Complete Hausa Novels

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 40 of 56

*page 78*

Da isar ta ne jirgin nasu ya sauko mutane suka fara firfitowa kan farin ciki bakin ta baya ko rufuwa sae rarraba ido take ta inda zata hango mohd.

Kai tsaye duk wani farin cikin nata a take ya tafi numfashinta ya nemi ya d'auke,

ganin mohd tafe cikin baqar suit maqale da Ryynt a jikin sa tana sanye da arabian gown baqa tayi rolling da black top kmr wata balarabia dan gabad'aya ta canza mata ta qara kyau da haske da ita har mohd d'in sae sheqi suke ga wani murmushi da suke da ya qara musu kyau suna tako cikin natsuwa.

Sam malika ta kasa gazgata abinda take gani musamman hannun mohd da ta hango ya zagayo dashi ta kunkunmin Ryynt yazo dashi har izuwa kan tulun cikinta da ya fito 6aro 6aro da cikin ne abinda yafi matuqar bata mamaki don har suka qaraso ta kasa gazgata abun wae kodai mafarki ne ba gske ba gashi ko qaramin yatsanta tama kasa motsawa sae dasqarewa da tayi a guri d'aya ta kafe su da ido tana kallo Nasir yaje ya tarbe su cike da murna.

Yayin da su saliha da mami dake tare dashi suka qanqame Ryynt cike da murnar ganin ta kafin suke zuwa gun matar Amir itama suka tarbe ta.

D'auke da murmushi mohd ke kallon malika dake qarasowa gurin su wacce tana isowa cikin tsananin 6acin rae ta damqo suit jacket d'in mohd da hannuwanta duka biyu ta jijjiga shi tace"gaya min shin mafarki nakeyi ko kuwa da gaske ne dae wnn abar ce nake gani a tare da kai!

Da qarfi mohd ya buge hannuwanta ya jawo Ryynt zuwa jikin sa yace"kin ganta gata ba mafarki kikeyi ba dagaske ne kuma wlh kar ki kuskura ki sake kiranta da wnn abar idan ba haka ba wlh zanyi mugun sa6a miki very stupid!

Nan kawae malika tayi kukan kura zata shaqo wuyan Ryynt man yayi saurin ture ta gefe

snn ya nuna ta da yatsa yace" Ryynt she is my wife n my life bazan ta6a yarda kici zarafinta ina tsaye ba and idan har kinsan tashin hankali ya kawo ki maza bar gurin nn in daina ganin ki ko kuma wlh na miki dukan tsiya a nn!

Tsaf tasan zae iya aikata abinda yace ta kalli Ryynt ta qyasta yatsunta tare da nuna ta tace"wlh wlh yau sae na zamo ajalinki"

Daga haka ta wuce fuuu a fusace.

Mohd dake kallonta ya buga tsaki dan shi a shirme ma ya d'auki zancen nata ya kalli Ryynt wacce still tana a jikin sa yace"Ryynt are u ok bata ta6a ki ba dae ko?

Ryynt ta girgiza kanta tana qoqarin maida hawayen da suka cika mata ido ba wae don ta tsorata da jin furucin malika ba sae don ko kad'an bata ji dad'in abinda ya faru ba har dae yanda gabad'aya gurin idon kowa ya tsaya a kansu har ma wasu na nuna su suna magana.

Nasir da Amir ne suka ce da mohd "wae me yake faruwa ne?

Mohd ya buga tsaki yace"da Allah ku fita batun mahaukaciya kuzo mu tafi"

Daga haka suka wuce ba wanda ya sake cewa komai.

Amir da matar sa da d'ansa motar su suka shiga da driven su yazo da ita yaja su zuwa family houshe.

Mohd da Ryynt kuwa motar Nasir suka shiga dasu har su saliha wanda basu zarce koina ba sae gidan inna wacce tana ganin Ryynt ta washe baki cikin tsananin murna suka rungume juna inna ta d'ago riqe da baki sae kallon Ryynt take cikin jin dad'i ganin yanda kallo da'ya zaka yiwa Ryynt kasan cewa tana samun matuqar kulawa da jin dad'i musamman yanda fatar ta tayi smooth da haske tayi fresh da laushi kmr ftr sabon jinjiri sae sheqi take tana qyalli.

Washe da baki inna ta qwalawa baaba hurera kira baaba hurare taxo da murna ta musu sannu da zuwa wacce itama ta kasa rufe baki sae kallon yanda Ryynt ta canza take.

Washe da baki inna tace"kema kinga yanda Rayyanah ta dawo ko awa wata balarabiyar saudia ai Alhamdulillahi ba abinda zance da kae Muhammadu sae nace Allah shiyi maka albarka dmn ba makawa Ryynt ta sami sauyi da kulawa a gurinka haqiqa naji dad'i wlh ubangiji Allah sarkin halitta shi qara yi maka albarka.

Mohd yace"Amin Amin inna"

yayinda yake kallon Ryynt dake murmushi tana fmn 6oyon tulun cikinta da take jin kunyar a gani.

Kai tsaye taga mohd ya d'aura hannun sa akan cikin nata yace"inna kalli d'an jikanki ki fa yanda ya taso"

Wata irin kunya Ryynt taji kmr ta nutse tayi saurin ture hannun sa zata bar gurin mohd ya janyota zuwa jikin sa yana dariya,a shagwa6e ta fashe masa da kuka ta qwace kanta ta koma jikin inna ta 6oye fuskarta a qirjinta tana ci gaba da kukan da ta soma maida shi da gaske don rugumar da ya mata yasa ta qara shiga wata kunyar.

Ya riqo hannunta yace"zo ni na 6oye ki a nawa qirjin tunda kunya kike ji.

Da sauri Ryynt ta fizge hannun ta yayinda inna ta girgiza kanta d'auke da murmushi tace"Allah ya shirye ka muhammadu snn ta shafo bayan Ryynt tace"qyalesa Ryynh yi shiru daina kuka ae yau ya jawa kansa don baza ki koma gidan sa ba

sae ya zo biko"

Mohd yayi saurin kama kunnen sa yace"Aa inna amin afuwa bazan sake ba na tuba"

Inna tace"kaja kunnen ka ma yafi na zomo tsayi bazan haqura ba sae kazo biko tunda har kasa min ita kuka.

Mohd ya shagwa6e fuska kmr qaramin yaro yace"inna nine fa"

Tace"kaiwa daga ina"

Mohd yace"mai gidan naki kuma inna Baaba hurera kinaji fa"

Baaba hurera dake kallon su ita da su Nasir suna murmushi ta girgiza kanta d'auke da murmushi taje da sauri dmn kawo musu abinci da lemu da ruwan sha kmr yanda inna ta umarce ta.

A nn tsakiyar falon aka shimfid'a qatuwar darduma Baaba hurare ta jera kulolin abinci akai da ruwa da lemu wanda dama musamman dan su aka had'a.

Zasu fara cin abinci knn wayar mohd ta shiga ring koda ya duba mae kula da harkokin gidan sa ne ya kirashi yake snr dashi irin 6arnar da malika ke aikatawa a gidan shi don sae farfasa abubuwa take.

A natse ya kalli Nasir yace"plz bani makullin motar ka"

Ba musu Nasir ya miqa masa makullin yace"lafiya dae ko"

Yace"ba wani abu bane yanzu zan dawo inshaa Allah"

Daga haka ya fita Ryynt ta bisa da ido sae ga inna ta fito daga ciki d'auke da fruits salad mai sanyi da ta ciro a cikin fridge taga bata ga mohd ba tace"Aa ina kuma muhamnadu ya tafi"

Tayi mgnr ne tana mai kallon Ryynt wacce bata iya cewa komai ba sae Nasir ne yace"an kira sa ne ya d'an fita ya dawo"

Inna tace"ayyo"

tare da ajiye fruit salad d'inda ke hannun ta.

Mohd kuwa yana isa gida yayi tsaye a cikin falo hannuwan sa cikin aljihu yana kallon yanda gun dining duk yayi kaca kaca malika duk ta watsar da liyafar da tasa aka shirya mae ta kuma farfasa duk sabbin kayan da yasa aka zuba a falon na gyaran gidan da yasa akayi gabad'aya duk wani abin fashewa bata bar shi ba har TV kuwa.

Yana tsaye sae gata ta fito kitchen riqe da wuqa sabuwa dal zir sae qyalli take.

Tayi kmr ma bata ganshi ba ga mamakin sa sae sauri take ta fita yayi hanzarin fizgota yace"ke ina kuma zaki je da wuqa"

Bata masa magana ba sae qwatar kanta da take qoqarin yi ya qara damqar ta had'e da daka mata tsawa yace"ina zaki tafi nace!

Ta fizge kanta tace"so kake kaji to gurin wnn abar zan tafi don wlh yau bazan barta da rai ba sae na hallaka ta na kuma hallaka abinda ke cikin cikin.....bata qarasa fad'a ba taji saukar wani irin gawurtaccen mari ya kuma ja hannun ta ya tafi da ita sae fizge fizge take har ya kaita d'akin ta ya jefar ya fito ya rufe d'akin ya xare key ya saka a aljihun sa ya fita yana mamakin hauka da baqin kishi irin nata.

Gidan inna ya koma Nasir ya kar6i makullin motor sa ya fita zuwa aiken da inna ta mai wacce tana bashi saqon ta koma daga ciki sbd wayar ta da taji tana ring.

Ya kasance falon ba kowa don mohd yana fita Ryynt taja su saliha suka tafi d'akinta da inna tasa aka share tun jiya da taji zasu dawo.

Ya nufi d'akin kai tsaye ya same su zaune su uku suna cin abinci a mazubi d'aya sae firar bayan rabuwa suke cike da nishad'i.

Ba tare da yace musu komai ba ya riqo hannun Ryynt ya fito da ita zuwa falo suka zauna kan darduma da abincin sa ke ajiye da aka sa d'ayan plate aka rufe ya bud'e abincin yace"muci wnn sae ki bar musu wancan suci gaba da ci"

Tace"meyasa abincin fa yana da yawa baza su iya cinye sa ba na mu uku ne muka d'iba"

Yace"eh ki bar musu kawae"

Ya fad'i hakane tare da d'ebo abinci a spoon zae kai bakinta tace"mk nifa ina jin kunyar inna tazo ta same mu muna cin abinci a tare"

Nan kawae ya tashi yaja hannun ta riqe da abinci suka tafi d'akinta da niyar suci a can ,

gashi ita ko a gaban su saliha d'in bata iya cin abinci a tare dashi,

tace"plz Mk tafi kawae kaci abinka ni sae na ci gaba da ci tare da su saliha kaji.

Man da har ya zauna kan sofa ya kalleta kawae bae ce mata komai ba ya tashi ya fita d'auke da alamar fushi a fuskar sa.

Jiki sanyaye Ryynt ta zauna dmn ci gaba da cin abinci tare da su saliha.

Saliha dake kallonta tace"is better ki tashi kije ki bashi haquri kici abincin dashi dmn ga dukkan alama fushi yayi"

Ryynt da qwallah suka taru a idon ta tace"Saliha kunya nakeji da dae mu kad'ai ne zan iya"

Saliha tace"olryt bari to mu koma falo nida mami sae ku dawo a nn kuci"

Saliha ba haka nake nufi ba ,saliha da ta fhmce ta tace"to ai sae ki zauna mijinki na fushi dake mala'ikun Allah na tsine maki"

Ryynt ta kalli saliha ,mami tace"kije mana Anti meye abin kunya dan kinci abinci da yaya nima fa da muna gidan sa a tare muke cin abinci kin sani"

Ryynt tayi d'an guntun murmushi tana kallon mami snn ta tashi taje falo ta samu mohd ya mayarda abincin ya rufe zae fita don har ma yakai bakin qofa.

Ryynt ta kira sunan sa a hnkli.

Ya tsaya kawae ba tare da ya juyo ba.

Taje ta riqo hannun sa ya juyo yana kallon ta tace"MK ina zuwa kuma baka ci abinci ba?

Yace"zanje inda za'a bani ba tare da na roqa ba"

A nn tayi saurin sadda kanta qasa d'auke da hawayen da suka cika mata ido don sae taji wani irin kishi duk da taga yanda suka kwashe shida malika a airpot.

Murya can ciki tace"yi haquri muje na baka"

Yace"tafi kawae kici inda kike son ci d'in ni ki barni na tafi abuna"

Hawayen da suka cika mata ido ne suka silalo a hnkli ta share hawayen jiki sanyaye ta juya zata bar gurin,

Jiki sanyaye mohd ya riqo ta yace"meye na kuka kuma Ryynt inace kinfi ra'ayin kici abincin a tare da su shiyasa nace ki tafi"

Ryynt tace"Allah ba wani nn fushi kayi "

Ya janyo ta zuwa jikin sa yace"to yi haquri kuma ni ba fushi nayi ba dama na gwada ki ne kawai inga ko kina son mijinki da gaske sae naga ashe ke dad'i miji ce da ba kya son ganin fushin sa.

Da wasa ta sha toka tace"me kake nufi?

Ya d'aura mata kiss kan lips yace"abinda kika fahimta shi nake nufi"

A shagwa6e ta maqale kafad'a tana doka qafafun ta qasa tace"wlh Aa ni ba dad'i miji bace"

Ya lakato hancinta tare da fad'in"ba wani nn na gano ki ae"

Kuka ta fashe dashi ta shiga kai masa duka irinta ta shagwa6a tana fad'in"wlh Aa ni ba dad'i miji bace"

A nn Mohd ya shiga kare dukan sae dariya yake ita kuma sae ci gaba da dukan sa take tana fad'in ita ba dad'i miji bace shidai ne haka ba ita ba nn ya kama yatsan ta ya gantsara mata d'an qaramin cizo ya gudu ya barta sae kukan shagwa6a take tana yarfi da hannu yaje kan darduma ya zauna tabi shi ta kama yatsan sa ta rama ya shiga yarfi da hannu sae dariya take masa dan da gaske ta cije shi, ganin zae kama hannun ta ya rama ta tashi da sauri ya biyota dai dai inna ta fito taje bayan inna ta la6e sae gwalo take masa tañà dariya.

Sorry 4 dis one

Billy giro😊

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

[10:05PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.