ta ga mami close to her ga kuma teddyn da ta gani a hannunta hkn yasa ta buga razanannen ihu had'e jefar da trayn hannunta.
kafin trayn yakai qasa ita kuwa mami ta fasa nata ihu tare da jefar da teddy sbd yanda taliya ta watso mata a hannu a rikice Rynt tayi kanta tana cire mata taliyar ita kuka mami kuka sbd har ftr gurin ta d'an kwaye ya kuma yi ja sosai.
D'aki suka je amma gabad'aya Rynt ta rasa natsuwarta don mami sae kuka take tayi. gashi tasan cewa man baya nn wacce taji hkne a bakin malika da zata sallami kuku hkn yasa ta yanke shawarar zuwa gidan inna.
Hijabi kawai ta zira ta d'auki mami suka tafi.
Bayan har sun wuce ne malika ta fito cike da murna don a lokacin da su Rynt sukayi ihu har kunnenta yaje sae ta d'auka ko ihun hauka ne ta jiyo sunayi.
Ta tafi kitchen ta same shi kaca kaca tray yayi nasa gefe taliya ma haka da kuma teddyn mami,nn ta kwashe da wata irin dariya tace"lallai aiki yayi kyau kmr yankan wuqa wata qil loma d'aya kawai sukà yi amma har sun bi sun haukata kitchen hk yanzu koina suka nufa ne oho Allah yasa ma sufi ruwa gudu"
Daga nn ta tafi d'akin Rynt don ta qara tabbatarwa kanta ta samu kuwa koina basa nn har bathroom,
farin ciki taji fal har ranta don sae kwasar dry take tana fad'in"matsiyaciya bake ba mijina har abada kai ko a lafira wlh, bari ma na kirashi naji ko ya isa lafiya.
Nn ta kira man suka jima suna waya cike da nishad'i byn sun gama tasa aka gyare kitchen tsaf ta kuma kira kuku a cewar ya dawo yaci gaba da aikin sa.
Sae a bayan snn ta kira pretty ta gaya mata sae dariya suke ta kwasa.
Sae dai bata snr da ita cewa har da mami ba.
Rynt kuwa suna zuwa gidan inna suka sami nasir a can shine ya d'auki mami suka je asibiti akayi treatment nata suka dawo.
Da yake inna tasan mohd yayi tfy tace da Rynt suyi zaman su har sae idan ya dawo sae su koma,har ma take cewa nasir yaje da Rynt gidan ta d'ebo musu en kyn sawa,
hkn kuwa yayi ma Rynt dad'i sosai duk da bata san ko kwanaki nawa man zaiyi bai dawo ba.
Da byn sllr isha'i ne suka je gidan Rynt ta d'ebo musu kayan sawa ita da mami sae dai bata had'o musu da uniform ba sbd an kusa shiga weekend kuma ta fiso sae mami taji sauqi snn ko zasu koma sbd ba wani sosai d'in nn ta qone ba.
Shigar su gidan har fitowar su basu had'u da kowa ba sae mai gadi kad'ai.
Bayan sun koma gidan inna ne nasir ya koma gida ,pretty tazo da murna ta tarbe shi ta kuma kawo mishi abinci ,ba kmr kullum da sae yace takawo mai take kawowa ba.
Zuba mishi abinci take har ta gama idonsa na kanta ,sae da ta zauna ne yake cewa"wae yau wane irin farin ciki ne kike ciki haka naga har bakin ki baya rufuwa,kallon sa take tana murmushi tace"ba komai kawai dai kati nake so zan kira umma,tun d'azu nake jiranka da kace zaka turo min naji shiru.
Nn yasa hannu a aljihu ya ciro kati ya miqa mata snn yace "kwata kwata mantawa nayi wlh"tace"to ngde"snn ta tafi d'aki ta sanya kati ta kira ummarta tana gaya mata lbrn da malika ta snr da ita,umma tace"da kyau qwarai kaddai ki sake Nasir yaji tace" haba ina hauka ne umma aini bana son kowa ma yaji har sae tayi nisanda ba'a iya gano ta ,umma tace"ai ta tafi kenan ba dawowa er matsiyata taje can ta qarata ba ita ba d'ana bare a tatse min shi"
pretty ta kwashe da dariya tace"umma zan kiraki anjima naji nasir na qwala min kira.
Nn suka katse wyr ta tafi gun kiran nasir da ta samu ruwa ne yake buqata.
Bayan kwana biyu da fauruwar hakane da yamma sosai man ya dawo daga tafiyar da yayi.
malika ta tarbe shi sae murna take tana wani nn nn dashi don kawai ta samu ta mantar dashi komai sbd bata son yayi saurin gano su Rynt basa gidan har dai mami da ta kasance abokiyar cin abincinsa.
Shi kuwa a gjye ya dawo shiyasa sam bai leqa d'akin Rynt ba sae a washe gari da ya dawo sllr asuba ya shiga bai gansu ba,yaje koina a gidan basa nn .
Da mamaki yaje yana tmbyr malika cewa ina wnn yrnyr ta tafi tunda safe haka?ta6e baki tayi snn tace"oho kawai dae tun rnr da kayi tafiya itama tasa qafa ta fita"yace"tasa qafa ta fita kuma shine har yau bata dawo ba,d'ibar kayanta tayi ta tafi dasu ko yaya? Oho ni ina zan sani Yace" lallai yrnyr nn ta raina ni da yawa wlh"
Daga hk ya wuce d'akinshi rae 6ace ,malika kuwa ta bishi da ido ta6e da baki.
Sae guraren 11 man ya fita gidan bai zarce koina ba sae gidan inna.
Ya sami inna, nasir, Rynt ,da kuma mami a nn harabar gidan sun fito zasu shiga mota.
Yana fitowa mota mami taje da gudu ta tarbo shi ya riqo hannunta suka qaraso gurin su Rynt .
Bayan sun gama gaisawa shida nasir da inna har suna mai ya hanya yace dasu alhmdlh snn yaje gab da Rynt ya tsaya yana mata kallon tuhuma,sau d'aya ta kalle shi ta sadda kanta qasa.
Mohd ya maida duban sa gun inna yace"inna me yrnyr nn taxo yi a gidan nn?tace"ayyo ai da baka nn ne tsautsayi ya sami mami ta qone a hannu duba ma kaga ga hannun nn ta fad'i hkne had'e da riqo hannun mami ta nuna mae ya duba hannun yaga qonuwar ba sosai bace kuma har ta soma warkewa dan kad'an ma ya saura,
yace"garin ya hk ta faru, Rynt ce tayi mae bayani inna ta d'aura da cewa shine nace suyi zaman su har sae ka dawo tukun tunda ba mae kula dasu can, yace"haba inna ai ko nasir mai zuwa yana duba su ne ba sae kin wani ce su zauna a nn ba"
Inna tace"yo kai Muhammadu kai kafi son kullum mutum yayi ta zama qunqushe cikin gida baya fitowa yaga en uwa"
A d'an qufule yace "shike nn inna naji yanzu ina kuma zuwa kun wani kwaso ku duka haka"
Sae da inna ta washe baki snn tace"wae zamu tafi ne gurin su saliha kasan yau ake bizitin "
yace"inna haka ai sae ku cika musu mkrnta ku kuje gida ma suje haba kar kusa a d'auke ku gidadawa mana.....yo muhammadu alqawari fa na musu akan zanje ko so kake na karya?
Yace"bance ba amma dae bazaku je da wnn yrnyr ba"ya fad'i hkne tare da nuna Rynt wacce tayi saurin d'agowa ta kalle shi yayinda inna ta gwalo ido cike da masifa tace"kan me! yace"kuje kawai ni zan kawo ta daga baya"
Inna tace"bakaji da kyau ba tare dae zamu tafi"
Nasir yace"Aa inna wata qil akwai unxurin da yake da shine"
Tace"yo kai baka san hln muhammadu bane, ba wani uzurin da yake da hana mata tfyr kawai yake sonyi"
Nasir yace" inna kawai dae muje tunda yace zai kawota d'in ai zai kawota"
Inna bata wani gamsu sosai ba amma hk tayi sallama da Rynt a cewar sae sunzo.
Daga nn suka shiga mota ita da nasir har mami.
Rynt kuwa ta kalli man idonta tap da qwalla sbd tasan hanata zuwan ne yayi,kallonta yake ta kauda kanta cike da son ta fashe da kuka amma ta danne sbd mami da taji ta qwala mata kira tana mata bye bye nn ita ma ta shiga yi mata bye bye har motar su tafita ta sake kallon man tare da fashe mai da kuka marar sauti,ta shiga roqon dan Allah yayi hqr ya barta taje bai kulata ba sae hannunta yaja zuwa mota tirje mai take amma haka ya d'ura ta mota ya rufe sae jin yayi ta fasa ihu yayi saurin bud'e gambun yana tmbyrta lafiya ?
bata
iya bashi amsa ba sae fitowa tayi ta fad'i nn qasa riqe da qaramin yatsanta na qafa sae kuka take tana yawo da qafar ,man ya rikice yana tmbyr mene ne wae tace"wani abune ya cije ni..... What bana son qarya fa a motar tawa! Tace"wlh Allah kuwa ka duba zaka ga koma mene ne, ba musu yaje yana duba motar tashi da ta kasance tsaf tsaf sae kawai yaga kunama ai kuwa da mugun mamaki yake ci gaba da kallonta yana kuma mamakin ina aka shigar mae da mota da baya nn har kunama ta sami damar shiga ciki kaddai d'an iskan driver ya samu mai shigar mae da mota koina ya samu,tsaki ya buga had'e da ciro takalmi ya kashe kunamar snn yayi kan Rynt da sauri ya cire necktie d'insa ya d'aure mata yatsa ya samu da qyar ta shiga motar don sae kuka take ita bazata sake shiga motar ba.
Bayan ta shiga motar yaja motar da sauri sae chemist aka mata allura a yatsar aka kuma bata magani snn sukayo gida wacce koda suka iso gidan tuni Rynt tayi bacci da kanshi ya d'auke ta ya shiga da ita gidan yayi kici6is da malika zata fita.
Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 1/31/2017]
```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```
🔮🔮🔮🔮
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.