Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 22 of 56
*page* *```40```*
Waya malika keyi bata san lokacinda wyr ta sa6ule a hannun ta ta fad'i qasa ba.
Bata damu da kula wyr ba sae kallon Rynt take da mugun mamaki tace"kai! me zan gani!
kan uba! badai wnn abar ce nake gani ba kuma d'auke a hannun ka!
Kallonta kawai mohd yayi ya ra6a ta gefenta ya wuce, bai zarce koina ba sae d'akin Rynt yayinda malika ke biye dashi cike da masifa tana mae tambayoyi ,sae da ya ajiye Rnyt snn ya jawo hannunta suka baro d'akin suna saukowa downstairs ta wani fizge hannunta da qarfi snn tace"kamin bayani nace a ina kaganta ne wae!da har zaka wani tallabota haka!
Yace"ha'a! a ina kuwa banda gidan inna! Da mamaki tace"gidan inna kuma?yace"eh mana da to ina zan ganta a tunanin ki? A d'an daburce tace "dole nayi mamaki mana byn nsn.....sae kuma tayi saurin katse kanta da cewa"abinda ma yafi d'aure min kai shine ya akayi ka tallabota wae?
Yace"bacci tamin a mota....what!amm kaji kunya wlh ai ko gawa ce wlh bai kamata ka zamo d'aya daga cikin masu tallabar gawar ba bare wae don ta ma bacci a mota iyye lallai wlh na yarda yrnyr nn ba'a banza ta bar ka ba!
Tsaki kawai ya buga ya fita yana qwalawa drivern sa kira.
Da sauri driver ya qaraso gare shi man ya kalle sa a fusace snn yace"dan gidanku ina ka shigar min da mota ne da bana nn yace"wlh koina ban shigar ma da mota ba yalla6ai!mohd yace wlh idan kamin qarya a bakin aikin ka tayaya to zan sami kunama a mota ta ka wani cemin bakaje da motar koina ba!
Driver yace"wlh na rantse yalla6ai ba inda naje da ita amma kuma nayi mamakin da kace ka sami kunama a ciki sae dae kuma gsky nasan jiya da dare na wanke motar har ma na shanya car mats akan flowers kuma gskyr magana da suka bushe ciro su kawai nayi na maida mota ba tare da na kakka6e ba don ban ko kawo cewa wani abu zai hau akai ba,nn kawai mohd ya shiga qwalawa baba mai gadi kira, wani dattijo yazo da sauri zai durkusa mai, mohd yayin saurin cewa"a'a basae ka durqusa min ba ina so zan kora ma bayani ne akan flowers d''in gidan nn ,bawai aikinka kawai ka riqa basu ruwa ba,
har tsaftar su sae ka kula da ita inace har maganin qwari sae da na siyo na baka wanda ga dukkan alama baka amfani dashi Baba, wlh haka ne yaro amma zan kiyaye daga yau ayi hqr,mohd yace"kaga Baba idan har kasan baza ka iya kula da flowers d'in nn ba kawai ka tsaya a iya gadinka na samo wani wanda zai kular min da flowers"
Baba maigadi yace"yaro wlh nayi ma alqawarin zan kula dasu yanda kake so"
Yace"to baba yanzu kaje ka saka maganin da na baka snn ka share duk wani datti dake qarqashin flowers d'in yace "to shikienan"ya tafi cikin hanzari yayinda man yace"da driver kai kuma kaje ka bud'e boot d'in motar ka ciro wnn car mat da na kashe kunama akai ka wanke shi tas snn itama motar ka bincika min ita da kyau ka kuma sake wanke ta then ina warning d'inka akan kar ka sake maida min abubuwan mota haka kawai ba tare da ka kakka6e ba idan ba hk ba wlh a bakin aikin ka .
yace "inshaAllah yalla6ai an gama"
Nn mohd ya juya ya koma cikin gida.
Malika kuwa lokacinda man ya buga tsaki ya fita taji kaman ta fasa ihu don takaici ga kuma tsananin mamakin da take d'auke dashi na ganin Rynt bata haukace ba kan dole ta duqa ta d'auki wyrta taje d'aki ta kira pretty ta gaya mata abun mamaki da haushi da suka faru da ita yanzu, pretty tace"abin da d'aurewar kai wae ma kin tabbatar taci abincin kuwa? Hm pretty ina d'aki fa na jiwo ihunta kuma koda nazo na sami kitchen duk a hargitse na kuma duba koina a d'akinta bata nn"pretty tace"me man yace miki taje yi a gidan inna? Ni ina naga natsuwar tmbyrsa haka don wlh ji nayi kmr zuciyata zata fashe a lokacin da naganshi d'auke da ita gani kuma d'auke da mamakin ya akayi ya samota don tuni na gama sata cikin jerin shafaffin mutane sae dai kuma a lokacinda na ganshi d'auke da ita nayi tunanin ko tsinto ta yayi garin haukarta shine aka mata allurar bacci,wae sae yace min bacci tamai a mota,pretty tace"kinsan hln yaya da baqar magana amma kuma dole idan taci wnn abinci sefa ta haukace kuma baxa a ta6a samota ba sbd qa'idar maganin kenan but yanzu kije gun yaya cikin hikima da nuna komai ya wuce a gurin kiji shin me taje yi gidan inna da har tayi kwanaki bata dawo ba,malika tace shikenan i will call u back idan nayi hkn.
Nn suka katse wayar ta nufi d'akin man ta same shi zaune kan sofa ya tasa 'ya'yan fruits gaba yana sha.
Taje gab dashi ta zauna ya kalle ta sau d'aya ya kauda kai.
Hannun takai ta juyo fuskar shi saitin fuskarta yayinda ta qirqiro hawayen qaryanda suka cika mata ido tap inda cikin muryar kuka tace"my man na fhmci ka daina sona kwata wata yanzu wnn abar kake so"
Ajiyar zuciya ya sauke yana mai kallon yanda hawaye suka fara sauka akan kumatun ta
yace"malika ta yaya kike tunanin zan daina sonki naso wnn abar da kwata kwata kinsan ita ba tsarina bace"
Tace"idan baso ba to meyasa don tayi bacci zaka wani d'aukota ai tashin ta ya kamata ace kayi,malika nifa tausaya mata kawai ne nayi sbd allurar baccin da take d'auke da ita,
Allurar bacci kuma?eh kunama ce ta harbe ta shine da muka je chemist nasa aka had'a mata har da allurar bacci,amma ai gwanda kabarta a motarka idan tafarka ai ta shigo da kanta dn sam ba ajinka bace a ganka d'auke da ita,yakai hannu yana share mata hawaye yace"naji abar zancen ya wuce"
Nan ya rungume ta sukayi shiru sae can malika ta kalle shi tace"hln me taje yi gidan inna da har ta kwana biyu ko inna ce ba lafiya? Yace"mami ce ta qone a hannu "garin me? Nn ya gaya mata bayanin da Rynt tayi mae tayi tsaki a ranta wacce a cikin ran nata take cewa
_"matsiyaciya bata ci ba kenan ai da na nasn hk zata faru da bazan bar mami ta tafi ba"_
Nn ta buga tsaki a fili zata fita man yace"yadai lafiya? Tace "haushi ta ban ne wlh in banda gidadanci teddy ce abin tsoro da har zata 6arar da abinci har ta kai ga qona mami"
Kallonta kawai man yayi yakai hannu kan wyrs da ta shiga ruri ya d'aga ita kuma ta fita taje d'aki ta kira pretty byn pretty ta d'aga tace"ke ashe matsiyaciyar bata ci abincin ba 6arewa yayi har ya sami mami a hannu ta qone shine suka je gidan inna"pretty tace"haba kam ni nsn idan taci sae dai wata ba ita ba,amma kar ki damu yanzu zan kira umma na gaya mata ta kar6o miki wani,malika tace"to shike nn bye tank u"
Ta katse wyr had'e da tsaki tana fad'in"niko kun sake kawo min maganin ba aiki zanyi dashi ba tunda har ana iya gujewa sharrin sa amma nawa sharrin ko waye ubanta tayi kad'an ta guje mishi wlh.
Mtsalar kawai ban san yaushe zan sami ciki ba ga man Dr ne bare na iya cikin qarya har na cimma burina bai gano ni ba....qarar wyrta ne ya katseta ta d'aga wyr had'e da shiga bathroom
Rynt kuwa tun lokacinda da man ya ajiye ta take bacci har akayi zuhur bata farka ba.
Man ne ya shigo d'akin wanda ya fito daga masallaci kenan yaje gab da ita ya zauna yana mae duba yatsar wanda yana kai hannunsa akan yatsar ne Rynt ta farka had'e da tashi zaune snn takai idonta akan yatsar da take d'an d'auke da kumburi, man yace"har yanzu kinajin zafin harbin ne? Ta girgiza mae kai snn tace kawai dai allurar tana min zafi"
yace"tashi kije kiyi sallah zai daina ne"
Ba musu ta tashi ta nufi bathroom inda kallonta yake har ta shige bathroom d'in snn ya tashi ya bar d'akin.
Tun daga lokacin bai sake komawa d'akin ba sae a washe gari da safe su Rynt na shirin school ita da mami sae ga man ya fad'o d'akin Rynt tayi kmr bata ganshi ba sae jin tayi ya jata ya zaunar ya durqusa had'e da riqo qafarta yana duba yatsar ya kalleta snn yace "kumburin ya sauka kenan ? Ta gyad'a mai kai tare da yunqurin tashi ya maida ta had'e da fad'in "zafin allurar fa?shaye da toka ta kalle shi kmr shima yanda yake kallonta ta kauda tata fuskar snn tace"ta daina min zafi"
Nn ya tashi tsaye ya kalli mami da taxo gurin shi tana fad'in"yaya amma yau kae zaka kaimu school ko?um um mami driver dae zai kaiku,uhm uhm pls yaya ka kaimu kar amana bulala kan kwanakin da mukayi bamuje ba kasan inna ta gaya ma kuma idan ba'ayi musu bayani ba zasu dake mu ne,yace"to shike nn idan kun shirya ku sameni a downstairs,tace"to yaya yanzu da mun gama shiri zamu zo"
Nn ya fita sukuwa suna gama shiri suka je suka sameshi yakai su school.
Bayan wata d'aya da faruwar haka Alhmdlh komai na bi dai dai yanda Rynt keso na harakar karatunta wacce ashe kwanyar ban mamaki ce da ita don qwarai qoqarinta ya shiga bayyana sbd duk wata test ko Assignmen kaf take lashewa haka ma class duk wata tambaya da malamai keyi ita ke farkon bada amsa ,
Kan qoqarinta ne wani malami yake mutuwar sonta sbd kaf makarantar ba wanda yasan ita mtr aure ce har frnds d'inta kuwa.
Kullum idan taje school sae ya aika a kirata amma bata zuwa, ba yanda bai yi ba ya samu ta kulashi ko sau d'aya ne amma fir taqi.
Rnr wata alhamis yayi aike har ya gaji taqi zuwa kan dole yaje da kanshi har class d'insu ya samu tana wani Assignment yaje kan desk d'inta ya d'aura hannyensa akai had'e da russunawa yana mata magana cikin yanayi na kmr wanda ke duba mata Assignment d'in itakuwa tayi kmr bada ita yake zancen ba sbd dama tsanar sa take tun farko dmn kowa ya sanshi makarantar d'an iska ne kuma mugu.
Da yaga taqi kulashi ne ya kar6e Assignment d'inda takeyi ta tashi a fusace cikin d'aga murya tace"kaga malam nifa ba irin en matan nn bace don hk ka daina bibiyar rayuwata haka nagaji!"
Mgnrta ta tinzirashi sosai musamman da yaga students duk hnklin su yayo kansu nn yasa ta kneel down ya nemi bulalar dorina sae zabgarta yake har sae da ya gaji don ganshi yabarta sae kuka take en class na bata hqr a cikin haka ne aka buga tashi wacce har aka zo d'aukar su suka isa gida kuka take ta tafi d'aki aguje zata fad'a kan bed sae jin tayi kawai an fizgota koda ta duba man ne yajata zuwa jikin shi ,
sosai taso qwatar kanta amma ta kasa sbd riqonda ya mata kan dole ta fad'a kan qirjinsa ta fashe mai da wani sabon kuka.
A hnkli ya kai hannunsa ya jaye hannuwanta da tasa a tsakanin qirjinsu ya shigar da ita gabad'aya cikin qirjinsa yana mai tmbyr abinda aka mata,saurin ture shi tayi daga jikinta ta nufi bathroom da gudu.
Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 2/1/2017]
```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```
🔮🔮🔮🔮
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.