Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx
Chapter 4 of 56
_*page*_ ```21```
Amma Alhj Allah ya isa tsakanin mu dakai don wnn cutuwa ce wlh!
Cikin nuna fushi Abba ya nuna ta da yatsa yace"wlh Rabi'a ki kiyaye ni da banzan kalaman nn naki dake shirin janyo miki mutuwar aurenki!
Gama fad'ar haka ya tafi kmr wanda zai tashi sama.
Umma kuwà ta bishi da kallo ta6e da baki tace"indai wnn kalmar ce ba yau na saba jinta a bakinka ba bare ta tayar min da hnkli,snn ta kalli mohd da ya shiga cikin tsañanin tashin hnkli tace"kaga kwantar da hnklinka aurenka da malika kmr anyi an gama kuma baza ka auri wnn er qauyen ba indai ina numfashi a doron qasa,kmr wanda zai yi kuka yace"umma ta yaya kike ganin hkn zai yiyu bayan kinaji Abba rantsuwaa yayi kawai ma umma dan Allah ki daina sa bakin ki a zancen nn sbd ko kad'an banji dad'in yanda Abba ya sako rabuwar aure a zancen nn ba .... Yo ai ba yau ya fara ba kuma dan ya rantse sae me! Kaidai tashi ka tafi kawai ai er iskar yrnyr zata dawo daga islamiyya ta sameni.....Aa ki barni da ita kawai umma ni nasan yanda zanyi da ita....ai da ka barni da ita wlh...No umma bana son kwata kwata wani abu ya had'aki da ita ne bare ta raina ki.
6:00pm
Rynt ce tafe kan hnyr dawowa islamiyya ita da munir sae er fira suke mai cike da nishad'i yayinda Rynt ke d'an duba kan titi ko zata hango napep.
Kmr daga sama ta hango motar man tafe ya zo gab dasu ya tsaya kmr mai shirin taka musu qafafu don tsirif ya rage har sae da sukayi saurin ja da baya.
Dukkan su da mugun kallo ya fito yana binsu dashi,yace da Rynt shiga mota"kallon sa ta tsaya yayi ya daka mata tsawa yace"shiga mota nace!cikin 6acin rai taje ta shiga motar ya zagaya ya shiga yaja motar a tsiyace had'e da bazawa munir qura.
Tafiya yayi da ita mai nisa snn ya samu guri ya parker ya kalli Rynt da tun lokacinda yaja motar gabanta ke dukan tara tara kaddai ace ya gane ko ita wace ce,yace"oya cire wnn baqin abun dake kan fuskar ki magana nake son zanyi dake"
Ba musu ta yaye niqab d'inta ba tare da ta kalle sa ba.
Sae da yakai hannu ya d'ago fuskarta yana kallonta shaye da toka snn yace"abu zan nema agunki wanda ban ta6a nema agun kowa ba wato alfarma, alfarmar itace ina son dan Allah idan Abbana ya kiraki ya tambaye ki ko kina sona kice masa A'a shine kawai ni kuma idan kika min haka nayi miki alqawarin duk wani abu da kike so a rayuwa ki tambaye ni zan miki shi koma mene ne kuwa"amma wlh kar ganin na had'aki da Allah ki raina min da wayo dmn duk kika yi gigin amincewa buqatar Abbana sae dai a nemi wata bake ba!
Manyan idanuwanta farare tas take ci gaba da kallon shi dasu snn ta ta6e baki tace"ai sae ka fayyace min komai ta yanda zan fhmta"
Mugun kallo ya watsa mata yace"daqiqiyar inace ke da bazaki fhmta ba ,da Allah ni ftr min daga mota kuma wlh ki tabbatar kinyi abinda na saki!
Ba musu kuwa ta fita motar don yanda taga yanayinsa ko tura ta zai iya yi ta fad'i, sae dai da gani akwai mgnr da takeyi a ranta haka kuma akwai nazarin da takeyi shi kuma mohd har lokacin kallon takaici yake mata snn yaja motarsa a tsiyace ya bar gurin.
Da qyar Rynt taga ta sami napep sbd yanayin anguwar da ba kwaramniya bare abin hawa ya yawaita.
Nazari take yi kam har ta isa gida ko kuma nace har akayi sllr isha'i bata daina nazarin ba yayinda tuni zuciyarta ta ganar da ita abinda ke shirin faruwa sae dai taqi bawa kanta damar amincewa da hkn har sae Abba ya kirata tukun taji koma mene ne.
Tana gama cin abinci Abba ya aiko Ameera yana son ganin ta.
Taje ta same shi shi kadai zaune a falo.
Ta nemi guri a qasa ta zauna ta kuma gaida shi cikin ladabi kmr koyaushe.
Cikin sakin fuska ya amsa snn yayi gyran murya yace"Rynt haqiqa duk mutumin da ya zauna dake zai yi sha'awar kyawawan halayenki da kuma d'abiunki,a dalilin hakane ma yasa nayi sha'awar had'aki aure da mohd,amma kuma ba dole sae idan kina ra'ayi kuma dan Allah kar ki 6oye komai a ranki,dmn ita rayuwar aure wata sabuwar rayuwace da ta banbanta da kowace rayuwa wacce dad'inta ka auri wanda kake so yake sonka, shiyasa nake son ki snr dani gskyr abinda ke ranki ma'ana idan ba kya ra'ayin auren ki da mohd kar kiji shayin komai ki snr dani idan kuma kina ra'ayi sae dai nace Alhmdh dmn zanfi kowa farin ciki da haka.
Tun farkon fara zancen sa ba qaramin girgiza Rynt tayi da jin zancen ba amma sae ta dake bata yarda ya fhmci halinda take ciki ba.
Bata son mohd bata kuma jin zata soshi har abada!amma kuma ko don ta d'auki fansarta a sauqaqe zaisa ta amince da aurensa to kuma ya zata ce da yaya munir dake matuqar son ya aureta.
Duk a cikin ranta take wnn tunanin ,Abba ya katse ta da cewa ke nake saurare Rynt ,sae da ta qara sadda kanta qasa snn tace"na Amince Abba zan aure shi"Abba yace "kin tabbatar Rynt ba cutar kanki kikayi ba? eh wlh Abba har raina na amince.
Wani irin dad'i Abba yaji har ransa, yace"Allah yayi miki albarka Rynt, ya kuma sa ki gama lfy da duniya"da qyar ta iya cewa amin kan kukan da ke qoqarin zo mata sbd tuna baffanta da tayi da kusan kullum sae yayi mata irin addu'ar nn.
Koda ta koma d'aki ba kowa sae tayi kwance abinta tana ta kukan tuna Baffanta har sae da tayi mai isarta snn ta tashi tana tunanin me zai faru idan mohd yaji ta amince da buqatar abbanshi ko ita ma kasheta zai yi kmr yanda ya kashe mata Abbanta.
Billy giro😊
🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮
[2:43PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [ 1/8/2017]
🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮
🔮🔮🔮
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.