Complete Hausa Novels

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 30 of 56

*page* *```48```*

Ta sami Rynt ta tashi tana linke carpet d'in sallah.

Inna ta kar6i carpet d'in ta koma shimfid'a mata a nn kusa da gefen gado tace da ita "zauna bari naje na kawo maki abinci kici ko"

Rynt ta gyad'a mata kai snn ta zauna,

inna ta kai hannu nn kusa da bedside drawer ta d'auki abincin rnr da Rynt bata ci ba taje dashi kitchen ta kawo mata tuyon shinkafa da miyar ganye wacce taji qassan nmn rago .

Ta kai kusa da Rynt ta ajiye snn ta kawo mata ruwa da kunu da magunguna a cewar idan ta gama cin abinci sae tasha.

Sae da Rynt ta yiwa inna godiya snn ta kai hannu had'e da bisimillah ta fara cin abinci.

Da ta kammala ne takai kwanika a kitchen ta dawo ta fad'a bathroom tayi wanka koda ta fito ta sami inna na waya cike da murna tana gama wyr ne take ce ma Rynt"Ashe saurin da na Nasiru keyi fatima ce a asibiti shine yanzu aka kirani aka snr dani ta sauka lfy ta sami d'a"

Rynt ta d'an saki fuska snn tace"to Allah ya raya masa shi akan sunna"

Inna ta washe haqora tace"Amin amin ai ba dan dare ba da naje naga sabon mae gidana"

Murmushi kawae Rynt tayi taje ta nemo kyn bacci ta saka ta kwanta.

Washe gari Rynt taji sauqi sosai don ita ma ta gyare gidan tsaf ta kuma je kitchen tana ragewa Baaba hurera aiki wacce tana zowa bata fara aiki ba suka tafi gidan su mohd gun barkar pretty ita da inna.

Tana cikin aikin ne suka dawo Baaba hurera ta shigo tana mata sannu da aiki snn tace taje inna na kiranta a falo.

Koda taje falon ta sami inna da Abban mohd taje ta durqusa cike da ladabi tana gaida shi ya amsa mata cikin sakin fuska snn yace"ya jikin naki?

Tace"Alhmdlh"snn yace"dama zançen karatun ki ne tunda kinji sauqi gobe

zan turo driver wanda zai riqa kai ki makaranta yana maida ki,snn kmr yanda ake maki lesson a can gidan nn ma zan nemo maki wanda zai riqa zowa yana maki lesson d'in,snn kuma duk wani abu da kk buqata ki snr da inna sae ta snr dani"

Tace"to Abba nagode"

Yace"shikenan tashi ki tafi"

Bayan ta wuce ne ya ciro kud'i a aljihun sa bandir d'in 1k guda biyu yaba inna yace"d'aya naki ne d'aya kuma ki riqa bawa Rynt d'ari biyar biyar duk safiya ta na samun na cin abinci idan taje mkrnta dn naga mkrntar tasu yini ake"

Ina ta kar6i kud'in had'e da sa mishi albarka yace"nagode inna ni zan tafi"

Tace"to d'an albarka Allah kai ka lfy"

Yace"amin"

snn ya fita.

Ita kuma taje d'aki ta adana kud'in.

*****

Kwance yake kan bed sanye da farar singlet da farin boxer malika ta shigo d'akin ta kalli yanda ya d'ora qafa kan qafa yana mai kallon silin.

Taje ta zauna kusa dashi tana mai kallon fuskar shi snn tace"my man ya kamata ka haqura ka daina tunani akan rashin da mukayi,ai Allah zai sake bamu wani ne komai baqin cikin wnn abar kuwa.

Lumshe idonsa kawae yayi ba tare da yace komai ba tace"ya zancen zuwa gidan naku ?

Yace"ki tafi kawai"

Tace"baza kaje ganin jariri ba knn ?

Kallonta kawae yayi bai ce mata komai ba sae kwanciyar sa da ya gyra.

Tasan ba amsar zata samu ba shiyasa kawae ta tashi tabar d'akin taje ta shirya ta fita.

Gidan su man d'in ta nufa wacce da shigar ta 6angaren su man kai tsaye ta haura sama zuwa d'akin mhfyr man ta bud'e qofar d'akin ta shiga ba ko sallama,pretty dake zaune kan bed tana shayarwa ta saki murmushi tace"sae yanzun"

Sae da malika ta zauna snn tace"hm nida nake ganin ma nayi sammako"

Pretty ta bata jariri tare da fad'in"yaya fa?

Tace"wlh yana can cikin damuwar rashin babyn mu har magana ma bai cika son yi ba"

Pretty ta cije le6e tace"wlh Allah matsiyar yarnr nn taci uban rainin wayo! ni kuna me wae ma har tayi nasarar 6arar miki da ciki?

Malika ta ta6e baki had'e da murmushi snn ta duba koina idan ba mai ganin su ta kai bakinta a kunnen pretty ta rad'a mata magana ,pretty ta fiddo ido had'e da washe baki snn tace"kai haba!

malika tace"Allah kuwa

snn tace"amma fa bakin ki qanin idonki wlh kar ki bari kowa yaji zancen nn don ina gudun ya koma kunnen yayanki"

Tace"haba dan Allah sae kace ban san me nakeyi ba ai ko umma bazata ji wnn zancen ba,,kuma kin san Allah da har kin ban haushi da naga na koma kai miki magani amma naji shiru ashe kinsan abinda kk shirin yiwa matsiyaciyar.

Malika tace"ai ke ajiye maganin gefe nayi nace sae na gwada plan d'ina tukun.

Pretty tace"shiyasa da muka je dubaki lkcn da umma keta masifa tana fad'in duk laifinki ne dan da kinsa mata maganin a abinci taci ta haukace da duk hkn bata faru ba sae naga kin kalle ta kawae kinyi shiru .

Malika tayi dariya tace"wae ina umma take ne ma?

Pretty tace"Wlh tana kitchen da fitar ta mane ba jimawa se kika shigo.

8:30pm

Inna ce zaune a falo ita da Rynt suna cin abinci bayan sun gama Rynt tace"inna nifa gobe bana da kayan sawa idan zanje makaranta duk suna gidan can"

Inna tace"ayyo ai tuni an kwaso maki kayanki suna a d'akin ki nasa nasiru yakai ,

ai a cikin kayan ne ma na d'ebo wasu en kyn sawa nakai miki a d'akina"

Tace"inna kayan mami fa?

Tace"yo ai kaji fa amma bari na kira nasiru naji da yaje kwaso maki kaya har da kayan mami ya kwaso ya had'o ko kuwa"

Nan ta d'auki wayarta ta kira nasir bayan sun gama wyr ne tace ma Rynt yace duka har kyn mami d'in ya had'o ya kwaso wanda tun d'azun yaso yazo ya d'auki kayn nata yakai gida sae bae sami lokaci ba amma yace yanzu zai zo ya d'auki kayan"

Rynt tace"to bari naje na had'a masa kayan kafin ya iso"

Inna tace"to"

Snn Rynt ta tashi ta nufi d'akinta da take zama a daa.

Kan gado ta sami kayan nasu komai har akwatinan lefenta wad'anda kallo d'aya ta musu ta kauda idonta ta d'auki akwatin mami ta bud'e taga komai nata na ciki ta rufe akwatin ta ajiye ta gefe kusa da qofar d'akin snn taje ta bud'e akwatin ta wacce inna ta saya mata ta samu itama komai nata na ciki zata rufe kenan akwatin ta sa6ule ta fad'i sae duk kayan suka fita nn ta hango tsofuwar ajiyar ta ,ta kai hannu a hnkli ta d'auki viva ledar ta bud'e .

Kayan da marigayi anwar ya bata ne a ciki nn ta shiga ciro kayan d'ai d'ai tana kallo.

Hawayenda suka cika mata ido ne suka shiga gangarowa a hankali yayinda ta ciro bandir d'in 1k guda biyu masu d'auke da jini a jikin su nn taji inna ta qwala mata kira tayi saurin mayarda kud'in har kynda anwar ya bata snn ta amsa kiran da inna ke mata had'e da share hawaye ta kama hanya zata fita sae ga nasir ya shigo d'akin yace"har kin gama had'a kayan?

tace"na samu kayan a had'e suke"

Yace "eh hkne ni na had'a kyn tun can sbd a wardrobe d'inta na sami akwatin ta shine na saka mata duk kayan da ke cikin wardrobe d'in haka kema"

Tace"mungode"

Snn yace"zancen da mukayi jiya dake ban manta ba ina son sae na sami lokaci ne sae nazo muje a cire cikin ko?

Tace"to"

Yace"yauwa sae ki maida hnkli ki ci gaba da zuwa mkrnta kinji"

Nn ta gyad'a mishi kae shi kuma yaja akwatin mami ya fita.

Ita kuma taje ta gyra kayan akwatinta da suka zube ta rufe sae dae kafin ta rufe akwatin sae da ta cire kynta na zuwa school ta d'auke su ta tafi dasu d'akin inna.

12:00 na dare

Man ne ya fito d'akin shi wanda bai zarce koina ba sae d'akin Rynt .

A nn bakin qofa yayi tsaye yana qarewa d'akin kallo sae can ya qarasa shiga d'akin yaje gun wardrobes ya bud'e yaga ba komai kaf an kwashe ya maida wardrobes d'in ya rufe .

Har zai fita sae ya hango farar suit jacket d'inshi kan sofa yaje ya d'auki jacket d'in a hnkli yana kallo,

Se kuma yayi saurin kauda idonsa kan jacket d'in ya kuma jefar da ita kan sofa ya fita.

Washe gari da safe Rynt ce ta kammala shirinta tsaf na school inna ta ciro d'ari biyar ta bata Rynt ta kar6i kud'in tace"ba canji ne inna?

Inna tace"canjin me kud'in ki ne fa da zaki tafi dasu makaranta na cin abinci ko basa isar ki?

Rynt ta bud'e ido tace"inna ai kud'in sunyi yawa ai d'ari biyu ma sun isa kuma ina ma da kud'i a hannu na da kin barshi kawae inna"

Inna tace"yo Rynh kud'in hannunki ai naki ne,wad'an nn kuma na cin abincin mkrntr ki ne kabiru ya bayar a riqa baki"

Tace"to inna nagode amma dae zan dawo da sauran canji dan sun min yawa"

Inna tace"to er albarka a dawo lafiya Allah tsare min ke ya kuma bada sa'ar karatu"

Tace"amin inna"snn ta fita ta samu driver na jiranta a qofar gida taje ta shiga motar yaja suka tafi.

Billy giro😊

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.